WALIYYAI DAGA JINSIN ALJANU. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

WALIYYAI DAGA JINSIN AL-JANU. 

  Acikin Aljanu akwai mutanen kirki,  Waliyyai,  Bayin Allah na gari kuma masoya Allah da ManzonSa kuma masu ƙoƙari wajen addini da zamantakewa mai kyau. 

   Kamar yadda mu ka san Addinin Musulunci wajen adalci,  duk irin yadda wasu jama'a suke wajen aikata 6arna da fajirci,  to indai suna da wani dan alkhairi ko yaya ne sai Allah Ya fade shi,  koda kuwa sharrinsu ya fi yawa. Hatta giya da caca,  sai da Allah Madaukakin sarki ya ce 'Acikinsu akwai cutarwa babba da kuma wani dan amfani kadan ga mutane'. Wato duk da su ba mutane ba ne kuma ba su da baki amma hakan ba ta sa saboda kyamar da Allah Yake yi mu su ya ki fadin cewa suna da amfani kadan ba. 

   Ka dubi sharri irin na Yahudawa da yadda suke kashe Annabawan Allah,  da yiwa Allah Ta'ala izgili da taurin kai amma duk da haka sai da Allah Ya ce 'Acikin Ahlil kitabi akwai jama'ar da suke tsayayyu, suna karanta ayoyin Allah dare da rana kuma sunaywa Allah sujjada'. Sannan Allah Ya ce 'Acikinsu akwai Salihai acikinsu kuma akwai wadanda ba haka ba.' Haka nan Allah Mai girma da daukaka Ya gaya mana cewa 'Acikin Ahlil kitabi akwai wanda in ka ba shi amanar dukiyarka,  komai yawanta,  zai dawo maka da ita ba ha'inci, acikinsu kuma akwai wanda in ka ba shi amanar dinare daya to ba zai dawo maka da shi ba,  sai ka tsaya a kansa,  tsayin daka'. 

Duba da haka,  da kuma umarnin da Allah Madaukakin Sarki ya bayar cewa 'Kada gabar da ke tsakaninku da wasu mutane ta sa ku keta haddi akansu,  ko ku kasa fadin gaskiya akansu.. ', ya sa mu ka ga ya dace kamar yadda muke yawan fadin sharrin Aljanu to kuma mu fadi alkhairinsu,  tunda suna da shi. 

(Duk ayoyin dana kawo a sama na kawo ma'anarsu ne,  ba cikakkiyar fassararsu ba amma insha Allahu duk ayar da zan kawo a kasa zan kawo cikakken rubutunta da larafci da kuma cikakkiyar fassararta da Hausa). 

Muna yawaita fadin cewa Aljanu makaryata ne,  mayaudara kuma macuta. Wanda wannan magana ko kuskure babu,  haka ta ke. To saidai ba dukkansu ne suke haka ba,  domin kuwa duk wanda ya qudurce cewa dukkan Aljanu makaryata ne kuma mayaudara,  ko kuma ya dauka fasiqaine gaba dayansu to bai yiwa jama'ar Aljanu adalci ba,  abu mafi hadari kuma shi ne duk wanda ya qudurce haka to ya karyata ayoyin Alqur'ani mai tsarki da kuma wasu daga ingantattun Hadisan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
da su ka nuna irin yadda jama'ar Aljanu suke zuwa jin wa'azi da yadda suke aiki da shi. 

Ko ban yi dogon bayani ba,  zan takaita ne kawai in kawo hujjoji daga cikin 'Suratul Jinni', in dangantakar bayani kuma ta kama in kawo wata ayar wacce ba daga Suratul Jinninba to saidai in kawo ma'anarta. 

Idan ka nutsu,  ka karanta 'Suratul Jinni' ma'ana 'Surar Aljanu' ko Sura mai bayani akan Aljanu,  wacce ita ce sura ta saba'in da biyu (72) acikin Alqur'ani mai girma, za ka fahimci bayanin Allah Madaukakin Sarki akan cewa:-

1- Aljanu sun saurari karatun Alqur'ani daga bakin Manzon Allahصلى الله عليه وسلم, 
sauraro na nutsuwa da fahimta. 

2-Karatun Alqur'ani yana burge Aljanu. 

3- Aljanu sun yarda cewa Alqur'ani yana shiryarwa ne izuwa ga gaskiya. 

4- Aljanu sun yi imani da Alqur'ani. 

5- Aljanu sun yi alkawari cewa ba za su sake yiwa Allah shirka ba,  tun a ranar da su ka fara jin karatun Alqur'ani. 

6-Aljanu sun yarda cewa girman Ubangiji ba karami bane ba. 

7- Aljanu sun yarda cewa Allah ba shi da d`a kuma ba shi da mata. 

8- Aljanu sun ce wawaye ne acikinsu suke fadin abinda ya ketare doka game da Allah Madaukakin Sarki. Ma'ana masu hankali da ilimin cikinsu ba sa yi wa Allah karya. 

