ƘISSAR HARUTA DA MARUTA. SHIN MALA'IKU NE SU KA KOYAR DA TSAFI?. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

QISSAR HARUTA DA MARUTA

Asalin tsafi.
Shin Mala'iku Ne Su Ka Koyar da Tsafi?

Daga Shafin Sunnah Medicine, Masu Yin Ruq'yah Da Harhada Magunguna na Musulunci. 

Lambar waya 0816260070, 08134434846. 

Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci sunayen Haruta da Maruta sau daya a cikin Alqur'ani mai girma, acikin Suratul Baqarah.

      Ruwayoyi da dama sun zo akan Qissar wadannan sunaye na Mala'iku ko kuma Sarakuna amma dai za mu dauki jigon ruwayar da Ahmad ya fitar acikin Musnad, da kuma ibnu Hibban aciki Sahihinsa daga ibn Umar رضي الله عنهما
sai mu shigar da bayanin sauran ruwayoyin a ciki.

Ga cikakkiyar Qissar :

 Lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da Annabi Adam ﻋﻠﻴﻪ السلام
daga Aljanna zuwa kasan duniya, sai Mala'iku suka dinga cewa "Ya Ubangiji, yanzu ka sanya wadanda za suy 6arna su dinga zubar da jinin junansu a duniya?!, alhali mu muna girmamaKa tare da gode maKa kuma muna kaskantar da kai gareKa?".

Sai Allah Madaukakin Sarki Ya ce "Ni Na san abinda baku sani ba".

Sai su ka ce "Ya Ubangiji, mu fa mun fi yi ma Ka biyayya sama da 'yanAdam, inda mu ne ka saukar da  mu duniya to ba za mu sa6a maka ba".

Sai Allah Mai girma Ya ce musu "To ku kawo Mala'iku guda biyu a cikinku, sai Mu saukar da su kasan duniya, don Mu ga yadda za su yi. (za suy biyayya ko ba za suy ba?!)".

Sai su ka ce "Ya Ubangiji, Ga Haruta da Maruta mun za6e su a kaisu"

.
Sai aka saukar da wadannan Mala'iku biyu zuwa duniya, aka sauke su a garin Babiyla.

Lokacin da aka sauke su sai aka ce musu ga Tsafi nan ku dinga koyawa mutane amma duk wanda ya zo zai koya ku gaya masa in ya aikata ya zama kafuri.

A wata ruwayar kuma an ba su Sihiri ne domin su dinga yiwa mutane gargadi akan su guje shi kada su aikata shi.

To bayan an saukar da su, sai Allah Ya mayar da Zahr', wato wannan babbar tauraruwar da muke gani a kusa da wata, sai aka mayar da ita siffar mace.

Sai ta zo wajensu a sura kyakkyawa.
 Da su ka ganta sai su ka nemeta. Sai ta qi amincewa, ta ce musu "Saidai in za ku kafurta to zan yarda da ku".

Da su ka ji haka sai su ka ce basu yarda ba.
Sai ta fi, ta sake dawowa da wani jariri a hannunta. 
 Sai su ka kuma nemarta. Sai ta qi amincewa,  ta ce "Saidai in za ku kashe wanan yaron, to zan ba ku hadin kai".

Sai su ka ce basu yarda ba. Sai ta tafi, ta sake dawowa da tukunyar giya a hannunta.

Suka nemeta. Sai ta ce bata yarda ba sedai in za su sha giya tukuna. Sai su ka yarda su ka sha giyar.

Bayan sun sha sai maye ya kama su, su kay zina da wannan matar sannan kuma suka kashe wannan jaririn.

Lokacin da suka farka sai Allah Ya tambayesu alqawarin da sukay akan ba za su sa6a masa ba. 

Daga nan sai aka ba su za6i akan su za6i irin azabar da  za ay musu. Shin a duniya suke so ay musu azaba ko kuma a bari sai an je Lahira?!.

Sai suka ce ai azabar Lahira bata karewa, mun za6i ta duniya. 

Shikenan sai aka kai daya inda rana take 6ullowa. Kullum idan rana ta 6ullo sai ta tafasa masa kansa dayan kuma sai aka kai shi inda rana take faduwa, kullum in rana zata fadi sai ta kona shi.

Ita kuma Zahra' sai aka mayar da ita tauraruwa ta koma sama.

