Posts

Showing posts from December, 2024

TAKOBI MAI KAIFI DOMIN YAƘI DA MASIHIRTA DA BOKAYE. Fasarar Littafin Assarimul Battar.Daga shafin Bashir Halilu. (Darasi na 2).

Image
BABI NA ƊAYA.  1- Ma'anar Tsafi ko Sihiri.  a) Tsafi a harshen Larabci.     * Mallam Al-Laith ya ce: "Tsafi wani abu ne da ake yi domin neman kusantar shaiɗan tare da neman taimakonsa." * Mallam Al-Azhari ya ce: "Asalin tsafi shine karkatar da abu daga gaskiyarsa zuwa wani abu daban."    *  Ibn Mandhur ya ce: "Mai tsafi yana nuna ƙarya a matsayin gaskiya kuma yana karkatar da abu daga asalin gaskiyarsa, ya juyar da shi."    * Shamar ya ruwaito daga Ibn Aisha ya ce: "Larabawa sun kira tsafi ne da sunan 'sihr' saboda yana mayar da lafiya zuwa rashin lafiya."   * Ibn Faris ya ce: "Wasu Malaman sun ce tsafi yana nufin nuna ƙarya a matsayin gaskiya."    * A cikin Littafin Al-Mu’jamul-Waseet, aka ce, tsafi yana nufin: "Wani abu mai ɓoyayye wanda aka yi shi ga hanyar hikima."   * A cikin Littafin Muheetil-Muheet kuma aka ce, tsafi yana nufin: "Nuna abu a cikin mafi kyau ga mutane domin su ruɗu ko a ɓatar da hankalins...

TAKOBI MAI KAIFI DON YAƘI DA MUGWAYEN MASIHIRTA, BOKAYE. Darasi na ɗaya (1).

Image
Gabatarwar mai fassara. Ni Bashir Halilu ina gabatar muku da wannan littafi wanda na yi alƙawarin da yaddar Allah zan dinga kawo muku fassarar sa a shafina na tiktok da kuma facebook. Littafin yana magana ne akan sihiri. Marubucin ya bayyana ma’anar sihiri, ya kuma kawo hujjoji daga Alƙur’ani mai girma da Hadisai kan gaskiyar samuwar sihiri tare da maganganun malamai game da yadda sihiri ya ke. Ya bayyana rabe-raben sihiri a fahimtar Malamai da dama, kamar Fakhruddin Al-Razi da Al-Raghib, sannan ya bayyana hanyoyin da masu sihiri ke bi don kiran Aljannu da yadda ake mallakar Aljanu da saka su ayyuka. Har ila yau, ya bayyana hukuncin sihiri a cikin shari’ar Musulunci da hukuncin Masihirta, Bokaye. Marubucin wannan littafi "As-Sarimul -Battar Fit -Tasaddi Lis-Saharatil -Ashrar": shi ne Wahid bin Abdussalam Bali, wanda aka haifa a Masar. Ya rubuta littattafai da dama kamar Fakihatul-Majalis, Bidayatul-Muttafiqah, Arba'in Khata'an Lil-Lisan, Sahihul-Adabul -Is...

ZA MU FARA DARASI KYAUTA DOMIN FASSARA LITTAFIN ASSARIMUL BATTAR FITTASADDI LISSAHARATIL ASHRAR, TA BIDIYO DA KUMA RUBUTU.

Image
Mutane da dama suna tambayata akan in buɗe musu aji na musamman akan 'Yadda ake haɗa magunguna da kuma wasu abubuwa da ke da alaƙa da Aljanu da warware sihiri. Insha Allahu zan fara kawo muku karatun littafin 'Assarimul Battar', wanda littafi ne sananne da aka wallafashi akan Matsalolin Aljanu da warware sihiri, a bisa tsari mai kyau na Ahlus sunnah wal jama'a.    Zan dinga kawo muku karatun littafin Insha Allahu ta hanyar bidiyo a shafina na tiktok mai suna "Shafin Bashir Halilu" sai kuma in rubuta tarjamarsa a wannan shafin nawa na facebook mai suna "Bashir Halilu". Ga kaɗan daga abubuwanda littafin ya ƙunsa. ١-تَصْحِيحُ الْعَقِيدَةِ فِيماَ يختَصُّ بِجَانِبِ السِّحْرِ وَالشَّيَاطِينِ . 1. Kyautata akidar Musulmi game da abinda ya ke da alaka da sihiri da aljannu: ٢-الاِ عْتِماَدُ عَلىَٰ الدَّلِيلِ فيِ مَسَائلِ عِلاجِ السِّحْرِ . 2- Dogaro da Alƙur'ani da Hadisi wajen warware mas'alolin sihiri.  ٣-كَيْفَ يَقِي الْـمُسْلِمُ نَفْسَهُ وَأَوْلاَ...