YADDA AKE GANE ASIRIN RUFA'IDO Daga shafin Bashir Halilu. Lambar waya 08162600700

YADDA AKE ASIRIN RUFA-IDO

 Assihrut takhayyal

    Shi wannan sihiri yadda          yake shi ne, mutum ya dinga ganin wani abu a idonsa amma a zahiri babu wannan abun. Misali, mutum ya dinga ganin kare ko maciji yana binsa amma kuma a hakika babu abinda yake binsa. Har zaka ga mutum yana ihu, yana cewa ga su nan za su kama ni amma kuma mutane basa ganin komai sannan kuma ba abinda zai kama shi, saidai shi yana ganin abun da idonsa.

Hakanan ya kan zamarwa 
mutum zai ga kamar ya aikata wani abu amma kuma bai aikata ba.

 Misali, mutum zai gan shi ya tafi makaranta, ya yi karatu, ya dawo gida amma a hakika ba inda ya je, yana waje daya a zaune ne kawai kuma ba mafarki yake ba.

Shi *Sihrut takhayyal* shi ne mutum ya ga wani abu ko yaga ya aikata wani abu a zahiri ba a mafarki ba amma kuma ahakika bai aikata ba. 

    Misali, mutum zai ce ya baka ajjiyar kudi amma kuma bai baka ba, alhali shi yasan ya baka a gaban shaidu, har an rubuta takarda, kuma ba mafarki yay ba a zahiri ya gani. Saidai a hakikanin gaskiya abun bai faru ba.

*Sihirin rufa ido* ko *Assihrut takhayyal*, tsohuwar sana'ar bokaye ce kuma yana cikin mugwayen asirai da ake yi domin saka dan-Adam acikin dimuwa ko a haukata shi, ana kuma yinsa don a damfari mutane, musamman a wanna lokaci.

Zaka gane cewa tsohon tsafi ne idan ka fahimci cewa irin wannan asiri ne matsafan Fir'auna sukay wa Annabi Musa Alaihis salam, wanda Allah Ta'ala ya ce shi kansa Annabi Musa Alaihis salam sai da ya ji tsoro lokacin da ya ga na'ukan tsafin na su.
Haka nan wannan nau'in asiri shi ne wani Bayahude yay wa Annabi Muhammad SallAllahu alaihi wa sallam, wanda Nana Ai'sha ta ce har saida ta kai Annabi sallAllahu alaihi wa sallam yana ganin ya aikata kaza, alhali bai aikata ba.

Allah Madaukakin Sarki Yana fada a Alqur'ani cewa

ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﻓﻰ ﺳﻮﺭﺓ ﻃﻪ – ﺍﻵﻳﺔ 65 ، 66
بسم الله الرحمن الرحيم
‏( ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻳَﺎﻣُﻮﺳَﻰ ﺇِﻣَّﺎ ﺃَﻥْ ﺗُﻠْﻘِﻰَ ﻭَﺇِﻣَّﺎ ﺃَﻥْ ﻧَﻜُﻮﻥَ ﺃَﻭَّﻝَ ﻣَﻦْ ﺃَﻟْﻘَﻰ * ﻗَﺎﻝَ ﺑَﻞْ ﺃَﻟْﻘُﻮﺍ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﺣِﺒَﺎﻟُﻬُﻢْ ﻭَﻋِﺼِﻴُّﻬُﻢْ ﻳُﺨَﻴَّﻞُ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻣِﻦْ ﺳِﺤْﺮِﻫِﻢْ ﺃَﻧَّﻬَﺎ ﺗَﺴْﻌَﻰ )

*Ma'ana:*

    _"Sai (matsafan) su ka ce Ya kai Musa! ko ka fara jefawa ko kuma mu mu fara jefawa. Sai yace a'a, ku jefa, sai ga shi igiyoyinsu da sandunansu sunay masa gizo kamar motsi suke yi"_.

Wannan aya tana bamu labarin cewa lokacin da matsafan Fir'auna suka zo da sanduna da igiyoyi, suka jefar da su a tsakiyar fili, sai Annabi Musa alaihis salam da sauran mutanen da ke wajen suka ga macizai suna motsi, suna tafiya. Alhali ba macizan bane, kawai an yi musu rufa ido ne.

Tabbas ba maciji ko daya a wajen, kawai an yi musu asirin rufa ido ne sai suka dinga ganin macizai, saboda haka Annabi Musa alaihis salam ya ji tsoron kada mutane su dauka gaske ne; amma ba wai macizan yake jin toro ba.

Zaka gane cewa ba macizai bane, saboda lokacin da maciyar Annabi Musa alaihis salam ta hadiye su bata kara girma ba kuma ba a ga alamun wani abu acikinta ba, saboda dama idonsu ne kawai yake ganin macizan amma ba komai a wajen.

*Sai mai shafin Sunnah Medicine ya ce*
Har yanzu akwai masu yin wannan sihirin, su tara mutane su ce za suy musu kudi, sai kaga an buga kudin, har a baka ka rike a hannunka amma a gaske ba komai a hannunka, idan asirin ya sakeka zaka daina ganinsu.

