AMFANIN SHINKAFA A JIKIN ƊAN ADAM. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
AMFANIN SHINKAFA A JIKIN ƊAN ADAM.
Shinkafa, wacce ta kusa zama abincin duk duniya, tana sanarwa da biliyoyin mutanen duniya wasu sinadarai masu matuƙar muhimmanci wajen gina rayuwarsu ta dalilin mayar da ita abincinsu da su ka yi.
Ga kaɗan daga amfanin shinkafa a jikin mutum.
1. Daidaita suga acikin jini.
Nau'in shinkafar nan mai ruwan ƙasa (brown rice) tana taimakawa mutane masu 'diabetes' wajen daidaita suga da ke cikin jininsu. Nau'in shinkafa mai ruwan ƙasa na da ƙarancin 'glycemic index' in ka kwatanta ta da farar shinkafa, wanda hakan ke nufin ba zata ta'azzara sugan cikin jini sosai ba.
2. Ƙara lafiyar zuciya.
Shinkafa musamman mai duhun nan (brown rice) na ɗauke da 'fiber' mai yawa wanda ke aiki wajen rage 'cholesterol' wato kitse mara amfani a jikin mutum, yana rage haɗarin kamuwa da ciwon zuciya da shanyewar ɓarin jiki. Haka nan tana dauke da 'vitamins' waɗanda ke taimakawa wajen zagayawar jini a jikin mutum da dai sauran ayyuka kamar baiwa jiki kuzari da dai sauransu.
3. Rage haɗarin kamuwa da cutar Kansa (cancer).
Shinkafa, musamman mai ruwan ƙasa, na ɗauke da wani sinadari da ake kira 'phenolic' wanda galibi ake samunsa acikin tsirrai, wannan sinadari na yaƙi da ƙwayoyin cutar da ke haifar da ciwon Kansa.
4. Lafiyar jiki wajen narkar da abinci.
Shinkafa mai ruwan ƙasa na taimakawa masu fama da lalurar narkewar abinci wajen sauƙaƙa narkar da abincin acikin jikinsu saboda 'fiber' da ke cikinta.
5. Sinadaran ƙara lafiyar jiki.
Shinkafa mai ruwan ƙasa na da ɗauke da sinadaran da ke kula da lafiya ko suke ɗauke da lafiyar gaba ɗaya, kamar:
- Vitamin B1 (thiamine).
- Vitamin B6 (pyridoxine).
- Magnesium.
- Phosphorus.
- Selenium.
- Manganese.
Amma a fahimta, farar Shinkafa daidai ta ke da Shinkafa ruwan ƙasa wajen ƙara kuzari da wasu abubuwa masu amfani, saidai kash! ana asarar yawancin amfanin shinkafa ne yayinda aka ɓare Shinkafa kuma aka mayar da ita daga ruwan ƙasa ta koma fara.
Farar shinkafa da jar shinkafa ko ruwan ƙasa dukkansu suna da amfani amma wacce ba a mayar da ita fara ba ta fi amfani da ƙara lafiya. Wannan duhun da ake cirewa a mayar da ita mai haske shi ne maganin da ake cirewa ana baiwa dabbobi ko a zubar.
Idan kuna bukatar sanin amfanin wani magani ko wani abinci sai ku rubuta a wajen comment insha Allahu za mu kawo muku.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment