Posts

Showing posts with the label sha'awa

ASIRIN KASHE AURE KO HANA MA'AURATA ZAMAN LAFIYA. WATO SIHRU TA‘AƊIYĪLIZ-ZAWĀJ (سِحْرُ تَعْطِيلِ الزَّوَاجِ) Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846.

Image
        A cikin Alkur'ani mai girma, suratul Baƙarah, ayah ta 102, Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi bayani akan sihiri da ake yi domin raba ma'aurata. Duk mai buƙata zai iya duba wannan ayah da fassararta da bayaninta domin samun ilimi akai. Na sha kafa hujja da ita wajen kawo bayanin sihiri don haka ba sai ma maimaita ta anan ba. Ayar da ta fara da 'Wattaba'uw'.   MA’ANAR SIHRU TA'AƊIYLIZ ZAWAJ     Malam Wahid bin Abdussalam Bali a cikin littafinsa  الصارم البتار في التصدي للسحرة الأشرار ya yi bayanin sihirin raba ma’aurata, inda ya kawo maganar Hafiz Ibn Kathir cewa: «وَسَبَبُ التَّفْرِيقِ بَيْنَ الزَّوْجَيْنِ بِالسِّحْرِ: مَا يُخَيَّلُ إِلَى الرَّجُلِ أَوِ الْمَرْأَةِ مِنَ الْآخَرِ مِنْ سُوءِ مَنْظَرٍ أَوْ خُلُقٍ، أَوْ نَحْوِ ذَلِكَ مِنَ الْأَسْبَابِ الْمُقْتَضِيَةِ لِلْفُرْقَةِ».      Ma’ana: Dalilin raba ma’aurata ta hanyar sihiri shi ne a sanya wa miji ko mata tunanin ganin ɗayan a mummunar sura ko munanan ɗabi’u, ko wasu abubuwan...

ILLOLIN MASTURBATION WATO ISTIMNA'I

Image
ILLOLIN MASTURBATION WATO ISTIMNA'I Masturbation ko kuma Istimna'i, wato wasa da tsiraici don biyawa kai bukatar jima'i. Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah,  masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846. Masturbation ko kuma Istimna'i a larabce, wata hanya ce da mutum kan bi don biyawa kansa bukatar sha'awa irinta aure. Wasu sukan yi amfani da hannunsu ko wasu sassa na jikinsu, wasu kuma sukan yi amfani da injina ko sauran abubuwa da aka kera musamman don ay wannan lalata da su. Masturbation ya zama ruwandare game duniya a tsakanin musamman matasa, wanda shi ne babban bala'in da ya ke lalata rayuwar matasa a wannan lokaci, ya 6ata rayuwar matasa da yawa maza da mata. Anan muna so ne muy bayanin illolin Masturbation da kuma hukuncin Mai yinsa a addinin musulunci, duk da dai wasu Malaman sun ce duk Mai Yin Istimna'i za a tashe shi ranar Alqiyama ya yi wa hannunsa ciki. Kafin in kawo illolin Masturbation, b...