9- Aljanu suka ce sun zaci cewa mutum da Aljan ba za su iya yiwa Allah karya ba (suna ganin cewa girman Allah Ya wuce mutum ko Aljan ya iya yi maSa karya, sai ga shi ana samun wawaye suna aikata hakan). 

10- Mutane ne suka fara neman Aljanu don ayi shirka,  ta hanyar rokon Aljanun su tsare su daga sharrin wawayensu, a maimakon su nemi taimakon Allah. 

11- Ta dalilin rokon Aljanu da mutane suke yi ne ya sa Aljanu suka fara shafar mutane da rashin lafiya da ciwon hauka kuma haka ne ya sa Aljanu su ka fara yiwa mutane dagawa da girman kai. 

12- Wawayen Aljanu ne suke cewa wai Allah ba zai kuma aiko wani Manzo ba bayan Annabi Musa عليه السلام
kamar yadda ya zo a wata surar cewa sun ce 'Mun ji wani littafi da aka saukar bayan Annabi Musa'. 

13- Alqur'ani ya tabbatar da cewa acikin Aljanu akwai Salihai akwai kuma wadanda ba Salihai ba,  mabiya hanyoyi ne daban-daban. 

14- Aljanu sun yi imani da Allah da ManzonSa, a lokacin da su ka ji bayanin shiriya. 

15- Acikin Aljanu akwai Musulmai akwai kuma karkatattu. 

16-Aljanu sun yi imani cewa guraben sujjada na Allah ne,  don haka bai kamata a bautawa Allah tare da wani ba. 

17- Jama'ar Aljanu suna yiwa 'yan uwansu wa'azi,  tare da shigar da su musulunci. 

18-Aljanu sun yarda cewa duk wanda bai yiwa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
biyayya ba to ba zai tsira a lahira ba. 
19-  In mu ka hada wadannan ma'anoni,  za mu iya cewa acikin Aljanu akwai Sahabbai,  Allah Ya kara yarda a gare su. 

   Da dai darussa da yawa da surar take karantarwa akan Aljanu. 
 In ka duba ingantattun Hadisai kuwa,  za ka samu cewa hatta irin abincin da ya kamata Aljanu su ci sai da su ka tambayi Manzon Allah صلى الله عليه وسلم، 
kuma Annabi صلى الله عليه وسلم
yana ware lokaci na musamman da yake zuwa yana yiwa Aljanu wa'azi. 
 Don haka ba daidai bane mu dauka cewa dukkan Aljanu 6atattu ne ko fasiqai,  lallai jama'ar Aljanu sun kasance kamar jama'ar mutane ce, akwai musulmai,  akwai arna,  akawai wawaye da jahilai akwai malamai da masu hankali,  akwai azzalumai, akwai kuma ma'abota karamci da adalci da son zaman lafiya, sannan akwai 6arayi akwqi kuma `yan kasuwa. 

Amma fa wannan bayani ba wai yana nufim cewa mutum ya saki jiki da wani Aljani bane da sunan wai shi Rauhani ne ko kuma Khadimi,  a'a,  na kawo bayanin ne saboda abu ne da ya shafi aqida, don kowane Musulmi ya zama yana da aqida mai kyau akan Aljanu ba gur6atacciya ba. 

Suratul Jinni ba iya wadannan darussan kawai take karantarwa ba,  a'a,  tana karantar da darussa da yawa,  don haka, ga cikakkiyar surar zan kawo muku da fassarar Hausa,  daga littafin Sheikh Mahmud Gummi,  RahimahUllah. Gabadaya fassarar da zan kawo daga littafin Mallam ta ke,  ba karin bayani na. 
بسم الله الرحمن الرحيم

قُلْ أُوحِيَ إِلَيَّ أَنَّهُ اسْتَمَعَ نَفَرٌ مِّنَ الْجِنِّ فَقَالُوا إِنَّا سَمِعْنَا قُرْآنًا عَجَبًا ( 1 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 1
Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki."

يَهْدِي إِلَى الرُّشْدِ فَآمَنَّا بِهِ ۖ وَلَن نُّشْرِكَ بِرَبِّنَا أَحَدًا ( 2 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 2
"Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba."

وَأَنَّهُ تَعَالَىٰ جَدُّ رَبِّنَا مَا اتَّخَذَ صَاحِبَةً وَلَا وَلَدًا ( 3 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 3
"Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba."

وَأَنَّهُ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى اللَّهِ شَطَطًا ( 4 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 4
"Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah."

وَأَنَّا ظَنَنَّا أَن لَّن تَقُولَ الْإِنسُ وَالْجِنُّ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا ( 5 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 5
"Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah."

وَأَنَّهُ كَانَ رِجَالٌ مِّنَ الْإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٍ مِّنَ الْجِنِّ فَزَادُوهُمْ رَهَقًا ( 6 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 6
"Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai."

