MAGAGIN BACCI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

MAGAGIN BACCI

Da abubuwan da suke kawoshi da kuma yadda ake maganinsa.
Ma'anar Bacci a Musulunci. 
Bacci wani yanayi ne da Allah Maudakin Sarki yake daukar ran halitta, saidai kuma ba daukewa ce gaba daya ba, Yana dawo da ran bayan wani lokaci, sai mutum ya farka. In Allah Ya so kuma sai Ya rike ran, shikenan sai a zarce da mutuwa. Bacci hutu ne ga Dan'Adam, kamar yadda Allah Ya fada. 

A al'adance da likitance kuma bacci hutu ne ga gangar jiki da kuma kwakwalwa. Su kan yi bacci,  wato su tsayar da ayyukansu,  su dan huta zuwa wani lokaci sannan su farka,  su cigaba.

Ma'anar Magagin Bacci. 
 Ita ce Mutum ya dinga magana ko tafiya ko yin wani aiki da jikinsa, alokacin da yake cikin bacci, ba tare da ya farka ba.

Yawanci dai Magagi ba ya wuce mintuna biyar zuwa sha biyar yake sakin mutane.

Magagin bacci, kamar yadda binciken zamani ya nuna, yana da alaqa da matsalar Dannau. 

Inda binciken ya nuna cewa, a yayinda mutum yake bacci, to kwakwalwarsa da gangar jikinsa dukkansu suna hutawa ne, idan ya tashi farkawa kuma sai su farka gaba daya.

     To idan aka samu matsala, kwakwalwar mutum ta farka, gangar jikinsa kuma bata farka ba, sai mutum ya ji ya dawo cikin hankalinsa amma ya kasa tashi kuma ya ji kamar an daddaure shi. Wannan shi ake cewa Dannau a bincikensu amma dai cikakkan bayani yana cikin wannan shudin rubutun

http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html .

To idan kuma ya kasance gangar jikince ta farka, kwakwalwar kuma bata farka ba, sai gangar jikin mutum ta tashi, ta dinga yawo ko ta dinga magana ko wani  aiki, ba tare da kwakwalwa ta san abinda ake yi ba. Wannan kuma shi ake kira Magagin Bacci.

ALAMOMIN MAGAGIN BACCI SUN HADA DA

1-  Tashi ayi tafiya. Wato mutum ya tashi, ya kama hanya, yana tafiya, ba tare da ya sani ba.

2- Mutum ya tashi, ya zauna, yana mummurza idanu, yana muzurai.

3. Za ka ga mutum ya bude idonsa amma kuma ba ya gane abinda yake gani.

4- Idan mutum yana Magagi, za ka ga idan ka nay masa magana ba ya gane abinda kake cewa ko kuma ba ya ba da amsa daidai.

5- Mai Magagin Bacci yana wahalar wattsakewa, ba kamar mai bacci ba.

6- Yin magana, lokacin da mutum yake bacci. Manya ma suna yi amma ya fi faruwa ga yara. Za ka ji suna ta hirar wasanni da kuma abubuwan da suke yi a makaranta.

7- Mai Magagin bacci ya kan ta shi, ya je yay fitsari, a wajen da ba a nan ake yi ba.

8- Wani kuma Magagin Baccinsa ya kan sanya shi buge-buge ne da jibgawa abokin kwanciyarsa kafa.

ABUBUWAN DA SUKE KAWO MAGAGIN BACCI.

1- Na farko akwai gado. Wato idan an samu acikin iyaye wani yana da shi, to zai iya yiwuwa acikin `ya`yansu wani ya gada.

2- Rashin Bacci. Idan ya kasance mutum ya dade sosai ba ya samun  bacci to in ya samu baccin kuma zai iya tashi da Magagi.

3- Tashin mutum lokacin da bacci bai ishe shi ba. Idan ka tashi mai bacci kafin lokacin da ya saba tashi, to zai iya tashi da Magagi.

