WAFATIN ANNABI ADAMU (A.S) DA WASIYYARSA GA ƊAN SA SHIYSU (AS).
Daga shafin Bashir Halilu Ya zo acikin littafin 'Albidayah Wan Nihayah' na Ibnu Kasir cewa: an ruwaito cewa Annabi Ādam عليه السلام ya rayu har tsawon shekara dubu (1000). Lokacin da ajalinsa ya kusa, sai Mala’ikan Mutuwa ya zo wurinsa. Sai Annabi Adam (AS) ya ce da shi: “Ba sauran shekara arba’in a cikin rayuwata ba?” Wannan kuwa saboda wata rana Allah Maɗaukakin Sarki Ya nunawa Annabi Adam (A.S.) tsawon rayuwar zuriyarsa, sai ya ga Annabi Dāwuda عليه السلام yana da gajeriyar rayuwa, shekara 40, sai Annabi Ādam (A.S) ya ce ya ba shi kyautar shekara arba'in daga rayuwarsa. Amma lokacin da Mala’ikan mutuwa ya dawo domin karɓar ransa, sai Annabi Ādam (AS) ya manta ya ce: “Ai ni ban ba shi wani abu daga rayuwata ba!” Sai Ibn Kathīr ya ce: "Annabi Ādam ya manta, zuriyarsa ma sai suke mantuwaa. Ādam ya musanta, zuriyarsa ma sai suke musu. Ya yi kuskure, zuriyarsa suke yin kuskure". Lokacin da Annabi Ādam (A.S) ya rasu — kuma hak...