To a lokacin ne aka ba su sihiri, (bisa sa6anin ruwaya).

Sai aka ce duk wanda ya zo yana so su koya, to su koya masa. 

Sai suka dinga koyawa mutane da Aljanu yadda ake raba tsakanin miji da mata amma basa koyawa kowa sai sun ce masa "Tabbas mu fitina ne!, don haka kada ka kafurta".
Ma'ana duk wanda ya koyi sihiri a wajensu to ya zama Kafiri. 

In Mutum ko Aljan ya yarda zai kafurta sai su koya masa.
Daga nan sai harkar Sihiri da Tsafi su ka yadu a tsakanin mutane da Aljanu.

Malamai sun yi raddi sosai akan wannan qissa musamman kasancewar Mala'iku basa sa6o da kuma maganar cewa su ne suka koyar da tsafi sannan ruwayoyin yawanci Isra'iyliyyat ne, ma'ana daga wajen Yahudawa aka samo su, sedai abinda aka samu na 6angarorin qissar daga Alqur'ani da kuma ruwayar ibnu Umar daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
kamar yadda muka ambata.

.
Harkar Bokanci, Sihiri, Tsafi, Surkulle, Rufa-ido, Tsibbace-tsibbace da makamantansu, sun samu shahara sosai da kar6uwa a wajejen aiko Annabi Sulaiman عليه السلام
shi yasa ya zamto yana daga cikin manyan abubuwan da Annabi Sulaiman عليه السلام yay fada  da su kuma ya yaqi masu aikata shi.

Sannan wannan harka ta samu kar6uwa ne da matsayi da shiga zukatan al'umma a wajejen zamanin Annabi Musa عليه السلام،
inda a lokacin ake ganin wanda ya iya sihiri tamkar wani shugaba kuma wani abin ay wa biyayya sannan abin tsoro.

Za mu kawo cikakkiyar qissar yadda Annabi Sulaiman عليه السلام ya yaqi masihirtan zamaninsa da kuma dalilin da yasa bayan ya  yi wafati Shaidanu suka ce ya mulki duniya ne ta hanyar tsafi.

Sannan za mu sake duba qissar Haruta da Maruta tare da bayanin yadda Annabi Musa ya fuskanci matsafan zamaninsa.

Duk wannan zai zo insha Allahu a cikin posting din mu mai taken "ASALIN TSAFI", Domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada acikin Suratuz Zariyari cewa:

.
ﻓَﻔِﺮُّﻭﺍ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻭَﻻ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻬﺎً ﺁﺧَﺮَ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻛَﺬَﻟِﻚَ ﻣَﺎ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻣِﻦْ ﺭَﺳُﻮﻝٍ ﺇِﻻَّ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺳَﺎﺣِﺮٌ ﺃَﻭْ ﻣَﺠْﻨُﻮﻥٌ ‏[ ﺍﻟﺬﺭﻳﺎﺕ :50 - 52] .
.
.
Ma'ana: "Kamar haka ne (Su wadannan mutanen) babu wani Annabi da ya zo wajen wadanda suka gabace su face sai sun ce masa mai Sihiri ko kuma mai hauka".
.
Wannan ayah tana nuna cewa tun zamanin Annabi Nuhu ﻋﻠيﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
duk da cewa shi ne farkon Manzanni, duk Annabin da Allah Ya aiko sai Kafurai sun ce masa mai sihiri ne. Kenan tun a lokacin ana yin sihiri.

Wasu Malaman kuma suna ganin sihiri ya samo asali ne daga hannun Aljanu kuma dalilansu sun fi karfi gaskiya.

Insha Allahu za mu kawo cikakken bayani a cikin "ASALIN TSAFI", wannan bayani zai zo nan gaba kadan da yaddar Allah.

Sunnah Medicine     08162600700.

ASALIN TSAFI
.
Bayani Daga Tafsirin "Wattaba'uw".

Daga Shafin Sunnah Medicine, Masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. 

Lambar waya 08162600700.

 A cikin Aya ta 102, cikin suratul Baqarah, Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu labarin Yahudawa, wadanda Allah Ya ba su littafi amma sai sukay watsi da shi, suka koma bin abinda Shaidanu suke fada na qarya akan Mulkin Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
cewa shi Annabi Sulaiman ba Annabi bane, kawai wani matsafi ne da ya mallaki duniya ta hanyar sihiri da tsafi da bokanci. "Wal iyazu billah".

