AMFANI ZA'AFARAN DA AMBAR DA KUMA ALMISKI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

AMFANIN ZA'AFARAN DA AMBAR DA KUMA ALMISKI WAJEN KYAUTATA LAFIYA.

Daga Shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.
1) ZA'AFRAN.
Shi Za'afaran wata ciyawa ce ko kuma tsiro mai dauke da launi mai abin sha'awa, galibi jar ciyawa ce ko yaluwa. Da akwai man Za'afran, da akwai turarensa kuma ana samun ciyawar tasa ma.
Ana amfani da shi wajen sinadarin girki kuma yana maganin cututtuka da dama yana kuma kyautata lafiya.

An fara noman Za'afaran ne a wajejen Greece. Sannan akay Safararsa zuwa Yammacin Amurka da kuma kasashenmu na Afrika.

Za'afaran yana maganin cututtuka kamar:

★Zubewar Gashi.
Shafa Man Za'afaran a fatar kai yana maganin sanqo. Hada Za'afaran da madara a shafa a kai yana maganin zubewar gashi kuma yana kara yawan gashi.

★Gyaran Fuska
Hada Za'afaran da madara a shafa a fuska a hankali amma a kaucewa ido. A bar shi tsawon minti goma sha biyar sannan a wanke da ruwa yana sa fuska tay kyau da sheqi. Ana yin wannan hadin sau daya a sati.

★Matsalolin fata.
A jika ciyawar Za'afaran a ruwa tsawon awa biyu zuwa uku. Sai a shafe fatar jiki da shi. Yana bada fata mai laushi da taushi. Ana yin haka sau biyu zuwa uku a sati.

★Maganin kuraje.
A hada Za'afaran da Ray'han a kir6a a shafa akan fata sai a wanke bayan minti goma. Wannan hadin yana maganin kuraje, kyasbi, makero da tabo da kuma sauran cututtukan fata.

★Kwayoyin Cuta.
Zuba ko fesa Za'afaran a waje yana maganin kwayoyin cututtuka da ba'a iya ganinsu kuma yana kyautata lafiya.

★Kyautata Bugun Zuciya.
Za'afaran yana da sinadarin potassium wanda ke kyautata bugawar zuciya da kuma bata damar yin aikinta yadda ya kamata.

★Zagayawar jini.
Za'afaran yana da sinadarai irinsu coper, potassaium, calcium, manganese, iron, magnesium, da zinc da kuma selenium. Wasu daga cikin wadannan sinadarai suna taimakawa wajen daidaita yanayin jini a jikin mutum.

★Rigakafin Cutar Kansa (cancer).
Za'afaran yana dauke da wasu kananan sinadarai kamar zea-xanthin da lycopene wadanda ke kare jikin mutum daga kamuwa da cutar Kansa wato Daji.

★Saukaka Narkewar Abinci.
Za'afaran yana da muhimmanci wajen saukake narkewar abinci a jikin mutum saboda sinadarin anti-cinvulsant da sauran sinadarai dake cikinsa.

★Ciwon Hakori.
Shafa Za'afaran hade da Zuma yana taimakawa wajen maganin cututtukan dasashi da hakori.

★Cututtukan Cikin Baki.
Idan aka hada Za'afaran da Zuma da Graceline ana shafawa a cikin baki yana maganin kuraje da sauran cututtukan da kan iya samuwa a cikin baki.

★Gyaran le6e.
Za'afaran yana cikin tsirrai kadan wadanda ke samar da sinadarin vitamin B2 mai yawa. Amfani da shi yana gyara la66a da kuma kyautata hadiyar abinci daga baki zuwa makogwaro.

★Maganin Sanyi da Tari.
Idan aka hada Za'afaran 1grm da ruwa 1ltr aka sha yana maganin Sanyi da kuma Tari.

★Jini lokacin Al'ada.
Za'afaran yana da kyau wajen daidaita zuwan jini yayin al'ada.

★Maganin Maza.
Amfani da Za'afaran yana taimakawa mazaje su dawo da karfinsu. Hatta tsofaffi yana ba su kuzari sosai.

★Maganin Aljanu da Sihiri.
Hada Za'afran da Jan Almiski da Ambar, a dinga shafawa a fata, yana maganin cututtukan Aljanu kuma yana taimaka wajen 6ata sihiri da ke jikin mutum.

★ Amma a kula ★

☆Yin amfani da Za'afaran ba bisa ka'ida ba zai iya sawa mutum:-

* Mura
*Ciwon Kai
da kuma
*Daukewar Miyau a baki.

★ Masana harkar lafiya ba suy bayanin illar Za'afaran ga mace mai ciki ba, sun ma dai ce yana taimaka mata.

