YADDA ZA KA GANE ALJANI YA FITA DAGA JIKIN MUTUM BAYAN RUƘIYYAH. Daga Dr. shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Wani sa'in akan yi alƙawari da Aljani cewa zai tafi daga jikin mara lafiya kuma a ba shi umarni ya fita nan take, amma in bai yi niyyar fita ba sai ya laɓe a jikin mara lafiya, a zuwan ya tafi. Wani kuma ana cikin gudanar da Ruƙiyyar sai Aljanin yay lamfo, sai a ɗauka ya gudu ne, alhali yana na. Ga wasu daga cikin alamomin da za ka iya ganewa idan Aljani ya fita ko kuma laɓewa ya yi. 1- Raguwar ƙarfi ko kasala nan take. Wato idan Aljanin mai azababben ƙarfi ne ko yana buge-buge, idan ya fita za ka ga jikin mutum ya yi lakwaf, kamar an zare jijiyoyin jikinsa. 2- Bacci na ɗan lokaci. Musamman idan Aljanin ya kasance a ƙwaƙwalwar mutum ya ke zama, da zarar ya fita sai mutum ya kwanta, ya yi bacci na ƴan mintuna nan take sannan ya farka, ya cigaba da harkokinsa. 3- Dawowa cikin hayyaci. Za ka ga mutum ya dawo cikin hayyacinsa nan take har ma yana tambayar wa ya kawo shi nan wajen ko kuma me ya faru da...