Ko kuma Aljanu su cewa wani Shehi za su kai shi Makkah ko wani waje mai tsarki yay sallah, sai yaga an dauke shi, ya je, yay sallah, har ya gaggaisa da wasu mutane da ya sani sun tafi umara sannan a dauke shi, a dawo da shi gida, alhali yana zaune ne a daki ba inda suka kai shi, kawai sun yi masa rufa-ido ne.

Shi yasa duk wanda yace wai Rauhanay ko Aljanu suna kai shi Ka'aba ko wani waje yay sallah, alhali ga shi a daki a zaune, to wAllahi karya yake, kawai sunay masa sihiri ne, yaga kamar hakan ta faru.

Allah Ya tsare mana imaninmu.

An samu Hadisi daga Nana Ai'sha, Allah Ya kara yarda agareta cewa Assihrut takhayyal ko sihirin rufa ido, shi ne nau'in asirin da Yahudawa sukay wa Annabi Muhammad SallAhu alaihi wa sallam, yay rashin lafiya mai tsanani, har takai yana ganin kamar ya aikata wani abu alhali bai aikata ba ko ya dinga ganin kamar ya je wajen wata acikin matansa alhali ba inda ya je.

Manzon Allah sallAllahu alaihi wa sallam ya kan zo wajen matansa, ya ce musu aikuwa na aikata abu kaza, sai su ce Ya RasulAllahi baka aikata ba kuma ahakika bai aikata ba din.
Malamai suka ce, ta fuskar wahayi ne kawai tunanin Manzon Allah sallAllahu alaihi wa sallam bai rikice ba, duk sakon da Allah Ya ba shi daidai yake isarwa.

Mai son karanta cikakkiyar wannan kissa sai ya karanta rubutuna mai taken *SHIN AN YIWA MANZON ALLAH (SAW) SIHIRI?*.

Na kawo ruwayoyin da kuma maganganun malamai akay amma ga ruwayar a larabce kamar yadda ta zo acikin Bukhariy da Muslim.

ﻭﻗﺪ ﺛﺒﺖ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻋﻦ ﺍﻟﺴﻴﺪﺓ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺑﺄﻛﺜﺮ ﻣﻦ ﺳﻨﺪ ﻭﻋﻨﻬﺎ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﺃﻧﻬﺎ ﻗﺎﻟﺖ : ‏( ﺳﺤﺮ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺯﺭﻳﻖ ﻳﻘﺎﻝ ﻟﻪ ﻟﺒﻴﺪ ﺑﻦ ﺍﻷﻋﺼﻢ ، ﺣﺘﻰ ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺨﻴﻞ ﺇﻟﻴﻪ ﺃﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﺸﻲﺀ ﻭﻣﺎ ﻓﻌﻠﻪ 0 ﺣﺘﻰ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﺫﺍﺕ ﻳﻮﻡ - ﺃﻭ ﺫﺍﺕ ﻟﻴﻠﺔ - ﻭﻫﻮ ﻋﻨﺪﻱ ، ﻟﻜﻨﻪ ﺩﻋﺎ ﻭﺩﻋﺎ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ، ﺃﺷﻌﺮﺕ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻓﺘﺎﻧﻲ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺳﺘﻔﺘﻴﺘﻪ ﻓﻴﻪ ؟ ﺃﺗﺎﻧﻲ ﺭﺟﻼﻥ ، ﻓﻘﻌﺪ ﺃﺣﺪﻫﻤﺎ ﻋﻨﺪ ﺭﺃﺳﻲ ، ﻭﺍﻵﺧﺮ ﻋﻨﺪ ﺭﺟﻠﻲ ، ﻓﻘﺎﻝ ﺃﺣﺪﻫﻤﺎ ﻟﺼﺎﺣﺒﻪ : ﻣﺎ ﻭﺟﻊ ﺍﻟﺮﺟﻞ ؟ ﻗﺎﻝ : ﻣﻄﺒﻮﺏ – ﺃﻱ ﻣﺴﺤﻮﺭ - ، ﻗﺎﻝ : ﻣﻦ ﻃﺒﻪ ؟ ﻗﺎﻝ : ﻟﺒﻴﺪ ﺑﻦ ﺍﻷﻋﺼﻢ ، ﻗﺎﻝ : ﻓﻲ ﺃﻱ ﺷﻲﺀ ؟ ﻗﺎﻝ : ﻓﻲ ﻣﺸﻂ ﻭﻣﺸﺎﻃﺔ ، ﻭﺟﻒ ﻃﻠﻊ ﻧﺨﻠﺔ ﺫﻛﺮ 0 ﻗﺎﻝ : ﻭﺃﻳﻦ ﻫﻮ ؟ ﻗﺎﻝ ﻓﻲ ﺑﺌﺮ ﺫﺭﻭﺍﻥ ﻓﺄﺗﺎﻫﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻧﺎﺱ ﻣﻦ ﺃﺻﺤﺎﺑﻪ 0 ﻓﺠﺎﺀ ﻓﻘﺎﻝ : ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ، ﻛﺄﻥ ﻣﺎﺀﻫﺎ ﻧﻘﺎﻋﺔ ﺍﻟﺤﻨﺎﺀ ، ﻭﻛﺄﻥ ﺭﺅﻭﺱ ﻧﺨﻠﻬﺎ ﺭﺅﻭﺱ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ، ﻗﻠﺖ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻓﻼ ﺍﺳﺘﺨﺮﺟﺘﻪ ؟ ﻗﺎﻝ : ﻗﺪ ﻋﺎﻓﺎﻧﻲ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻓﻜﺮﻫﺖ ﺃﻥ ﺃﺛﻴﺮ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻪ ﺷﺮﺍ 0 ﻓﺄﻣﺮ ﺑﻬﺎ ﻓﺪﻓﻨﺖ ‏) ‏( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ ).

*Sai Bashir Halilu ya ce*
Har yanzu ana yin sihrut takhayyal a matsayin wata hanya ta cutar da mutane, musamman don a damfari mutum. Zaka ga an buga maka kudi amma ba kudin bane, kawai iska ce. Bayan 'yan mintuna idan asirin ya sakeka sai kaga ba komai a hannunka.

Ana yinsa don a haukatar da mutum ko a ruda masa tunaninsa.

Wasu suna koyarsa don su dinga yin abubuwan burge mutane ko yaudararsu da suan *Karama*, ta inda za su dinga nunawa mutane kamar ga su suna ta6a wuta ko turare yana zubowa ta 'yan yatsunsu har ana jin kamshi alhali karya ce ba wuta suke ta6awa ba, ba tutarene yake zuba ajikinsu ba.

*YADDA MUTUM ZAI GANE AN YI MASA SIHRUT TAKHAYYAL*

1-Canjawar hakika. Wato ga yadda mutane suke ganin wani abu amma ya kasance kai wani abun daban kake gani.

2- Mutum zai dinga ganin kamar duniyar ta canja, yana ganin hayaki ko qura amma mutane za su ce ma sa ba haka bane.

3- Mutum zai dinga ganin kamar tsutsotsi suna hawa jikinsa, ko maciji zai sare shi ko wani abun tsoro yana kawo masa hari amma in yay ihu mutane suka taru za su ce basu ga komai ba.

4- In aka kawowa mutum abinci zai ga kamar abincin ya zama wuta ko yaga wata kazanta aciki wadda ba zai iya ci ba alhali ba komai a aciki.

5- Mutum zai dinga ganin wasu mutane sun zo suna hira da shi har yana ba su amsa amma a hakika shi kadai yake maganarsa.

6- Mutum zai dinga ji an kira sunansa ko anay masa magana amma in ya duba sai yaga bai ga kowa ba.

7- Mutum zai dinga ganin kamar wani ya gifta ta gabansa ko kamar wani abu zai fado masa.

8- Mutum zai ga gaba dayan mutane sun zama dabbobi ko kuma dabbobi sun zama mutane. Wani lokacin kuma matarsa ce zata dinga yi masa kama da wata dabba ko ita matar ta dinga ganin mjinta ya zama wata halitta ta daban.

9- Shi mutum akan-kansa, sai yaga ya zama wata dabba, misali mutum ya dauka ya zama zakara, ko ya zama rago. Don haka sai ya dena shiga cikin mutane, ya koma cikin raguna ko kaji yana zama kuma yana cin abinci irin nasu.

10- Wani zai ga kamar an canja duniyar, an dauke shi zuwa sama. Misali, idan ka ce masa 'Yanzu a ina muke?', zai iya ce ma ka 'Sama ta uku'. don shi anan yake ganin kansa.

11- Wani lokacin mutum yana zaune sai yaga kamar wata katanga zata fado masa, sai ya mike aguje, ko kuma yaga gidan ya ruguje gaba daya alhali ba katanga ce zata fado ba kuma gidan bai ruguje ba.

12- Mutum zai dauka ya zama Sarki ko ya zama Soja ko ya za Mai kwasar shara. Daidai sauransu. Don haka sai ya koma aiki irin nasu, misali, ya dinga shiga irinta sojoji, ko kuma ya dinga yawo yana tsintar ledoji, yana share titi a matsayinsa na ma'aikacin kwasar shara.
Da dai alamomi da yawa.

*_IRIN WANNAN SIHIRI YANA CIKIN AIYUKAN SHIRKA MASU FITAR DA MUTUM DAGA MUSULUNCI_*

*Allah Ya tsare mana imaninmu da lafiyarmu, ya karemu daga dukkan sharrin masu sharri.*

```Daga cibiyar Sunnah medicine, masu yin ruqiyyah da harhada magunguna na musulunci. Lambar waya```

08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts