FALALAR YIN SADAKA DA MATSAYIN MASU YIN SADAKA RANAR ALƘIYAMA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
FALALAR SADAKA DA MATSAYIN MASU YIN SADAKA RANAR ALƘIYAMA.
Masu yin sadaka suna da darajoji da lada mai yawa a wajen Allah Maɗaukakin Sarki, kamar yadda waɗannan hadisai su ka tabbatar.
1- Allah Yana kare mai yin sadaka daga shiga bala'i ta dalilin sadakarsa. Manzon Allah (SAW) ya ce:
“باكروا بالصدقة فإن البلاء لا يتخطّى الصدقة”
Baihaƙiy ne ya ruwaito shi.
2- Sadaka dalili ce ta samun albarka acikin dukiya, domin sadaka ba ta rage yawan dukiya. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce:
«ما نقصت صدقة من مال»
Muslim ne ya ruwaito shi.
3- Sadaka dalili ce wajen samun nutsuwar zuciya da walwalar ruhi da jin daɗi. Daga Aba Hurairata (RA), Manzon Allah (SAW) ya ce:
(مَثَلُ الْبَخِيلِ وَالْمُنْفِقِ؛ كَمَثَلِ رَجُلَيْنِ عَلَيْهِمَا جُبَّتَانِ مِنْ حَدِيدٍ مِنْ ثُدِيِّهِمَا إِلَى تَرَاقِيهِمَا، فَأَمَّا الْمُنْفِقُ فَلا يُنْفِقُ إِلا سَبَغَتْ أَوْ وَفَرَتْ عَلَى جِلْدِهِ حَتَّى تُخْفِيَ بَنَانَهُ وَتَعْفُوَ أَثَرَهُ، وَأَمَّا الْبَخِيلُ فلا يُرِيدُ أَنْ يُنْفِقَ شَيْئًا إِلا لَزِقَتْ كُلُّ حَلْقَةٍ مَكَانَهَا فَهُوَ يُوَسِّعُهَا ولا تَتَّسِعُ)
Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.
4- Sadaka tana tsarkake dukiya da tsaftace ta daga rantsuwar da ake yi akan kasuwanci da rafkana daga ibada da akayi don neman dukiya. In mutum yai sadaka sai ta tsarkake masa dukiyarsa. Manzon Allah (SAW) ya ce:
«يا معشر التجار، إنَّ هذا البيع يحضره اللغو والحلف فشوبوه بالصدقة»
Abu Dawuda da Tirmizi da Nasa'iy da Ibn Majah duk sun riwaito shi.
5- Sadaka na magance cututtukan zuciya da bushewar zuciyar wajen kasa aikin alkhairi da ayyukan biyayya ga Allah. Manzon Allah (SAW) ya umarci wani mutum mai fama da bushewar zuciya cewa ya dinga yin sadaka da tausayawa marayu.
فقد نصح نبينا الكريم شخصاً شكى له قسوة قلبه، فقال عليه الصلام والسلام: «إذا إردت تليين قلبك فأطعم المسكين، وامسح على رأس اليتيم»
Imam Ahmad ne ya ruwaito shi.
6- Allah Yana yayewa mai yin sadaka tsoro ko abinda ke ba shi tsoro. Kamar yadda ya zo a cikin Hadisin Manzon Allah (SAW) :
جاء في الصحيحين أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال عن كسوف الشمس: “فإذا رأيتم ذلك فادعوا الله وكبروا وصلوا وتصدقوا. قال ابن دقيق العيد في شرحه: وفي الحديث دليل على استحباب ذلك عند المخاوف لاستدفاع البلاء المحذور.
Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.
7- Sadaka na sa mutum ya samu matsayin mai biyayya a wajen Allah Maɗaukakin Sarki. Allah Ta'ala Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
{لَن تَنَالُواْ الْبِرَّ حَتَّى تُنفِقُواْ مِمَّا تُحِبُّونَ}
Ayah ta 92, suratu Ali Imran.
8- Mai yin sadaka yana samun addu'ar Mala'iku, suna roƙon Allah Ya sanyawa dukiyarsa albarka kuma Ya mayar masa da mafi alkhairin abinda ya bayar, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya faɗa:
: «ما من يوم يصبح العباد فيه إلا ملكان ينزلان فيقول أحدهما: اللهم أعط منفقًا خلفاً، ويقول الآخر: اللهم أعط ممسكًا تلفًا»
Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.
9- Mai sadaka shi ne wanda dukiyarsa ta fi ta kowa albarka, saboda abinda ya bayar sadaka shi ne ya tabbata a matsayin na sa. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya gayawa Nana A'isha (RA) :
سأل النبي صلى الله عليه وسلم يوماً عائشة رضي الله عنها عن الشاة التي ذبحوها ما بقى منها: قالت: ما بقى منها إلاّ كتفها. قال: «بقي كلها غير كتفها»
Muslim ne ya ruwaito shi.
10- Sadaka tana cinye ayyukan saɓo da mutum ya yi, kamar yadda ruwa ya ke kashe wuta. Manzon Allah (SAW) ya ce :
«والصدقة تطفىء الخطيئة كما تطفىء الماء النار»
Sahihut targiyb
11- Komai ƙanƙantar sadaka tana iya hana mutum shiga wuta ranar alƙiyama. Mazon Allah (SAW) ya ce:
«فاتقوا النّار، ولو بشق تمرة».
12-Mai yin sadaka ranar Alƙiyama sadakarsa za ta zo ta yi masa inuwa. Wannan yana cikin mutane bakwai waɗanda Manzon Allah (SAW) ya ce suna cikin inuwar ayyukansu ranar alƙiyama:
«رجل تصدق بصدقة فأخفاها، حتى لا تعلم شماله ما تنفق يمينه»
Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.
Haka a wannan hadisi mai zuwa, Manzon Allah (SAW) ya ce "Kowane mutum yana ƙarƙashin inuwar sadakarsa ranar Alƙiyama har a gama yi wa mutane hisabi"
وجاء في حديث عقبة بن عامر رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «كل أمرئ في ظل صدقته، حتى يقضى بين الناس».
13- Za a kira masu sadaka ranar Alƙiyama su shiga Aljannah ta ƙofa ta musamman da aka ware musu. Acikin wannan hadisi Manzon Allah (SAW) ya ce:
«من أنفق زوجين في سبيل الله، نودي في الجنة يا عبد الله، هذا خير: فمن كان من أهل الصلاة دُعي من باب الصلاة، ومن كان من أهل الجهاد دُعي من باب الجهاد، ومن كان من أهل الصدقة دُعي من باب الصدقة، ومن كان من أهل الصيام دُعي من باب الريان»
Bukhari ne ya ruwaito wannan hadisi.
Ya Allah Ka sanya mu cikin masu sadaka kuma Allah Ka karɓa daga garemu.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment