JINNUL ASHIƘ. ALJANI MAI HANA AURE KO MAI KWANCIYA DA MATAN MUTANE. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

JINNUL ASHIQ
Aljani mai hana aure ko mai kwanciya da matan mutane
ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ
Idan aka ce Jinnul Ashiq na nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji.

Daga shafin Dr. Bashir Kano, 
lambar waya 08162600700, 08134434846. 

Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma in ta samun cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau'in Aljani shi muke kira
JINNUL ASHIQ ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ

Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne mutum yake yi da su.

YADDA MUTUM ZAI GANE YANA DA AL-JANIN DARE

_Ta 6angaren namiji:-_
1-rashin sha‘awar aure ko jima'i sam-sam.
2-‘kin mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i, alhali kuma haka kawai ma yana tashi.
3-‘kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana
iya zama a cikin marainan mutum.
4-saurin gajiya, yayin jima‘i da rashin iya komawa
5-jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in
haihuwa yayin jima‘i.
6-rashin cimma bukatar jima,i.
7- in ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka.
8- da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo
tun kafin ka fara.
9- komawar gaba da maraina su shige ciki.
10- yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili, faduwar
gaba, da dai sauran su.
11- haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka.
12- Yawan mafarki kana saduwa da wata mata.
13- Yawan samun matsaloli aduk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace.
14- Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai.
15- Matsananciyar sha'awa da tsoron mata.
Da dai sauransu.

YADDA MACE ZATA GANE AL-JANI YA AURETA

1- yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi acikin.
2- a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta
ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al'adarta bane.
3- jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.
4- suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba
ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta
ba.
5- matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.
6-‘kin yarda da jima‘i.
7- Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban.
8- yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da
taron suna.
9- ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa
a cikinki ta ya fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.
10- yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen
dalili ba.
11- yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.
12- jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana
dada girma, amma in likitoci suka auna za su ce ba
su ga komai ba.
13- rashin son yin magana da kowa da jin haushin
mutane haka kawai.
14- tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha'awar wasu mazan.
15- Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen
gaba.
16- Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba.
17- Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi.
18- In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suy mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu.
19- Za ta dinga yawan zaman a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane.
20- Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.
21- Yawan ciwon kai da yin jiri.
22- Faduwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa.
25- Iadan mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka.
Da dai alamomi da yawa.

Daga shafin Dr. Bashir. Muna yin rukiyyah don cire Aljan kuma muna hada magungunan karya sihiri da na jinnu. 

Lambar waya 08162600700.

Comments

Popular Posts