YADDA IBLIS YA SO YA ƁATAR DA MATAR ANNABI AYYUBA (AS).



   Daga shafin Bashir Halilu.

    Mun karanta a ƙissar Annabi Ayyuba (AS) cewa Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya mai tsanani, wacce ta kai ba ya iya komai da jikinsa, ƴaƴansa duka su ka mutu, dabbobinsa duka su ka mutu, dukiyarsa ta ƙare, jama'arsa su ka guje shi, sai matarsa ce kawai ta kasance tare da shi ta ke taimakonsa. Ita ce mai nemo abinci da gyara masa jikinsa. Kafin rashin lafiyar, Allah Ya azurta Annabi Ayyuba da yawan ƴaƴa da tarin dukiya mai yawa da ma'aikata da manyan gine-gine da taimakon mabuƙata da yawan ibada, kamar dai yadda mu ka kawo a cikin ƘISSAR ANNABI AYYUBA (AS).

      Ibni Abid Dunya, ya kawo acikin littafinsa Maka'idish Shaiɗani cewa:

     "Fudhayl bin Abdul-Wahhab ya ba mu labari, ya ce: Abubakar bin Ayyash ya ba mu labari, daga Ibn Wahb bin Munabbih, daga mahaifinsa, ya ce:

      "Iblis ya tambayi matar Annabi Ayyuba (A.S), ya ce:

     “Me ya sa kuka fuskanci wannan bala’in da ya same ku?”

Sai ta ce: “Ƙaddarar Allah Maɗaukaki.”

      Sai Iblis ya ce: “To, ki biyo ni.”

    Sai ta biyo shi. Sai ya nuna mata dukan dukiyar da suka rasa a wani kwari (rami mai zurfi).
   Sai ya ce: “Ki yi min sujjada , ni kuma zan dawo muku da dukkan abinda ku ka rasa.”

     Sai ta ce: “Ina da miji, bari in je in nemi izininsa.”

    Ta koma ta sanar da Annabi Ayyuba (A.S), sai ya ce mata:
     “Shin har yanzu ba ki gane cewa wannan shi ne Shaiɗan ba?, Wallahi idan na warke daga wannan cutar, sai na yi miki bulala ɗari!”

❋・────━【❆】━────・❋

   Wannan Ƙissa akwai darussa da yawa aciki. Ɗaya daga ciki shi ne: duk abinda Allah Ya jarrabe ka ka rasa shi, to idan aka ce ka saɓawa Allah domin abun ya dawo kada ka aikata, domin yaudara ce daga Shaiɗan. Zai sa ka yi biyu-babu. Ba dukiya kuma ba imani.

    Allah Ya kiyaye mu.

    Daga shafin Bashir Halilu.

Comments

Popular Posts