YADDA AKE YIN MAN HABBATUS SAUDA DA KUMA AMFANIN HABBATUS SAUDA WAJEN KYAUTATA LAFIYA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
YADDA AKE YIN MAN HABBATUS SAUDA DA KUMA AMFANIN HABBATUS SAUDA WAJEN KYAUTATA LAFIYA.
Da fari, a samu Ƴaƴan Habbatus sauda (da Hausa ana kiran Habbatus sauda Baƙin Algaru), sai a auna adadin da ake bukata wanda za a yi man da shi, sai a gyara ta sosai, a tsince, a cire datti.
Daga nan sai a daka su sosai ko a niƙa, ta zama gari, yin hakan na taimakawa wajen sauƙin fitar da man.
Sai a samu man da za a haɗa da shi kamar man Zaitun ko Man gyaɗa ko man Auduga ko man Kwakwa kodai wani mai me tsafta da ake da shi, sai a zuba akan wannan garin Habbatus saudar. A zuba cikin kwalba ko wani mazubi kamar jarka, a kulle shi da kyau.
A ajjiye wannan kwalbar ko jarkar acikin rana ko waje mai zafi tsawon kamar sati uku. Kullum a dinga ɗauko wannan man ana girgizawa, yana haɗuwa sosai. A hankali dukkan wasu sinadarai masu amfani za su dinga fita daga jikin garin Habbatus saudar suna komawa cikin man.
Bayan kamar sati uku sai a samu yanki ko rariya a tace wannan man sannan a zuba shi acikin kwalba mai duhu.
Ana ajjiye man Habbatus sauda ne a wajen da babu hasken rana kuma cikin kwalba mai duhu. Man Habbatus saudan da aka adana shi yadda ya kamata yana yin shekara ɗaya bai lalace ba, ba tare da an saka masa chemical ba.
Wasu daga Amfanin Man Habbatus sauda
1-CIWON KUNNE.
A ɗiga Man Habbatussauda ɗigo 1, zuwa 2 yana Maganin Ciwon Kunne.
2-BAQIN ISKA.
Yin Hayaqi da 'Ya'yan Habbatussauda Ko Garin Ta Yana Raba Mutum da Shaidanun Aljanu
3-RASHIN BACCI
Azuba Man Habbatussauda cokaci 1 A Ruwan Dumi Asha Kafin a Kwanta da Awa 1 Zaayi Bacci Ciki Nutsuwa da Jin dadi
4-CIWON ZUCIYA
Asami Nonon Akuya Kofi Daya Azuba Man Habbatussauda 4ml Ciki a Sha Sau 2 A rana Tsawon Mako 1 Zaa Sami Lafiya, insha Allahu
5-CUTUTTUKAN IDO
Shan Man Habbatussauda Cokali1a Cikin Ruwan Markadadden Karas A Rana Yana Magance Cututtukan ido
6-MATSALOLIN AL'ADA
A Niqa Garin Yayan Habbatussauda a Hada da Zuma Baqa, a Sha Cokali 1 da Safe 1 da yamma Na Kwana 7 Zaa Rabu da Matsalar Alada
7-CIWON QODA
Asami Garin Habbatussauda Gram 300
A Sami Zuma 600ml Mai kyau , A Hade su su da Kyau, A Riqa Shan cokali 1 Rana Har Ya Qare zaa Rabu da Ciwon ƙoda
8-KUMBURI
Man Habbatussauda na Sa6e Kumburi A Jikin Mutum Idan Aka Shafa a Inda Ya kumburan
9-FARFADIYA
Yin surace da Garin Habbatussauda Ko Yayan ta Na Dan Lokaci Yana Maganin Farfadiya
10-CIWON HAQORI
A Sa man Habbatussauda a Haqorin dake Ciwon Zaa Sami sauqi
11-HAWAN JINI
Shan Shayin Garin Habbatussauda Yana Saukar da Hawan Jina SoSai
12-CUTUTTUKAN FATA
Asami Garin Habbatussauda da man Habbatussauda, A Hade su Ana shade jiki
Zaa Rabu da Duk Wata Matsalar Fata
13-HIV/Aids AIDS
Mai Shan Shayin Yayan Habba da Zuma Cutar Qanjamau Baza ta Ta6a Yin Tasiri a Jikin sa ba
14-CIWON HANTA
Sa Garin Habbatussauda A Cikin Abinci Lokacin da Zaaci, Yana Maganin Ko Wanne Nau'in Ciwon Hanta
15-CIWON SIGA
Shan Shayin Yayan Habbatussauda Yana Saukar da Sukarin jikin Mutum Komai Yawan Shi Amma baa sa Sukari A ciki
16-SHANYEWAR BARIN JIKI ( PARALYSIS)
A Riqa Sa man Habbatussauda 3 ml Cikin Nonon Raqumi Kofi 1 Wato 30 ml A Rana Ayi Hakan Kullun Zuwa Wani Dan Lokaci zaa warke insha Allah.
Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment