ASIRIN MALLAKA WATO ASSIHRUL MAHABBAH. Sihirin da ake yi domin a mallaki soyayyar mutum, a mallaki zuciyarsa kuma a dinga juya shi yadda ake so. Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.
Sihirin Mallaka ko Sihirin hada Soyayya, a Larabce ana kiransa da Sihrul Mahabbah السحر المحبة ko a ce Sihrut Tiwalah السحر التولة. Wannan nau'in Sihiri, ana yinsa ne don wani mutum ya mallaki zuciyar wani mutum, ta yadda zai dinga sa shi ya aikata masa duk abinda yake so. Wannan nau'in Sihiri sananne ne kuma shahararre wanda ya yadu a tsakanin mutane. Mafi yawa Sihrul Mahabbah ana yin sa ne ta hanyar Sihrul Ma'akuwli wanda mukay bayaninsa jiya, wato sihrin da ake baiwa mutum abu ya ci ko ya sha ko ya shaki kamshimsa, da dai sauran hanyoyi. HANYOYIN DA BOKAYE SUKE BI DOMIN YIN SIHRUL MAHABBAH. 1- Idan mace tana so ta mallake zuciyar mijinta, ta dinga juyashi yadda take so. Bokan zai iya cewa ta kawo jinin hailarta, ya rubuta ayoyin Alqur'ani da shi. Sai ya wanke ya bata ta zubawa mijinta a abinci. Ko kuma ya bata Rubutun Qur'ani ya ce ta wanke gabanta da shi, indai mijinta ya sadu da ita to Sihirin ya kama shi. Da dai mak...