AMFANIN ROGO WAJEN ƘARA LAFIYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

AMFANIN ROGO WAJEN ƘARA LAFIYA.

   Rogo wata saiwa ce wadda kusan duk duniya ake amfani da shi, wanda ya ke da matuƙar amfani wajen kyautata lafiyar al'uma. A fannin da rogo ya ke aiki waje kyautata lafiya kusan babu kamarsa acikin saiwoyi, saboda

    1. Rogo cike ya ke da 'nutrients'. Domin giram 100 kawai na garin dafaffen Rogo yana dauke da
    - Calories 191. 

   - Carbohydrates kashi 84 bisa ɗari. 
    - Protein giram 1.5. 
     - Fat giram 3. 
     - Fiber giram 2. 
     - Vitamin C kashi 20 bisa ɗari na adadin abinda jikin mutum ke bukata a kullum. 
     - Copper kashi 12 bisa ɗari na bukatar jikin mutum a kullum. 
     - Thiamine kashi 7 bisa ɗari na bukatar jikin mutum a kullum. 
     - Folate kashi 6 bisa ɗari na bukatar mutum a kullum. 
     - Vitamin B6 kashi 6 bisa ɗari  na bukatar kullum. 
     - Potassium kashi 6 bisa ɗari. 
     - Magnesium kashi 5 bisa ɗari. 
     - Niacin kashi 5 bisa ɗari. 
   
  Wanda hakan ke nuna cewa Rogo shi kaɗai ya kusan kaiwa abinda zai iya riƙe mutum a rayuwarsa wajen bayar da kuzari da gudunmawa mai yawa wajen kyautata lafiya. 

    2. Gyara jini da kuma kyautata lafiyar jiki. 
 Rogo tushe ne mai kyau wajen samar da 'resistant starch' wanda ke taimakawa wajen gyara lafiya da kuma samar da kyakykyawan sinadarin 'sugar' wanda jini ke amfani da shi. 
   
3. Ƙara ƙarfin garkuwar jiki. 
   Rogo na samar da sinadairin 'vitamin c' wanda ke ƙara ƙarfin garkuwar jiki da yaƙi da cututtuka bayan ga samar da jini da kuma haɓaka jikin mutum. 

4. Taimakawa masu fama da 'food allergy'. 
 Waɗanda jikinsu ke da matsalar iya narka da abinci yadda ya kamata za su amfana da Rogo sosai idan su ka ci dafaffe ko gasasshensa. 

5.Bayar da kuzari ga mazaje. 
    Cin Rogo yadda ya kamata na baiwa namiji kuzari na gaske wajen iya kula da iyali. 

   Daga cikin sharaɗin cin Rogo shi ne ya kamata a dafa shi kafin a ci saboda yawan sinadaran da ke cikinsa ba kowanne mutum ne zai ci ɗanyensa ya zauna lafiya ba. Ɗanyen Rogo kan iya zama guba ga waɗansu. 

  Rogo dai tabbas abinci ne mai daraja da amfani da kyautata lafiyar bil'Adama, don haka ya kamata Rogo ya zama cikin kayan da kake haɗa abinci da shi ko da lokaci zuwa lonaci ne.
 
    Ana iya sarrafa Rogo ta hanyar dafawa, gasawa, wainar Rogo, Jiƙaƙƙen kwaki, teba, mandaƙo, ɗan wake, tubani da dai sauransu.

  Idan kuna bukatar sanin amfanin wani magani ko wani abinci sai ku rubuta a wajen comment, za mu kawo muku insha Allahu.

 Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts