Posts

Showing posts with the label Addinin musulunci

DUK WANDA YA ƘIRƘIRO SABUWAR IBADA TO BA SHI DA LADA

Image
عَنْ أمِّ المُؤمِنينَ أمِّ عبْدِ اللهِ عائشةَ رَضِي اللهُ عَنْهَا قالَتْ: قالَ رسولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: {مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ مِنْهُ فَهُوَ رَدٌّ} رواه البخاريُّ ومسلمٌ. وفي روايةٍ لمسلمٍ: {مَنْ عَمِلَ عَمَلاً لَيْسَ عَلَيهِ أَمْرُنا فَهُوَ رَدٌّ}. An karɓo daga Ummul-Mu’uminina, Ummu Abdullahi, Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: “Duk wanda ya ƙirƙiri wani abu a cikin wannan al’amari na mu (addininmu), wanda ba daga cikinsa ya ke ba, to abun juyarwa ne.”     ★Wato dukkan wanda ya ƙirƙiro wani aiki na ibada wanda ba musulunci ne ya yi umarni ba to za a mayar masa da aikinsa, Allah ba Zai karɓa ba ballantana Ya ba shi lada. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.) A wata ruwaya daga Muslim kuma: Manzon  Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya aikata wani aiki wanda ba bisa umarninmu ba ne, to ba a karɓa.”      ★Ma'ana aikin ibada wanda Allah da Manzonsa ba su ce...