4-  Rashin lafiya ko Zazza6i. Idan mutum ba shi da lafiya, to in ya samu bacci zai iya tashi da Magagi, musamman idan tashinsa aka yi.

5- Shan Magani. Idan mutum ya sha magani lokacin da zai kwanta bacci, musamman maganin asibiti, to zai iya tashi da Magagi. 

6- Gajiya. Wanda yay Bacci bayan ya yi aikin gajiya sosai, shi ma zai iya tashi da magagi.

7- Idan mutum ya kwanta bacci, yana jin fitsari, to zai iya tashi da magagi kuma zai iya yin fitsarin a ko ina ne.

8-  Yin bacci a waje mai hayaniya.

9- Canjin wajen kwanciya. Idan mutum ya kwanta a wajen da ba anan ya saba kwanciya bacci ba, to shi ma zai iya yin Magagi.

       Saidai binciken Malamai ya tabbatar da cewa:-

 KASHI CASA'IN DA BIYAR BISA DARI (95%) NA MAGAGIN BACCI YANA DA ALAKA NE DA SHAFAR AL-JANU KO SIHIRI

 Kashi biyar bisa dari (5%) ne kawai wadancan abubuwan da aka lissafa suke sabbabawa.

MA'ANAR MAGAGIN BACCI A WAJEN MALAMAN RUKIYYAH

     Magagin bacci wani abu ne da yake faruwa, a lokacinda Aljani ya shiga jikin mutum, lokacin da yake bacci. Wani lokacin kuma Aljanu sukan zo suyi wasa da `ya`yan mutane, shi yasa yara suke magana, in suna bacci.

 Wani lokacin, Aljanin ne da kansa ajikin mutum, yake magana. Wani lokacin kuma ya kan zowa mutum a mafarki ne, sai ka ji mutum yana magana, ko ihu ko wani aiki, a lokacin da yake bacci, amma in ka tambaye shi bayan ya farka, zai gaya maka cewa ya ga wani abu ne a mafarki. (Za mu kawo cikakken bayani akan mafarki, nan gaba kadan, insha Allahu).

ABUBUWAN DA SUKE KAWO MAGAGIN BACCI.

     1- Rashin yin addu'a, yayin kwanciya bacci.
     2- Kwanciya da janaba.
    3-Fara kwanciya a 6arin hagu.
      4- Kwanciya rigingine ko rub da ciki.
        5- Matsalar Aljanu, indai mutum yana fama da matsalar Aljanu, zai iya dinga fama da magagi amma ba kowane Aljani ne ya ke sa magagi ba.
       6- Matsalar Sihiri. Idan aka yi wa mutum asiri mai alaqa da kwakwalwa, kamar Asirin Mallaka ko asirin Haukatarwa ko asirin raba kauna da dai sauransu, to zai iya dinga fama da magagi.

ME YASA AL-JANU SUKE SA MUTANE MAGAGI?

Mun yi bayani cewa ba kowane nau'in Aljani ko sihiri ne yake sa magagi ba amma ga abubuwan da suke sawa Aljanu suke sa mutane magagi:-

            1- Aljani ya kan sa mutum magagi ne idan ya kasance ba ya iya shiga jikinsa sai lokacinda yake bacci.

       2- Idan aka yi wa mutum asiri don ya so wa ni ko kuma don ya kyamaci wani, to Aljanin zai iya zuwa jikinsa, sai ya dinga kiran sunan wancan din.

3- Idan aka yiwa mace asiri don a koreta daga gidan mijinta, za ta iya tashi acikin magagi, ta bude kofa, ta fita waje, komai tsakar dare, saidai idan an lura a bi ta, a kamo ta. In gari ya waye kuma za ta ce ba ta san ta yi ba, saboda Aljnin ne ajikinta yake yi.

4- Musamman wanda aka yi wa asiri don a haukata shi, ko a kore shi daga garinsu, zai dinga tashi a firgice, yana zurawa da gudu, ko ya dinga dukan mutane amma daga baya zai ce bai san ya yi ba.