وَأَنَّهُمْ ظَنُّوا كَمَا ظَنَنتُمْ أَن لَّن يَبْعَثَ اللَّهُ أَحَدًا ( 7 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 7
"Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba."

وَأَنَّا لَمَسْنَا السَّمَاءَ فَوَجَدْنَاهَا مُلِئَتْ حَرَسًا شَدِيدًا وَشُهُبًا ( 8 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 8
"Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye."

وَأَنَّا كُنَّا نَقْعُدُ مِنْهَا مَقَاعِدَ لِلسَّمْعِ ۖ فَمَن يَسْتَمِعِ الْآنَ يَجِدْ لَهُ شِهَابًا رَّصَدًا ( 9 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 9
"Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa."

وَأَنَّا لَا نَدْرِي أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَن فِي الْأَرْضِ أَمْ أَرَادَ بِهِمْ رَبُّهُمْ رَشَدًا ( 10 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 10
"Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?"

وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَٰلِكَ ۖ كُنَّا طَرَائِقَ قِدَدًا ( 11 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 11
"Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam."

وَأَنَّا ظَنَنَّا أَن لَّن نُّعْجِزَ اللَّهَ فِي الْأَرْضِ وَلَن نُّعْجِزَهُ هَرَبًا ( 12 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 12
"Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba."

وَأَنَّا لَمَّا سَمِعْنَا الْهُدَىٰ آمَنَّا بِهِ ۖ فَمَن يُؤْمِن بِرَبِّهِ فَلَا يَخَافُ بَخْسًا وَلَا رَهَقًا ( 13 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 13
"Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba."

وَأَنَّا مِنَّا الْمُسْلِمُونَ وَمِنَّا الْقَاسِطُونَ ۖ فَمَنْ أَسْلَمَ فَأُولَٰئِكَ تَحَرَّوْا رَشَدًا ( 14 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 14
"Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."

وَأَمَّا الْقَاسِطُونَ فَكَانُوا لِجَهَنَّمَ حَطَبًا ( 15 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 15
"Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama."

وَأَن لَّوِ اسْتَقَامُوا عَلَى الطَّرِيقَةِ لَأَسْقَيْنَاهُم مَّاءً غَدَقًا ( 16 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 16
"Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa."

لِّنَفْتِنَهُمْ فِيهِ ۚ وَمَن يُعْرِضْ عَن ذِكْرِ رَبِّهِ يَسْلُكْهُ عَذَابًا صَعَدًا ( 17 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 17
"Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."

وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا ( 18 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 18
"Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)."

وَأَنَّهُ لَمَّا قَامَ عَبْدُ اللَّهِ يَدْعُوهُ كَادُوا يَكُونُونَ عَلَيْهِ لِبَدًا ( 19 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 19
"Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa."

قُلْ إِنَّمَا أَدْعُو رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِهِ أَحَدًا ( 20 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 20
Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba."

قُلْ إِنِّي لَا أَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا رَشَدًا ( 21 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 21
Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri."

قُلْ إِنِّي لَن يُجِيرَنِي مِنَ اللَّهِ أَحَدٌ وَلَنْ أَجِدَ مِن دُونِهِ مُلْتَحَدًا ( 22 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 22
Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi."

إِلَّا بَلَاغًا مِّنَ اللَّهِ وَرِسَالَاتِهِ ۚ وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَإِنَّ لَهُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ( 23 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 23
"Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada."

حَتَّىٰ إِذَا رَأَوْا مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ أَضْعَفُ نَاصِرًا وَأَقَلُّ عَدَدًا ( 24 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 24
Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.

قُلْ إِنْ أَدْرِي أَقَرِيبٌ مَّا تُوعَدُونَ أَمْ يَجْعَلُ لَهُ رَبِّي أَمَدًا ( 25 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 25
Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!"

عَالِمُ الْغَيْبِ فَلَا يُظْهِرُ عَلَىٰ غَيْبِهِ أَحَدًا ( 26 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 26
"Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa."

إِلَّا مَنِ ارْتَضَىٰ مِن رَّسُولٍ فَإِنَّهُ يَسْلُكُ مِن بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ رَصَدًا ( 27 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 27
"Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."

لِّيَعْلَمَ أَن قَدْ أَبْلَغُوا رِسَالَاتِ رَبِّهِمْ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيْهِمْ وَأَحْصَىٰ كُلَّ شَيْءٍ عَدَدًا ( 28 ) Al-Jinn ( The Jinn ) - Aya 28
"Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."

Daga cibiyar Sunnah Medicine,  masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci.

Shi ga cikin wannan shudin rubutun kayi downloading Application dinmu,  wanda za ka dinga samun rubututtukanmu cikin sauki
https://appsgeyser.io/7550770/Bashir%20Halilu%20Tarbiyyah%20Islamiyyah

Shiga shafinmu na facebook acikin wannan shudin 
rubutun,  sai ka danna like 
http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/

  Daga shafin Bashir Halilu. 
Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts