ƘISSAR ANNABI SULAIMAN ALAHIS SALAM. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

ƘISSAR ANNABI SULAIMAN (AS). 
YAUSHE AKA FARA TSAFI A DUNIYA?. 

   A cikin Aya ta 102, cikin suratul Baqarah, Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu labarin Yahudawa, wadanda Allah Ya ba su littafi amma sai sukay watsi da shi, suka koma bin abinda Shaidanu suke fada na qarya akan Mulkin Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
cewa shi Annabi Sulaiman ba Annabi bane, kawai wani matsafi ne da ya mallaki duniya ta hanyar sihiri da tsafi da bokanci. "Wal iyazu billah".

 Ya zo a cikin kissar Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ingantacciya cewa: Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ya gaji mahaifinsa Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
wanda Allah Ya hore masa tsuntsaye da duwatsu suna zuwa wajensa idan yana ambaton Allah suna taya shi.
Kuma Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
shi ne Allah Ya hore masa karfe yana sarrafa shi yadda yake so. 

      Malamai suka ce komai karfin karfe da hannu Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
yake lankwasa shi ya kera abinda yake so da shi. Domin shi ne ya fara kera kayan amfani na karfe irinsu wuqa da kayan noma da kuma rigar sulke ta bakin karfe da sauran kayan yaqi, kuma duk da hannu yake kerawa.

     Annabi Dawuda kakkarfa ne, domin shi ne ya kashe Jaluta a yakinsu da Ɗaluta, sai jama'a suka za6e shi ya zama Sarkinsu.

     To shi Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
shi ne ya gaji Mahaifinsa Annabi Dawuda ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ta fuskar ilimi da kuma baiwa da mu'uzija da Allah Yay masa sannan ya gaji sarauta kuma shi ma Allah Ya za6e shi a matsayin Annabi.

    Allah Ya yi wa Annabi Sulaiman baiwa, Ya hore masa abubuwan halitta baki daya kuma Ya sauqaqe masa su. Allah Ya hore masa iska. Duk inda yake so ya je, sai kawai ya shinfida dadduma, mutane su hau kai da dabbobi da kayan abinci da dukkan kayan bukatunsu, sai kawai ta lula da su sama ta kai su.

     Allah Ya ba mu labarin cewa ita wannan iska kakkarfa ce, tana gudana da umarnin Annabi Sulaimam عليه السلام
sannan gudunta wata guda ne tafiyarta sannu sannu ma wata guda ne. 
Allah Ya hore masa tsuntsaye wadanda yake saka su suy masa aiki irinsu Alhud'huda wanda muka ta6a kawo muku kissarsa.
Haka nan Allah Ya hore masa Aljanu suna yi masa aikin gine-gine da kere-kere kuma suna yin nutso a cikin kogi suna debo masa ma'adanan karkashin kasa irinsu 'gold' da dai sauransu.

   A cikin Aljanun akwai wadanda yake sa su suy masa aiki mai wahala irin wanda mutane ba za su iya ba, kamar dauko wani daga wani waje mai nisa da dai sauransu. 

    Allah ya fada a Alqur'ani cewa dukkan Aljani ko Shaidanin da Annabi Sulaiman ya saka aiki amma yay gardama to Allah Zai dandana masa azaba mai tsanani. Malami suka ce, an wakilta wani Mala'ka ne a tare da shi, yana dauke da ankwa a hannusa. Duk Aljani ko Shaidanin da Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ya sa shi aiki ya qi, to wannan Mala'ikan mai ankwa shi zai kama shi ya hukunta shi.

   Allah Ya horewa Annabi Sulaiman ji da fahimtar maganar tsuntsaye da kwari da sauran halittu.

   Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ya mulki duk duniya ne daga farkonta zuwa karshenta, ba wata qasa guda daya ba.

     Malaman tarihi suka ce duk duniya Sarakuna biyu ne kawai suka mulki duniya baki dayanta, daga Annabi Sulaiman عليه السلام
sai Annabi Zulqarnaini عليه السلام
wanda muka kawo muku tarihinsa a kwanakin baya.

    Annabi Sulaiman ya yi fada da masu aikata sihiri da tsafi kuma ya yake su. Domin kasuwar matsafa ta fara kar6uwa ne a duniya a wajejen aiko Annabi Musa ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
inda mutane suke daukar wanda ya iya tsafi a matsayin wani babba abin girmamawa da kuma yi wa biyayya .

    Bayan matsafan Fir'auna sun musulunta, harkar tsafi ta ci gaba da yaduwa a hannun wasu mutane har zuwa zamanin Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ .

   Ya zo a qissar Annabi Sulaiman ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
cewa "Da akwai wasu mutane da suke aikata tsafi a zamaninsa, sai yasa aka kamo masa su ya hukunta su ya kwace takardun da suke tsafin da su, sai ya binne takardun a karkashin kujerar mulkinsa.

   Bayan tsawon shekaru har Annabi Sulaiman ya bar duniya. Sai Shaidan La'ananne ya zo ya cewa mutane "Ai Annabi Sulaiman ba Annabi bane. Kawai ya mallaki duniya ne da mutane da Aljanu da iska da tsuntsaye da suaran abubuwa ta hanyar Tsafi da sihiri.

Da mutane suka ji haka sai sukay masa tsawa suka ce "Karya kake"

Sai Shaidan ya ce "Idan na nuna muku inda ya 6oye takardun tsafin na sa za ku yarda? ".
Sai suka ce za su yarda.

