YADDA ZA KA MAGANCE MATSALOLIN ALJANU DA ASIRI DA MAITA TA HANYAR MAGUNGUNA Kashi na biyu (2). Daga shafin Dr. Bashir Halilu. Lambar waya 08134434846
11- Haɗin magani. A samu Turar ruwa, gashin jima, Fusuhul jinni, da hiltit. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau daya. Amfaninsa. Wannan hadin yana karya sihiri, yana maganin yawan faduwar gaba da 6acin rai mara dalili da ciwon kan lokacin magriba da jin haushin mutane ba dalili. 12- Hadin magani. A samu Buruƙu, ganyen raiɗore, duman rafi da kaikayi-koma-kan-mashekiya. A tafasa a dinga sha da wanka. Amfaninsa. Maganin Kowace irin lalura ta Aljanu wacce ta shafi cikin jiki, ciki, mara, ƙirji, ƙasusuwa, ciwon kai da dai sauransu. 13- Hadin magani. Sassaƙen gawo, kaikayi koma kan mashekiya, sassaken katsari. A dafa, sha da wanka. Yana maganin sammu da maita da baki da kambun ido. 14- Hadin magani. A samu Ganyen sarka...