YADDA AKE KWANCE ALJANIN DA YA MAƘALE A JIKIN MUTUM Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Akan samu matsala wani sa'in sai Aljani ya kasa fita daga jikin mara lafiya, alhali shi kan sa Aljanin yana so ya fita. Wani sa'in ma ya kan yi bayani cewa shi fa ba zai iya fita ba, wani ma ya kan ce shi saidai kawai a kashe shi amma ya rasa yadda zai yi ya bar jikin mara lafiya. Ga wasu abubuwa da kan sa Aljani ya kasa fita daga jikin mara lafiya, alhali shi kan sa yana son fita. 1- An ɗaure Aljani da sihiri. Musamman idan an tura Aljani jikin mutum ne ta ƙarfin tsiya, ta yin amfani da sihiri ko tsafi, ana saka Aljanin a jikin mutum sannan a ɗaure shi, ta yadda komai wahalar da za a ba shi ba zai iya guduwa ya bar jikin mutumin ba. Shi kan sa Aljanin zamansa a jikin mutumin cutuwa ne a gare shi amma ya rasa yadda zai yi ya ceci rayuwarsa kuma yana fatan samun mafita. A irin wannan yanayin, shi kansa Aljanin za ka ji yana baiwa mara lafiyar addu'o'i da kuma gaya masa yadda zai warware sihirin ko kuma tura shi wa...