5- Wani Aljanin idan yunwa ta ishe shi, sai ya shiga jikin mutum lokacin da yake bacci, ya zuba abinci, ya ci, amma in ka lura da mutum za ka ga yana cin abincin yana gyangyadi, kuma daga baya zai ce bai san ya ci ba.

6- Wani idan yay magagin bacci, to daga baya yana iya gane cewa ya aikata kaza amma kuma lokacin da ya aikata ba ya iya sarrafa kansa. To wannan da alamun Aljanu na so su shiga jikinsa kenan, ko kuma an yi masa sihiri.

7- Kamar dai yadda yake a matsalar Dannau, wani lokacin Aljani ya kan sadu da mace, ta yadda zata dinga yin wasu abubuwa, kamar magagi, alhali Aljani ne yake saduwa da ita ( karanta cikakken bayani akan Aljani mai saduwa da matan mutane acikin wannan shudin rubutun 
  https://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/jinnul-ashiq-aljani-mai-saduwa-da-matan.html )

ABUBUWAN DA MAI MAGAGIN BACCI YA KAMATA YA DINGA KIYAYEWA

Likitocin zamani da sukai bincike akan magagin bacci, sun bada shawarwari kamar haka:-

 
1- Yana da kyau kada ka dinga kwanciya a dakin da yake akwai abuwawa masu hatsari, kamar wuta ko abubuwa masu kaifi.

2- In zai yiwu, kamata yay ka dinga kwanciya a kasa, ba a kan gado ba.

3- Ka tabbatar ka kulle kofofi da makulli.

4- Yana da kyau ka saka kararrawa ajikin kofar dakin da kake kwanciya, yadda idan an ta6a ta za ta yi kara.

A ADDINANCE KUWA, YA KAMATA KA KIYAYE

1 - Kwanciya da Alwala.

2 - Yana da kyau mutum ya karkade shinfida kafin ya kwanta. Domin Aljanu su kan zo, su kwantar da yaransu ko su baza kayansu akan shinfidar mutane. In ka kwanta a kansu sai su shiga jikinka, kamar dai yadda mu ka kawo bayani acikin wannan shudin rubutun
http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/10/aljanar-jarirai-ummul-atfal-aljana-mai.html 

cikin bayanin mu mai taken AL-JANAR JARIRAI.

3 - Karanta Ayatal Kursiyyu kafin kwanciya bacci.

4 - Karanta Addu'ar Kwanciya Bacci.

5- An fi so mutum ya fara  kwanciya a 6angaren dama, in ya gaji sai ya koma hagun.

ILLOLIN MAGAGIN BACCI

                     1- Yana iya sa wa mutum ya raunata kansa, kamar faduwa ko bugewa.

              2- Yana sawa mutum ya fita cikin tsakar dare ya kama hanya yana tafiya, wanda har matan aure ana samun masu yin haka.

               3- Idan magagin baccin mutum yana da alaqa da Aljanu, to suna iya shafar kwakwalwarsa.

                  4- In Magagin mutum yana da alaqa da sihiri, to wani yana iya yin kwana goma zuwa sati biyu, ko sama da haka, yana cikin magagin bacci.

             5- Magagin bacci yana da alaqa da matsalar kwakwalwa ko kuma zai iya haddasa ta.

6- Mai yin dariya acikin magagi ya fi mai yin kuka matsala kuma ya fi wahalar dainawa ko magani.

7- Mai magagin bacci yana razanar da abokan kwanciyarsa, domin zai iya dinga zaginsu ko ya sa musu duka. 

8- Magagin bacci ya kan mayar da mutum dolo ko soko ko kuma shawaraki a Sakwkwatance. 

               In kana Magagin Bacci ko kana da mai yi,  to ka hanzarta zuwa Asibiti ko wajen Malaman Ruq'yah don samun shawarwari da magunguna. 

Daga Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.

Lambar waya 08162600700.

Comments

Popular Posts