YADDA ALJANU SUKE HAWA SAMA DON SATO MAGANAR MALA'IKU. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

YADDA ALJANU SUKE HAWA SAMA DOMIN SATO MAGANAR MALA'IKU
https://www.youtube.com/@bashirhalilutv

A cikin Alqur'ani mai tsarki, Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi magana akan masu hawa sama ko ƙoƙarin hawa sama, domin su saurari irin maganganu da Mala'iku suke yi, don su dawo ƙasa su dinga sanar da Bokaye da kuma yadda Allah Maɗaukaki Ya tanadi wasu taurari a sama masu jefe irin waɗannan Shaiɗanun masu yiwa Mala'iku laɓe.

Ka duba tafsirin Aya ta 23 cikin Suratu Saba'i da Ayah ta 7 cikin Suratus saffati da Ayah ta 18 cikin Suratul Hijri da dai wasu gurare da dama a Alƙur'ani, domin ganin yadda Allah Mai girma da ɗaukaka Yai bayani akan satar bayani da wasu Shaiɗanu suke yi daga Mala'iku domin su sanar da Bokayae, su kuma Bokaye su dinga taƙamar cewa sun san gaibu.

Yanzu ga wani Hadisi wanda  bayani ya zo daga bakin Manzon Allah (SAW) game da yadda Aljanu suke hawa sama domin satar maganar Mala'iku da kuma abinda ya ke kasancewa.

روى البخاري  عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: 

  إذا قضى الله الأمر في السماء ضربت الملائكة بأجنحتها خضعاناً لقوله، كأنه سلسلة على صفوان ينفذهم ذلك. حتى إذا فُزِّع عن قلوبهم قالوا: ماذا قال ربكم؟ قالوا: الحق وهو العلي الكبير فيسمعها مسترق السمع ـ ومسترق السمع هكذا بعضه فوق بعض ـ وصفه سفيان بكفه فحرفها وبدد بين أصابعه ـ فيسمع الكلمة فيلقيها إلى من تحته، ثم يلقيها الآخر إلى من تحته، حتى يلقيها عن لسان الساحر أو الكاهن فربما أدركه الشهاب قبل أن يلقيها، وربما ألقاها قبل أن يدركه، فيكذب معها مائة كذبة فيقال: أليس قد قال لنا يوم كذا وكذا: كذا وكذا فيصدق بتلك الكلمة التي سمعت من السماء. 
صحيح. 
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruq'yah da bayarda magunguna  na musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Kalli cikakken wannan bayani acikin bidiyo acikin wannan shuɗin rubutun

https://www.youtube.com/@bashirhalilutv.
Wannan hadisi ya zo da ruwayoyi daban-daban amma za mu yi bayanin ma'anarsa tare da shigar da bayanin sauran ruwayoyin acikin fassarar. 

Acikin wannan sahihin Hadisi da Bukhari ya ruwaito, Manzon Allah SallAllahu alaihi wa sallama ya ce

      "Idan Allah Ta'ala Ya yanke wani hukunci a sama, wato acikin fadarsa, sai sama ta kama girgiza mai ƙarfi ko ko kuma tsawa mai ƙarfi, sai kuma Mala'iku su dinga bubbuga fuka-fukansu, don nuna girmamawa ga umarnin Allah Maɗaukakin Sarki, kai ka ce sarƙa ake bugawa akan fan dutse kuma su faɗi suyi sujjada. Har sai sun samu nutsuwa tukuna, sai ya zamanto Mala'ika Jibrilu shi zai fara ɗago kansa, sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanar da shi abinda ya nufa. Daga nan sai sauran Mala'iku su dinga cewa "Me Ubangijinmu ya ce ya Jibrilu?". (Ma'ana wane umarni Allah Ya bayar?). Sai ya  ce "Allah Ya yi umarni na gaskiya ne, kuma shi ne Maɗaukaki mai girma.
Dukkan saman da Mala'ika Jibrilu ya wuce sai Mala'iku su ce masa" "Me Ubangijinmu ya ce Ya Jibrilu? ". Shi kuma sai ya ce gaya musu abinda Allah Ya sanar da shi. 