Sai ya je ya nuna musu karkashin kujerar Annabi Sulaiman. Sai suka haqa, sai kuwa suka samu wadancan takardu da ya kwace daga hannun wadancan mutane.

Sai suka ce ashe kuwa da gaske ne Sulaiman tsafi ya ke (wal iyazu billah).

   Daga nan sai suka koma harkar tsafi suka jefar da littafin Allah a bayan-bayansu suka bi abinda Shaidanu suke fada a kan Mulkin Annabi Sulaiman عليه السلام. 

Shi ne Allah Ya ce:

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺤﻴﻢ
ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﻣَﺎ ﺗَﺘْﻠُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦُ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﻠْﻚِ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻣَﺎ ﻛَﻔَﺮَ ﺳُﻠَﻴْﻤَﺎﻥُ ﻭَﻟَﻜِﻦَّ ﺍﻟﺸَّﻴَﺎﻃِﻴﻦَ ﻛَﻔَﺮُﻭﺍ ....
.
Ma'ana:
"Kuma su ka bi abinda Shaidanu suke karantawa akan mulkin Annabi Sulaiman (cewa ya mallaki duniya ta hanyar tsafi),

 kuma Annabi Sulaiman ai bai kafurta ba (domin dukkan mai yin tsafi kafiri ne), saidai su Shaidanun (masu fadar wannan magana) su ne  kafurta..."

ﻳُﻌَﻠِّﻤُﻮﻥَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺍﻟﺴِّﺤْﺮَ ﻭَﻣَﺎ ﺃُﻧْﺰِﻝَ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﻠَﻜَﻴْﻦِ ﺑِﺒَﺎﺑِﻞَ ﻫَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎﺭُﻭﺕَ ﻭَﻣَﺎ ﻳُﻌَﻠِّﻤَﺎﻥِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﻘُﻮﻻ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻓِﺘْﻨَﺔٌ ﻓَﻼ ﺗَﻜْﻔُﺮْ ﻓَﻴَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣِﻨْﻬُﻤَﺎ ﻣَﺎ ﻳُﻔَﺮِّﻗُﻮﻥَ ﺑِﻪِ ﺑَﻴْﻦَ ﺍﻟْﻤَﺮْﺀِ ﻭَﺯَﻭْﺟِﻪِ ﻭَﻣَﺎ ﻫُﻢْ ﺑِﻀَﺎﺭِّﻳﻦَ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﺃَﺣَﺪٍ ﺇِﻟَّﺎ ﺑِﺈِﺫْﻥِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻳَﺘَﻌَﻠَّﻤُﻮﻥَ ﻣَﺎ ﻳَﻀُﺮُّﻫُﻢْ ﻭَﻻ ﻳَﻨْﻔَﻌُﻬُﻢْ ﻭَﻟَﻘَﺪْ ﻋَﻠِﻤُﻮﺍ ﻟَﻤَﻦِ ﺍﺷْﺘَﺮَﺍﻩُ ﻣَﺎ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺂﺧِﺮَﺓِ ﻣِﻦْ ﺧَﻼﻕٍ ﻭَﻟَﺒِﺌْﺲَ ﻣَﺎ ﺷَﺮَﻭْﺍ ﺑِﻪِ ﺃَﻧْﻔُﺴَﻬُﻢْ ﻟَﻮْ ﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ

Allah Ya ce "(Su wadannan Shaidanu da suka kafirce) suna koyawa mutane sihiri da kuma abinda aka saukarwa Haruta da Maruta a (garin) Babila (Haruta da Maruta wasu Mala'iku ne da suke koyawa mutane yadda ake yin tsafi), amma ba sa koyawa kowa sai sun gaya masa cewa "Mu fa fitina ne,  kada ka kafurta"

Sai su dinga koyar yadda za su raba tsakanin miji da mata,  amma ba sa iya cutar da kowa sai da izinin Allah. 

 Sannan suna koyar abinda zai cutar da su ne , ba zai amfanesu ba. 

Hakika tabbas sun san cewa wAllahi duk wanda ya sayi tsafi yake yinsa to ba shi da rabo a lahira kuma tir da abinda suka siya da kansu,  da suna da ilimi (da sun gane). 

{Suratul Baqarah,  Ayah ta 102}.

    A cikin wannan ayah Allah Ya ba mu kissar Haruta da Maruta,  wato wasu Mala'iku da aka saukar da su suna koya wa mutane tsafi.  Shafin Tarbiyyah Islamiyyah ya kawo cikakkiyar wannan kissa.  Mai bukata sai yay min magana in tura masa ta whatsApp ko ka shiga wannan shudin rubutun don karantawa. 
https://plus.google.com/103289796355839003804/posts/US6kpvGST5B

   Sannan Ya yi maganar masu koyar sihirin da suke raba tsakanin miji da matarsa.  Shi ma mun yi bayani akan wannan sihiri da yadda mutum zai gane an yi masa da kuma hanyoyin warware shi.  Shi ma mai bukata za mu tura masa ta whatsApp. 

   Sannan Allah Ya yi bayanin cewa duk wanda ya sayi tsafi,  ma'ana ya koya kuma gake aikatwa,  to ba shi da rabo a lahira.  Shi ma mun h
yi cikakken bayani a cikin posting da mukay mai taken Siffofin Bokaye.  Za ku iya karantawa acikin wannan shudin rubutun.
https://plus.google.com/103289796355839003804/posts/KpKhCReHgi5
  
  
Daga shafin Bashir Halilu. 
 Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts