BAYAN AN ƊAUKE RUWAN ƊUFANA.
Bayan an ɗauke ruwan Ɗufana sai Annabi Nuhu (AS) ya ga wani mutum a cikin jirgin ruwansa, alhali bai san shi ba.
Sai Annabi Nuhu (AS) ya ce ma sa "Me ya shigo da kai?".
Sai mutumin nan ya ce "Na shigo ne don na saka masifa a cikin mutanenka, ya zamanto zuciyarsu tana tare da ni gangar jikinsu kuma tana tare da kai".
Da jin haka sai Annabi Nuhu (AS) ya gane cewa lallai wannan Shaiɗan ne ba mutum bane, sai ya ce ma sa "Fita ya maqiyin Allah".
Sai Shaiɗanin nan yace ma sa "Ina da abubuwa biyar da nake halakar da mutane da su, zan gaya ma ka uku amma ba zan gaya ma ka guda biyu ba".
Nan take sai Allah Maɗaukakin Sarki Yay wa Annabi Nuhu (AS) wahayi cewa " Ba ka da bukatar ukun da zai gaya ma ka, ka umarce shi ya gaya maka biyun da ya ce ba zai fada ba"
Sai Iblis ya ce "To guda biyun su ne waɗanda na fi halakar da mutane da su. Na ɗaya Hassada, na biyu kuma kwaɗayi"
Ya ce "Saboda hassada aka tsine min kuma aka maida ni Shaiɗani abin jefewa kuma da kwadayi ne na ruɗi Annabi Adam (AS) har buƙatata ta biya aka fitar da shi daga Aljannah".
Ya Allah Ka raba mu da hassada da kwaɗayi.
(Littafin Talbiysu Iblis تلبيس إبليس).
Daga shafin Bashir Halilu.
Comments
Post a Comment