Daga shafin Sunnah Medicine, Masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.

2)AMFANIN AMBAR GA LAFIYAR AL'UMA.

Ambar wani magani ne da ake samun sa daga jikin wata bishiya. Wato kamar irin farin ruwan nan dake fita daga jikin bishiya. Shi ne ake hada
shi da wasu sinadarai a samar da Ambar. Kuma ana samunsa a jikin bishiyoyi da dama. Idan ku ka duba wannan hoton za ku ga hoton Ambar kamar Qaro.

Bayan amfanin da Ambar yake da shi wajen kiwon lafiya, haka ma yana taimakawa wajen magance cututtukan jiki da na jinnu ko sihiri.

Ana iya hada Ambar da wasu magunguna kamar zuma, miski, habba, zaitun, da dai sauransu, ayi amfani da shi don samun ingantacciyar lafiya

Yi amfani da Ambar kadan ka samu lafiya mai yawa da yaddar Allah.

Ana samun Anbar na gari, ana samun na ruwa, ana samun na turare, ana
samun kwa6a66e na shafawa .

★ Sanya nishadi.
Ambar yana sanya nishadi idan aka sha kilogram daya tare da zuma cokali daya.

★Kara karfin hakora.
Ambar yana kara karfin hakori idan ana goge hakora da man sa, wato Amber oil.

★Gyara kwakwalwa.
Man Ambar yana maganin cututtukan kwakwalwa idan ana shan sa tare da Man zaitun
da Habbatussaudaa.

★Maganin ciwon Hauka.
Ga mai lalurar hauka sai adinga tofa ayoyin Ruq'yah a cikin Ambar, a zuba a ruwa, a ba shi, ya sha kuma a dinga yi masa hayaki da shi musamman a
hada da miski wajen hayakin.

★Ciwon kai.
Ciwon kai bari guda sai a hada Ambar da jan miski da Man juda a kwa6a, a dinga shafawa a kan kuma ana yin hayakin sa.

★Lalata sihiri.
Ana amfani da Ambar ta hanyoyi da dama wajen 6ata sihiri wanda mutum ya ci ko ya sha.

★Hawan jini.
Masu hawan jini su sha Ambar kadan a cikin ruwa.

★Gyaran fata.
Don gyaran fata da jin dadin jiki, sai a diga Ambar kadan a cikin ruwan wanka ay wanka da shi.

★Dadin bacci.
Mai son yin bacci mai dadi shi ma sai ya zuba Ambar kadan a ruwan wankansa.

★Hutawar kwakwalwa.
Ambar yana taimakawa kwakwalwa wajen samun hutu mai dadi.

★Lafiyar zuciya.
Amfani da Ambar yana kara kyautata karfin zuciya.

★Asthma.
Masu cutar Asthma su ma Ambar yana taimaka musu idan suna amfani da shi.

★Gudanawar jini.
Amfani da Ambar yana kara kyautata gudanawar jini a jikin mutum.

★Karfin jima'i.
Yin amfani da Ambar yana kuma kara karfin jima'i ga maza da mata.

★Narkewar abinci.
Amfani da Ambar na saukaka narkewar abinci a cikin ciki, yana hana kumburin ciki, tusa da sauran matsalolin ciki.

★Dadin jiki.
Yana kara soyayya tsakanin miji da mata, idan dayan su yana amfani da
shi.

★ Warkewar ciwo da kashe kwayoyin cuta.
Sai a zuba man Ambar a kan
ciwon bayan an wanke shi. To zai warke cikin sauki insha Allah.

★ Amma a kula ★
.
Duk da amfanin Ambar kuma zai iya cutarwa .

★Mata masu ciki su guji amfani da Ambar, musamman sha a ciki.

★Ambar din da ba a gauraya shi da wani abu ba kamar ruwa da makamantansu, to a guji shan sa kai tsaye.

★Ba'a sa Ambar a cikin ido.

★A guji ajjiye Ambar kusa da yara.

Daga cibiyar sunnah medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.

3) AMFANIN ALMISKI

Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya fade shi a Alqur‘ani.

Amfanin sa.

★ Yana maganin dafi kowane iri.

★ Yana kara karfin jiki.

★ Yana maganin hawan jini idan an sheka.

★Yana maganin Aljanu, ya kan ma iya kashe Aljani idan an hada shi da Za‘afaran ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaki.

★Yana maganin warin gaba idan ana shafawa.

★Yana maganin namijin dare.

★Yana taimakawa masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gma al'ada.
Akwai jan Miski akwai baki kuma akwai farin Almiski akwai kuma miski na ruwa.

Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.

Lambar waya 08162600700, 08134434846. 

Comments

Popular Posts