  Sai Mala'iku su dinga gayawa ƴan uwansu Mala'iku cewa Allah Ya ce za a yi kaza da kaza a duniya. Suna cikin wannan magana ne sai Aljanu masu sauraron maganar Mala'iku su ji wannan zance da Mala'iku suke yi, sai Aljanin da ke can kusa da sama ya gayawa Aljanin da ke ƙasansa abinda ya ji, shi ma ya gayawa na ƙasansa. Kowane in ya tashi sai ya ƙara ƙarya ɗari cikin abinda ya ji, sannan ya gayawa na ƙasa da shi. Sun kasance suna hawa sama ta hanyar wani ya taka kafaɗar wani, shi ma wani ya hau kan kafarsa har izuwa sama. Haka za su yi ta gayawa junansu wannan magana da su ka jiyo daga sama, har zuwa na ƙasansu, wanda shi kuma zai je ya gayawa Boka cewa abu kaza zai faru a duniya rana kaza a waje kaza. To wani sa'in Aljanin ya kan samu dama ya faɗawa ɗan uwansa zancen da ya jiyo, wani sa'in kuma kafin ya faɗa sai tauraro ya jefe shi, ya kashe shi.
To daga nan sai Bokan ya dinga gayawa mutane cewa abu kaza zai faru rana kaza, sai kuma a ga abun ya faru. Sai ka ji mutane suna cewa 'Ai rannan ya ce da mu abu kaza zai faru, kuma abun ya faru da gaske'. Sai su dinga gasgata shi saboda wannan kalma da aka jiyo daga bakin Mala'iku a sama.
     Bukhari ne ya ruwaito shi, wasu sassansa kuma daga wasu Malaman ne.

https://www.youtube.com/@bashirhalilutv

Acikin wanna ƙissa za mu fahimci cewa

1) Aljanu suna iya zuwa wani waje mai nisan gaske acikin sararin samaniya, ta yadda suke iya jin maganganun da Mala'iku suke tattaunawa akan abubuwan da za su faru a duniya.

2) Aljanu ba sa iya tunkarar Mala'iku domin su samo labarin abinda zai faru a duniya, sai dai suyi masu laɓe, su sato wata kalma ba tare da Mala'ikun sun sani ba.

3) Aljanu da Mala'iku dukkansu ba su san gaibu ba, har sai Allah Ya kira Mala'ika Jibrilu Ya sanar da shi, sannan su sani.

4) Aljanu suna iya kaiwa inda za su ji maganar Mala'iku ne ta hanyar taka kafaɗun junansu, wannan ya hau kan wannan, wannan ya hau kan wannan, har su isa zuwa sama.

5) Ba kowane lokaci ne Aljanu suke samun damar satar maganar Mala'iku ba, domin wani lokacin tauraro yana jifansu, ya kashe su kafin su kawo zancen zuwa duniya.

6) Ainihin maganar da Aljanu su ka jiyo a sama ba ita suke kawowa ƙasa ba, sai sun ƙara  ƙarerayinsu aciki sannan su kawowa Boka, shi ma ya ƙara ƙaryarsa sannan ya sanar da mutanensa.

7) Abinda Bokaye suke gayawa mutane yawanci ƙarya ne, sama da 99% ƙarya ne, sauran kuma irin maganar da aka sato daga Mala'iku ce, sai ka ga  sun faɗi abu kuma ya faru. Shi ne dalilin da ya sa wasu suke gasgata Bokaye. 

 

8) Malamai sun yi bayanin cewa ba kowace magana ce ake barin Aljanu su jiyo ta daga sama ba, misali wahayin da ake kaiwa Annabawa, ba a bari wani Aljani ya san da wannan magana kafin ta je ga Annabin Allah.

Kalli cikakken wannan bayani acikin bidiyo acikin wannan shuɗin rubutun
https://www.youtube.com/@bashirhalilutv.

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruq'yah da bayarda magunguna  na musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts