AMFANIN DAFAFFEN ƘWAI GA YARA
AMFANIN DAFAFFEN ƘWAI GA YARA.
Ƙwai na da matuƙar muhimmanci da ƙara lafiya ga yara da manya, mata da maza amma a wannan darasin za mu duba amfanin Ƙwai ne ga yara.
Ƙwai na ɗauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen ƙara ƙarfin karfin garkuwar jikin yara musamman ƴan kasa da shekaru 5.
1. Dafaffen Ƙwai na buɗe ƙwaƙwalwar yaro ta yadda ya kan taimakawa yaro ya zama mai kaifin ƙwaƙwalwa.
2. Dafaffen Ƙwai na ɗauke da sinadarin ‘lutein’ da kuma ‘zeaxanthin’ waɗanda ke ƙara lafiyar idanuwan yaro.
3. Dafaffen Ƙwai na ƙara ƙarfin ƙashi a jikin yara ƙanana domin yana ɗauke da sinadarin 'Vitamin D'.
4. Dafaffen Ƙwai na ɗauke da sinadarorin leucine, phenylalanine, histidine, isoleucine, lycine, methionine, threonine, tryptophan da kuma 'valine' waɗanda ke taimakawa wajen gina jikin yaro da kuma ƙara masa jini.
5. Dafaffen Ƙwai na kara girman ƙumba da gashin kan yara.
6. 'Omega-3' da ke cikin dafaffen kwai na taimakawa wajen buɗe ƙwaƙwalwar yaro kuma zai yi saurin gane abubuwa da fahimtar karatu
7. Dafaffen Ƙwai na ɗauke da sinadarin 'iron' wanda ke taimakawa wajen samar da issashen jini a jikin yaro.
Ƙwai wanda aka dafa ya fi amfani a jikin mutum sama da wanda aka soya shi domin soya Ƙwai yana kashe wasu sindarai masu muhimmanci da yawa acikinsa.
Inda hali kullum ka baiwa ɗanka dafaffen Ƙwai guda ɗaya ko rabi ko kuma ya zama abinda za a dinga ba shi yana ciki akai-akai.
Idan kuna bukatar sanin amfanin wani magani ko abinc ko yadda ake sarrafa wani magani sai ku yi magana ta wajen comment, za mu kawo muku insha Allahu.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment