AMFANIN SHAJARATU MARYAM. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN SHAJARATU MARYAM ﺷﺠﺮﺓ ﻣﺮﻳﻢ
Ana kuma kiranta da suna KAFFU MARYAM ko
SHAJARATUL IFFAH ko SHAJARATUR RAHIB ko kuma a ce
SHAJARATU IBRAHIM
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Wannan bishiya shahararriya ce wajen
magungunan cututtuka dababan-daban. Ana iya
shan ta ko ay hayaki wato sirace da ita ko ay
wanka da ruwanta.
1- Ga mai son ya samu karfin ga6o6in jiki,sai ya
dinga shan wannan bishiya musamman tare da 'ya'yan tsidau. Zai sa ka karfin jiki da kwanji. Za
kuma a iya shanta ita kadai.
2- Mai fama da ciwon sanyi kamar rikewar ga6o6i ko sanyin qashi Sai ya dinga tafasa ta yana wanka da ruwan yana kuma sha.
3- Mata masu Sanyin mara ko Toilet infection, sai ki tafasa shajaratu Maryam tare da ganyen Sarqaqiya
ki dinga sha kullum da safe, Sai kuma ki tafasa
wata tare da Bagaruwa ki dinga tsugunawa bayan
kwana uku-uku.
4- Masu dattin ciki sai a tafasa ko a jika Shajaratu
Maryam tare da 'Dinya a sha, ko a sha ta ita kadai.
5- Shajaratu Maryam tana fito da fitsari cikin sauki ga
masu lalurar rashin iya yin fitsari. Sai a jika a sha.
6- Karfin jima'i ga 'yan uwa maza. Sai a dinga Shan
Shajaratu Maryam. Musamman a hada da Murucin
kan dutse da kayan yaji a daka a dinga cin nama
da yajin.
7- Wanda yake fama da rashin iya cin abinci sosai sai
ya jika ta ya din ga sha. Insha Allahu ciki zai bude.
8- Shajaratu Maryam tana da fa'ida sosai wajen
abinda ya shafi lalurorin mata kamar ciwon
ciki,nakuda,ciwon mara, rikicin jini da dai
sauransu.
9- Shajaratu Maryam tana bin ALJANI duk inda ya
la6e a jikin mutum ta karya shi ta fitar da shi
komai taurin kan sa insha Allahu.
10- Tana da karfi wajen karya Sihirin da mutum ya sha
ko ya ci a abinci ko aka binne masa a jikin sa.
Mun godewa Allah da ya fito mana da Shajaratu
Maryam kuma ya sanar da mu amfaninta.
★Sama da mutum dubu dari da talatin da takwas ne a cikin wannan group din na mu, na facebook suke amfana da ADDU'O'I DA MAGUNGUNA NA MUSULUNCI BISA KOWACE IRIN CUTA.
Bayani dalla-dalla, cikin harshe Hausa. Shiga cikin wannan shudin rubutun, za ka ga group din, sai ka danna join.
http://m.facebook.com/groups/842715785785303?ref=m_notif¬if_t=group
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.
Comments
Post a Comment