Ya zo a cikin kissar Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ingantacciya cewa: Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ya gaji mahaifinsa Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
wanda Allah Ya hore masa tsuntsaye da duwatsu suna zuwa wajensa idan yana ambaton Allah suna taya shi.
Kuma Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
shi ne Allah Ya hore masa karfe yana sarrafa shi yadda yake so. 

Malamai suka ce komai karfin karfe da hannu Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
yake lankwasa shi ya kera abinda yake so da shi. Domin shi ne ya fara kera kayan amfani na karfe irinsu wuqa da kayan noma da kuma rigar sulke ta bakin karfe da sauran kayan yaqi, kuma duk da hannu yake kerawa.

Annabi Dawuda kakkarfa ne, domin shi ne ya kashe Jaluta a yakinsu da Daluta, sai jama'a suka za6e shi ya zama Sarkinsu.

To shi Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
shi ne ya gaji Mahaifinsa Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ta fuskar ilimi da kuma baiwa da mu'uzija da Allah Yay masa sannan ya gaji sarauta kuma shi ma Allah Ya za6e shi a matsayin Annabi.

Allah Ya yi wa Annabi Sulaiman baiwa, Ya hore masa abubuwan halitta baki daya kuma Ya sauqaqe masa su.

Allah Ya hore masa iska. Duk inda yake so ya je, sai kawai ya shinfida dadduma, mutane su hau kai da dabbobi da kayan abinci da dukkan kayan bukatunsu, sai kawai ta lula da su sama ta kai su.

Allah Ya ba mu labarin cewa ita wannan iska kakkarfa ce, tana gudana da umarnin Annabi Sulaimam عليه السلام
sannan gudunta wata guda ne tafiyarta sannu sannu ma wata guda ne.

Allah Ya hore masa tsuntsaye wadanda yake saka su suy masa aiki irinsu Alhud'huda wanda muka ta6a kawo muku kissarsa.

Haka nan Allah Ya hore masa Aljanu suna yi masa aikin gine-gine da kere-kere kuma suna yin nutso a cikin kogi suna debo masa ma'adanan karkashin kasa irinsu 'gold' da dai sauransu.

A cikin Aljanun akwai wadanda yake sa wa su suy masa aiki mai wahala irin wanda mutane ba za su iya ba, kamar dauko wani abu daga wani waje mai nisa da dai sauransu. 

Allah ya fada a Alqur'ani cewa dukkan Aljani ko Shaidanin da Annabi Sulaiman ya saka aiki amma yay gardama to Allah Zai dandana masa azaba mai tsanani. Malami suka ce, an wakilta wani Mala'ka ne a tare da shi, yana dauke da ankwa a hannusa. Duk Aljani ko Shaidanin da Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ya sa shi aiki ya qi, to wannan Mala'ikan mai ankwa shi zai kama shi ya hukunta shi.

Allah Ya horewa Annabi Sulaiman ji da fahimtar maganar tsuntsaye da kwari da sauran halittu.

Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ya mulki duk duniya ne daga farkonta zuwa karshenta, ba wata qasa guda daya ba.

 Malaman tarihi suka ce duk duniya Sarakuna biyu ne kawai suka mulki duniya baki dayanta, daga Annabi Sulaiman عليه السلام
sai Annabi Zulqarnaini عليه السلام
wanda muka kawo muku tarihinsa a kwanakin baya.

Annabi Sulaiman ya yi fada da masu aikata sihiri da tsafi kuma ya yake su. Domin kasuwar matsafa ta fara kar6uwa ne a duniya a wajejen aiko Annabi Musa ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
inda mutane suke daukar wanda ya iya tsafi a matsayin wani babba abin girmamawa da kuma yi wa biyayya .

Bayan matsafan Fir'auna sun musulunta, harkar tsafi ta ci gaba da yaduwa a hannun wasu mutane har zuwa zamanin Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ .

Ya zo a qissar Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
cewa "Da akwai wasu mutane da suke aikata tsafi a zamaninsa, sai yasa aka kamo masa su ya hukunta su ya kwace takardun da suke tsafin da su, sai ya binne takardun a karkashin kujerar mulkinsa.

