AMFANI JIRJIR WAJEN ƘARA LAFIYA Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

AMFANIN  JIRJIR WAJEN KARA LAFIYA. 

Ciyawar Jirjir da ƙwayoyin 'ya'yansa suna da amfani sosai a jikin dan'Adam.

Ga kadan daga cikin fa'idodinsa:

   :{1}: Man Jirjir yana ƙara ƙarfin Jima'i ga Maza.
     Kamar mutumin da yake da Qarancin sha'awa, ko kuma rashin Qarfi, idan yana Shan Man Jirjir acikin ruwan dumi ko kuma  shayi  ba madara, insha Allahu za'a dace.

:{2}:Yana sa ƙarfin gashi ga mata. 
   Duk matar da take fama da karyewar gashi sai ta dinga Shafa Man jirjir, gashinta ba zai rika karkaryewa ba. Haka za ki iya amfani da shi don rigakafin karyewar gashi.

:{3}: Wanda yake fama da matsalar As'ma ko tari, idan yana shan jirjir   a cikin zuma tare da kanumfari insha Allah zai samu waraka.

: {4}: Wanda yake da Qarancin Jini ajikinsa, idan yana shan Man jirjir ko kuma Garinsa, zai samu Qaruwar jinin jikinsa.

:{5}:Ciwon daji   Bincike ya nuna cewar Jirjir yana kashe 97% na Kwayoyin chutar Daji. Musamman ma Sankaran Mama wato ciwon nono.

:{6}:. Matar da Jinin al'adarta ya rikice, sai ta samu  Man Jirjir ta dinga zuba cokali daya a ruwan dumi tana sha, zata samu waraka insha Allahu.

:{7}: Mutumin da yake fama da Sikila idan yana sha kuma yana shafa man Jirjir za'a dace da yaddar Allah.

:{8}: Matar da take shayarwa idan tana shan Man Jirjir zata samu Qaruwar ruwan nononta. Shi yasa ma akasashen da suke nomanta, da zarar mace ta haihu suke bata yawancin abincin da yake dauke da Ganyen Jirjir acikinsa.

:{9}: Mutumin da Cinnaka ko rina ko zuma ta harbeshi, idan ya shafa Man jirjr nan take zai samu waraka. Insha Allah.

Amma a kula. 
           
     Matar da take dauke da Juna biyu kada ta sha Man Jirjir domin kuwa yana matso Wuyan mahaifarta kuma zai iya haddasa mata ɓari ko nakuda cikin gaggawa, don haka a kiyaye.

Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts