MATSALOLIN MATA DA MAGUNGUNANSU
★ JININ HAILA DA YADDA AKE BAMBANCE SHI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA. ★CIWON SANYI NA MATA DA MAZA DA YADDA AKE MAGUNGUNANSA. ★MATSALOLIN DA SUKE FARUWA BAYAN ZUBAR DA CIKI KO 6ARIN CIKI. Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. ASALIN JININ HAILA 1- Datti ne da ke cikin mahaifar mace, shi ne a duk wata ake wanko mata shi yana fitowa. . 2- Kwan haihuwa ne na mace yake saukowa, idan bai samu kwan namiji sun samar da abin halitta ba sai ya lalace ya ru6e, daga nan sai a wanko shi ya fito waje. Mace tana fara haila ne lokacinda ta balaga. Mata kan iya fara haila daga shekara tara ko sama ko kasa da haka, ya danganta ne da irin abincin da take ci da kuma yanayin wajen da ta ke rayuwa. Wasu suna daina haila da wuri idan sun fara tsufa, wasu kuma suna dadewa ba su daina ba. Saidai daukewar...