MAGAGIN BACCI
MAGAGIN BACCI Da abubuwan da suke kawoshi da kuma yadda ake maganinsa. Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruq'yah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. Ma'anar Magagin Bacci itace:- Mutum ya dinga magana ko tafiya ko yin wani aiki da jikinsa, alokacin da yake cikin bacci, ba tare da ya farka ba. Yawanci dai Magagi ba ya wuce mintuna biyar zuwa sha biyar yake sakin mutane. Magagin bacci, kamar yadda binciken zamani ya nuna, yana da alaqa da matsalar Dannau (karanta cikakken bayani akan Dannau acikin wannan shudin rubutun http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/04/dannau-dannau-lokacin-bacci-aljani-mai.html ) inda binciken ya nuna cewa, a yayinda mutum yake bacci, to kwakwalwarsa da gangar jikinsa dukkansu suna hutawa ne, idan ya tashi farkawa kuma sai su farka gaba daya. To idan aka samu matsala, kwakwalwar mutum ta farka, gangar jikinsa kuma bata farka ba, sai mutum ya ji ya dawo cikin hanka...