Bayan tsawon shekaru har Annabi Sulaiman ya bar duniya. Sai Shaidan La'ananne ya zo ya cewa mutane "Ai Annabi Sulaiman ba Annabi bane. Kawai ya mallaki duniya ne da mutane da Aljanu da iska da tsuntsaye da suaran abubuwa ta hanyar Tsafi da sihiri.

Da mutane suka ji haka sai sukay masa tsawa suka ce "Karya kake"

Sai Shaidan ya ce "Idan na nuna muku inda ya 6oye takardun tsafin na sa za ku yarda? ".
Sai suka ce za su yarda.

Sai ya je ya nuna musu karkashin kujerar Annabi Sulaiman. Sai suka haqa, sai kuwa suka samu wadancan takardu da ya kwace daga hannun wadancan mutane.

Sai suka ce ashe kuwa da gaske ne Sulaiman tsafi ya ke (wal iyazu billah).

Daga nan sai su ka koma harkar tsafi su ka jefar da littafin Allah a bayan-bayansu, us ka bi abinda Shaidanu suke fada a kan Mulkin Annabi Sulaiman عليه السلام. 

Shi ne Allah Ya ce:
.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺤﻴﻢ
ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻣَﺎ ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ....
.
Ma'ana:
"Kuma su ka bi abinda Shaidanu suke karantawa akan mulkin Annabi Sulaiman (cewa ya mallaki duniya ta hanyar tsafi),

 kuma Annabi Sulaiman ai bai kafurta ba (domin dukkan mai yin tsafi kafiri ne), saidai su Shaidanun (masu fadar wannan magana) su ne  sunka kafurta..."

ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ ﻭَﻣَﺎ ﺃُﻧْﺰِﻝَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﻜَﻴْﻦِ ﺑِﺒَﺎﺑِﻞَ ﻫَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤَﺎﻥِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻘُﻮﻻ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻓَﻼ ﺗَﻜْﻔُﺮْ ﻓَﻴَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣَﺎ ﻳُﻔَﺮِّﻗُﻮﻥَ ﺑِﻪِ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﻤَﺮْﺀِ ﻭَﺯَﻭْﺟِﻪِ ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢْ ﺑِﻀَﺎﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻟَّﺎ ﺑِﺈِﺫْﻥِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻳَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﻳَﻀُﺮُّﻫُﻢْ ﻭَﻻ ﻳَﻨْﻔَﻌُﻬُﻢْ ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻋَﻠِﻤُﻮﺍ ﻟَﻤَﻦِ ﺍﺷْﺘَﺮَﺍﻩُ ﻣَﺎ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺂﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦْ ﺧَﻼﻕٍ ﻭَﻟَﺒِﺌْﺲَ ﻣَﺎ ﺷَﺮَﻭْﺍ ﺑِﻪِ ﺃَﻧْﻔُﺴَﻬُﻢْ ﻟَﻮْ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ
.
Allah Ya ce "(Su wadannan Shaidanu da suka kafirce) suna koyawa mutane sihiri da kuma abinda aka saukarwa Haruta da Maruta a (garin) Babila (Haruta da Maruta wasu Mala'iku ne da suke koyawa mutane yadda ake yin tsafi), amma ba sa koyawa kowa sai sun gaya masa cewa "Mu fa fitina ne,  kada ka kafurta"

Sai su dinga koyar yadda za su raba tsakanin miji da mata,  amma ba sa iya cutar da kowa sai da izinin Allah. 

 Sannan suna koyar abinda zai cutar da su ne , ba zai amfanesu ba. 

Hakika tabbas sun san cewa wAllahi duk wanda ya sayi tsafi yake yinsa to ba shi da rabo a lahira kuma tir da abinda suka siya da kansu,  da suna da ilimi (da sun gane). 

{Suratul Baqarah,  Ayah ta 102}.

A cikin wannan ayah Allah Ya ba mu kissar Haruta da Maruta,   Shafin Sunnah Medicine ya kawo cikakkiyar wannan kissa.  

Sannan Ya yi maganar masu koyar sihirin da suke raba tsakanin miji da matarsa.  Shi ma mun yi bayani akan wannan sihiri da yadda mutum zai gane an yi masa da kuma hanyoyin warware shi.  

Sannan Allah Ya yi bayanin cewa duk wanda ya sayi tsafi,  ma'ana ya koya kuma yake aikatawa,  to ba shi da rabo a lahira.  
Allah Ya kiyaye mu. 
Daga shafin Bashir Halilu Idris. 
Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts