Posts

Showing posts with the label magungunan misulunci

AMFANIN ALBASA DA TAFARNUWA DA CITTA

Image
AMFANIN ALBASA DA TAFARNUWA DA CITTA Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar wayarmu 0816260070. Hakika albasa na da tsohon tarihi duba da yadda al'umma ke amfani da ita a harkokin abincinsu da kuma magani. Masana sun yi ittifakin cewa albasa na da wasu muhimmman sanadarai da ke taimakawa wajen gina jikin dan-adam, baya ga haka sinadaran da albasa ke kunshe da su na da tasiri kan wasu cututtukan jiki. Shekaru da yawa da su ka shude, al'ummomin Duniya daban-daban ke amfani da albasa don magance cututtukan da ke damun su, kamar ciwon sanyin kashi, mura, ciwon makogoro da gabobi da sauran su. 1. Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro.          Daga cikin amfanin albasa ga dan-adam akwai maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro. Duk wanda ke fama da daya ko duk ciwon da muka zana a sama, musamman wanda ke fama da tari ko mura mai tsanani, ya nemi man Albasa cikin babban cok...