YANA DAGA KYAKKYAWAR ƊABI'A A MUSULUNCI MUTUM YA BAR SHIGA ABINDA BA SHI DA AMFANI A GARE SHI KO ABINDA BA ZAI TAIMAKE SHI BA.

Daga shafin Bashir Halilu.

عن أبي هريرةَ رَضِي اللهُ عَنْهُ قالَ: قالَ رسولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:

{مِنْ حُسْنِ إِسْلاَمِ الْمَرْءِ تَرْكُهُ مَا لاَ يَعْنِيهِ}.

حديثٌ حَسَنٌ رواه التِّرمذيُّ وغيرُه هكذا

     Ma'ana:
     An karɓo daga Abū Huraira (Allah ya yarda da shi) cewa: 
    "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

    "Daga kyawawan halayen Musulunci na mutum shi ne barin abin da bai shafe shi ba."

    Wannan hadisin yana nuna cewa daga cikin kyautata Musulunci da halayyar mutum shi ne ka guji shiga abubuwan da ba su dameka ba, ba za su amfanar da kai a cikin addininka ko rayuwarka ta yau da kullum ba. Kamar shiga harkokin wasu mutane, yawan magana marar amfani, ko tambayar abin da ba zai amfani mutum ba.

     Wannan hadisi kuma yana koyar da:

1. Mutum ya tsaya akan abin da ya shafe shi kawai.

2. Yana hana shiga cikin sirrin mutane ko yawan tambayoyi da suka wuce gona da iri.

3. Yana karfafa tarbiyyar kirki da nutsuwa da kamun kai.

4. Yana sa mutum ya mai da hankali kan abubuwan da zasu amfanar da shi a duniya da lahira.

5. Yana nunar da Musulmi akan ya auna dukkan abinda zai aikata, idan zai samu fa'ida a duniya ko lada a lahira sai ya aika, idan kuma babu sai ya bar shi.

       Allah Ya sa mu yi aiki da wannan hadisi wajen kaucewa zaƙulo laifukan waɗansu da aibobinsu da kuma shiga tsakanin Allah da bayinSa.

Daga shafin Bashir Halilu.

Comments

Popular Posts