YADDA ZA KA GANE AN YI HACKING ƊIN WAYARKA. Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
YADDA ZA KA GANE WANI YANA ƘOƘARIN HACKING ƊIN WAYARKA.
A taƙaice, ana iya yin hacking ɗin wayar mutum kamar yadda ake hacking ɗin facebook, ya zamanto wani yana amfani da wayarsa yana ganin komai na cikin wayarka kuma yana iya buɗe kowane Application a wayarka sannan zai iya yin kira ko aika saƙonni da lambar wayarka, zai ma iya cire kuɗi daga account ɗinka na banki. Ana ma iya hacking ɗin kyamarar wayarka, ta yadda duk abinda kake tana ɗauka, wani yana kallonka.
Daga shekaranjiya zuwa yau wasu ɓata_gari sunata bibiyata, suna ƙoƙaring hacking ɗin wayata amma Allah bai ba su nasara ba, shi ya sa zan bayyana muku yadda za ku gane wani yana ƙoƙarin hacking ɗin wayarku domin ku ɗauki mataki.
1. Saurin zuƙewar batir.
Idan ka ga haka kawai wayarka na saurin zuƙe caji ba yadda ta saba ba, to mai yiwuwa hakan na faruwa ne saboda wani daga nesa yana buɗe maka wasu application 'running at the background' ta yadda ba ka gani, don haka aiki yaiwa wayar yawa, ta ke zuƙe caji.
2. Shan DATA.
Idan ka ga da zarar ka sayi DATA sai ta ƙare ba tare da ka yi cikakken amfani da ita ba to mai yiwuwa wani yana amfani da DATArka wajen leƙen asiri a wayarka.
3. Rikicewar waya.
Haka kawai ka ga idan ka danna wani waje a 'screen' ɗin wayarka sai wani wajen daban ya buɗe inda ba nan ka danna ba, ko kuma ka da idan ka danna wani waje sai ya ƙi buɗewa, sai bayan kusan rabin minti ko ma minti ɗaya sai ya buɗe.
4. Daukar zafin waya.
Lokaci ɗaya wayarka ta dinga mugun zafi wanda ba ta taɓa yi ba, to da alama ku biyu kuke amfani da ita, ɗayan yana daga nesa yana buɗe ma aiki.
5. Sababbin applications.
Idan ka dinga ganin wasu applications a wayarka waɗanda ba kai ne ka saka su ba, to da alama wani ya tura ma ka wani application wanda ya ke amfani da shi yana kai ma ka hari.
6. Budewar applications da kansu.
Haka kawai sai ka ga wayarka tana shiga wasu applications tana buɗe su da kanta ko kuma browser dinka in ka duba history sai ka ga an shiga wasu gurare inda ba kai ne ka shiga ba. To da alama akwai mai amfani da ta sa wayar yana buɗe ma ka ta ka.
7. Notification barkatai daga wasu applications ɗin.
Idan ka ga lokaci guda application da yawa suna ta turo ma ka notification to ka tsaya ka karanta, domin wasu application ɗin suna sanar da mutum idan ana ƙoƙarin yi masa hacking amma idan bai ɗau mataki ba sai su bayar da dama.
8. Tsintar hotuna da bidiyoyi acikin wayarka.
Idan kana yawan ganin hotuna ko bidiyo a wayarka waɗanda ka rasa yadda aka yi su ka shigo to da alama wani ya yi hacking ɗin wayarka. Kuma alama ce ta camera compromising, wato tare kuke amfani da kyamarar wayarka da wani.
9- Gardamar application akan aikin da ya saba yi.
Wato misali idan aka kiraka a waya, in ka danna handsfree sai ya ƙi dannuwa ko kuma sound ya ƙi yi idan ka kunna video.
10- Mutuwar waya da kuma kunna kanta.
Idan mutum yai hacking ɗin wayarka to zai iya kunnata ko kuma ya kasheta koda kana cikin amfani da ita.
11- Idan wani application yana ba ka matsala ko da ka yi updating ɗin sa sai ya cigaba.
12- Shigowar wasu links cikin wayarka.
Wani sa'in idan za a yi hacking ɗin wayarka za ka dinga ganin ana turo ma wasu links marasa ma'ana. Ana iya tura ma ka ta whatsApp ko facebook ko kuma message kai tsaye. Da zarar ka danna wannan link ɗin ko kuma ka shiga domin ka ga abinda ke ciki to shikenan an yi hacking ɗin wayarka.
Don haka koda yaushe ka dinga bincike kana kulawa da waɗannan abubuwa a wayarka.
Saboda ta haka na gano mai ƙoƙarin yi min hacking kuma na gano lambar wayarsa da address ɗinsa da hotunansa.
A rubutu na gaba zan kawo muku matakin da ya kamata ku ɗauka idan kun fahimci ana ƙoƙarin yi muku hacking.
Daga shafin Bashir Halilu.
Comments
Post a Comment