MATSALAR KARKACEWAR BAKI DA YADDA AKE MAGANCE SHI.



Daga shafin Bashir Halilu.

      Matsalar Karkacewar Baki (Facial Deviation ko Mouth Deviation) wani yanayi ne da bakin mutum ko fuskarsa ke karkata zuwa gefe guda, musamman lokacin magana, dariya, ko kuma lokacin da ba a motsa fuskar gaba ɗaya. Wannan matsala na iya zama alamar wata cuta mai tsanani ko matsala a jijiyoyi, musamman jijiyar fuska.

ABUBUWAN DA KE KAWO KARKACEWAR BAKI 
1. Ciwan jijiyar fuska.
Wannan yana faruwa ne idan jijiyar fuska ta kamu da kumburi ko takura, yana haifar da gazawar motsi a gefen fuska guda ɗaya. Wato jijiyar ta takure, ta yadda ba ta iya miƙewa sosai ta yi aikinta, sai ɓangaren ya karkace.

2. Bugun jini da ake kira da 'stroke'.
Idan jinin da ke kai iskar oxygen zuwa kwakwalwa ya tsaya, yana iya sa gefen fuska ya mutu ko ya karkace.

3. Ciwon ƙwaƙwalwa.
Ciwon da ke tasowa a kusa da jijiyoyi ko cikin ƙwaƙwalwa na iya shafar jijiyar fuska.

4. Rauni.
Jin ciwo ko bugewa a kai na iya lalata jijiyar fuska, wanda hakan kan iya janyo karkacewar baki ko fuska gaba ɗaya.

5. Ciwon kunne.
Ciwon kunne na can ciki da ya kai ga jijiyar fuska, na iya hana jijiyar fatar kumatu sakewa da janyo karkacewar baki.

6. Matsalar narkewar jini da ake kira 'Diabetes, Hypertension'
Na iya rage ƙarfin jijiyoyi da kawo matsala a fuska ko jijiyoyin fatar baki.

ALAMOMIN KARKACEWAR BAKI 

1- Baki ya karkata gefe guda, dama ko hagu.

2- Daga gira ko rufe ido ya zama da wahala a wajen mutum.

3- Ya kan haɗa da ciwon kai ko kunne.

4- Fuska ta kasa motsi.

5- Rashin iya dariya ko magana yadda ya kamata.

6- Idan mutum zai yi murmushi sai fatar bakinsa da laɓɓansa su karkata gefe guda.

YADDA AKE HAƊA MAGANIN KARKACEWAR BAKI 

(wanda yakan faru sakamakon buguwar jini ko wasu cututtukan da suka shafi jijiyoyin kwakwalwa)

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

1. Citta – Ɗan yatsa 1, a daka ta sosai.
2. Kanunfar– Ƙwaya 7 zuwa 10, a daka su
3. Ganyen magarya – Ganyaye 7 zuwa 10, a jika a ruwa
4. Ganyen ɓaure – A tafasa shi da ruwa
5. Man zaitun – Gwangwani ɗaya.
6. Zuma – Gwargwadon buƙata.

7. Ƴaƴan Habbatus Sauda – A daka ta.
8. Ganyen zogale.

Yadda Ake Haɗawa:

      A haɗa citta, kanunfari, habbatus sauda da man zaitun, a tafasa su a cikin ƙaramar tukunya na minti 10. A tace ruwan sannan a zuba zuma da ɗan ruwan ganyen magarya ko baure da aka tafasa a ciki. A ɗora tukunya a wuta, a juya haɗin har sai ya ɗan yi kauri. A bar shi ya huce. Sai a dinga sha cokali 1 da safe da yamma bayan cin abinci na tsawon kwanaki 21 zuwa 40.
    Wannan haɗi zai warkar da karkacewar baki wanda ya ke da alaƙa da cikin bakin.

 Na shafawa daga waje 

    A ɗauki man zaitun da habbatus sauda da citta, a tafasa su tare, a barshi ya huce, a rika shafawa gefen bakin da ya karkace da safe da yamma.

Idan akwai wanda zai iya yi maka tausa 'massage' a gefen fuskar da wannan man, zai fi kyau 

  Ga mai bukatar maganin da mu ka haɗa domin magance karkacewar baki da sauran magunguna na matsalolin iska ko cututtuka na yau da kullum sai a tuntuɓe mu a wannan lamba 08134434846.

Daga shafin Bashir Halilu.
Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts