AMFANINI NAMIJIN GORO. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN NAMIJIN GORO
Kamar yadda masana suka bayyana, namijin goro na da matukar amfani ta fuskoki da dama, musamman a bangaren da ya shafi magunguna, karin kuzari da sauran makamantansu.
Ga wasu daga amfanin da Namijin Goro.
1– Namijin goro na maganin tari.
Idan aka hada shi da alawar tomtom aka ci a tare.
2– Namijin goro na maganin matsalar ciwon sanyi. Idan aka hada shi da kanumfari a tafasa a ruwa aka rika sha.
3– Namijin goro yana maganin matsalar tsutsar ciki; idan aka jajjaga shi aka matse ruwan, sai a zuba zuma a rika sha.
4– Haka nan, namijin goro na maganin olsa, idan aka hada shi da dabino aka daka, sai a zuba zuma cokali biyu a sha.
5– Namijin goro na maganin kara kuzari da nisan tafiya ga masu iyali, idan aka hada shi da dabino sai a rika tauna su tare.
6– Namijin goro na gyara maniyyi, idan aka jajjaga shi aka samu garin hulba aka tafasa, sai a samu madarar ruwa a zuba a shanye baki-daya.
7– Namijin goro na kawar da majinar kirji, idan ana cin sa lokaci zuwa lokaci.
8– Namijin goro na hana shan taba, idan aka hada shi da furen tumfafiya, aka dake aka samu karan sigari da madarar shanu mai kyau, a hada guri guda a bar su su kwana da safe kafin a ci komai, sai mai shan tabar ya shanye duka. Bayan wasu mintuna ko awanni zai yi aman dattin tabar baki-daya, sannan ba zai kara sha’awar sake ba da yardar Allah.
9– Namijin goro na maganin ciwon kai, idan aka dake shi ya zama gari, sai a rika yin hayaki (turare) da shi, musamman ma mata masu yawan ciwon kai.
10– Namijin goro yana gyara murya, idan aka hada shi da danyar citta da zuma, ana dafawa da lifpton a sha kafin a ci komai da safe.
11– Namijin goro na maganin kuraje, idan aka samu garin namijin goron; aka kwaba da man zaitun. Idan kuma karzuwa ce ko bakon dauro, sai a kwaba da manja a rika shafawa.
12– Namijin goro na maganin sanyin mara, idan aka hada da kanunfari da lemon tsami da Citta da garin albabunaj, sai a tafasa a rika sha da zuma.
13– Namijin goro na maganin kuna, idan aka hada da sassaken itacen kirya aka daka, sai a rika barbadawa a kan kunar.
14– Namijin goro na tsayar da jini, idan aka hada da tsamiya aka tafasa, sai a sha nan take jinin zai tsaya da izinin Allah.
15– Bugu da kari, namijin goro yana kawar da wasu cututtuka da suke a cikin mutum iri daba-daban.
★ Illolin Namijin Goro.
Cin Namijin goro ba bisa ƙa'ida ba ko cinsa yai yawa kan iya haifarwa mutum da faduwar gaba, jiri, ciwon kai, rashin bacci ko rawar jiki.
Mata masu ƙaramin ciki da ƙanan yara su guji cin Namijin goro.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment