Posts

Showing posts with the label Cuttukan

CUTUTTUKAN MATA DA MAGUNGUNANSU

1- CIWON NONO 2- GOYON CIKI 3- JININ HAILA 4- RASHIN SHA'AWA 5- ILLOLIN MASTURBATION 6- MAGUNGUNAN GARGAJIYA 7- MAGUNGUNAN ASIBITI CIWON NONO GA MATA. Wato Sanqaran Mama ko kuma Kansar mama. MA'ANAR ciwon nono shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin nonon mace, wandanda ke haddasa ciwo da canja yanayin nonon mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yay sanadin a yanke shi gaba daya. YADDA AKE DAUKAR CIWON Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono. 1- Shekaru ko tsufa.     Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono. 2- Sinadarin 'iyistirogen', idan yay yawa ajikin mace. 3- Fara jinin al'ada kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono daga baya. 4- Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al'ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono. 5- Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su...