Posts

Showing posts with the label labaran shaiɗan kissoshin iblis

HAƊUWAR SHAIƊAN DA ANNABI YAHYA (AS) HAR KARO BIYU.

Image
Daga Shafin Bashir Halilu      A cikin littafin Maka'idish Shaiɗan, Ibni Abid dunya ya ruwaito cewa:    Abdullahi ɗan Muhammad ɗan Ubayd ya ce: Ahmad ɗan Ibrahim al-Abdiyyu ya ba mu labari, ya ce: Muhammad ɗan Yazid ɗan Khunays ya ba mu labari, daga Wuhaib ɗan -Ward ya ce:      "An ruwaito mana cewa: Iblis, mugu kuma makiri, ya bayyana ga Annabi Yahya ɗan Annabi Zakariyya (AS),  sai ya ce masa:        'Ina so in ma ka nasiha.' Sai Annabi Yahya (AS) ya ce:          'Ƙarya kake! Kai ba za ka yi min nasiha ba. Amma ka ba ni labarin mutane.' Sai Iblis ya ce: 'Ɗan Adam ya kasu gida uku a wurinmu: 1. Na farkon su ne mafi wahala a gare mu. Muna zuwa wajensu, mu sa su aikata saɓo, amma su kan tuba da neman gafara, har su lalata duk wani makirci da muka yi musu. Muna komawa kansu, su kuma su dawo su tuba. Ba ma samun abin da muke so daga gare su, kuma ba ma daina ƙoƙarin fitinarsu. Wannan ya jef...