RAYUWAR JINNUL ƘARIN Nau'in Aljanin da kowane mutum yana da shi a jikinsa, har Annabawa.
RAYUWAR JINNUL ƘARIN Nau'in Aljanin da kowane mutum yana da shi a jikinsa, har Annabawa. Daga shafin Bashir Halilu. Alƙur’ani da Hadisai sun yi magana akan jinnul ƙarīn, wato Aljani mai rakiyar mutum, wanda ke tare da shi tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Wannan Aljani mugun Aljani ne asali, kuma yana da halaye da ayyuka da suka shafi saka mutum ya aikata sharri da ruɗar mutane. Asalin Jinnul Ƙariyn dukkansu kafurai, maƙiya Allah da Manzonsa kuma aikinsu a koda yaushe shi ne su sa mutum ya aikata saɓo. Ga hujjoji daga Alƙur'ani mai girma da Hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kuma magangun Malaman sunnah akan samuwar jinnul Ƙariyn, kasantuwarsa tare da kowane mutum da kuma yadda suke cutar da mutane ta hanyar saka su saɓon Allah. BAYANI AKAN JINNUL ƘARIN DAGA ALƘUR'ANI 1) Suratu Ƙaf, ayah ta 27. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: قَالَ قَرِينُهُ رَبَّنَا مَا أَطْغَيْتُهُ وَلَكِن كَانَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ • قَالَ لَا تَخ...