Posts

Showing posts with the label watan azumi

GAME DA SALLOLIN TAHAJJUDI DA TARAWIHI. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Image
GAME DA SALLOLIN TAHAJJUDI DA TARAWIHI.  * 1- Ya tabbata Annabi (SAW) yana kara kokari na ibada a cikin goman karshe na Ramadhan, kokarin da ba ya yin irinsa a wasu kwanakin. عن عائشة رضي الله عنها قالت: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ يَجْتَهِدُ فِي رَمضانَ مَالا يَجْتَهِدُ في غَيْرِهِ، وَفِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ منْه مَالا يَجْتَهدُ في غَيْرِهِ" رواهُ مسلمٌ. * 2- Asali Allah Ya kwaɗaitar a yi sallar Tahajjudi har ma ya ce ya kusanta Allah Ya tasheka a wani matsayi mai girma.  {وَمِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَكَ } [الإسراء: 79] Tahajjudi shi ne rashin bacci da raya dare da Sallah da Ibada.  * 3- Annabi (SAW ) ya kasance yana raya dare da Ibadau a goman karshe kamar yadda ya zo a Hadisin A’isha (SAW ) cikin Bukhari da Muslim. وعَنْهَا رَضَيَ اللَّه عَنْهَا، قَالَتْ: كَانَ رسُول اللَّهِ ﷺ: إِذا دَخَلَ العَشْرُ الأَوَاخِرُ مِنْ رمَضَانَ، أَحْيا اللَّيْلَ، وَأَيْقَظَ أَهْلَه، وجَدَّ وَشَدَّ المِئزرَ متفقٌ عَلَيهِ. * An  sunnanta mana yin Jam’i a Sallar...

TSAYUWAR DARE TARE DA LIMAN A WATAN RAMADAN.

Image
TSAYUWAR DARE TARE DA LIMAN A WATAN RAMADAN.  An karɓo daga Abiy Zarrin (RA) ya ce "Mun yi Azumi tare da Manzon Allah (SAW) a watan Ramadhana, bai tsaya da mu wani abu ba a wannan watan (don yin sallolin nafila), har sai da ya rage saura kwana bakwai, sai ya tsaya da mu, har sai da ɗaya bisa ukun dare ya shuɗe.     Da ya zama saura kwana shida bai tsaya da mu ba, da ya rage saura kwana biyar sai ya tsaya da mu har sai da rabin dare ya ahuɗe.  Sai na ce "Ya Rasulallahi da ka yi mana nafilar tsayuwar  wannan daren gaba ɗaya", sai ya ce "Ai haƙiƙa idan mutum yay sallah tare da liman har ya idar to za a lissafa masa (lada) na tsayuwar wannan daren".   Da ya rage kwana huɗu bai tsaya da mu ba. Da ya rage saura kwana uku sai ya tara ahalinsa da matansa da sauran jama'a, ya tsaya da mu har sai da mu ka ji tsoron lokacin sahur zai ƙuɓuce mana. Daga nan kuma bai kuma tsayawa ragowar kwanakin watan ba".      - Abu Zarrinil Giffariy....