AIKIN SAƁON DA SHAIƊAN YA FI SO YA SAKA MUSLMI
Daga shafin Bashir Halilu
Ibni Abid dunya ya ruwaito cewa: Al-Qurashiy ya ce: Ahmad bin Jameel Al-Marwazi ya ba ni labari, ya ce: Ibnul-Mubarak ya ba mu labari, ya ce: Sufyan ya ba mu labari daga Aɗā’ binis-Sā’ib daga Abū ‘Abdir-Raḥmān as-Sulamī daga Abū Mūsā (Allah ya yarda da shi) ya ce
“Idan Iblis ya wayi gari, sai ya baza sojojinsa a doron ƙasa, sai ya ce:
‘Wane ne ya ɓatar da wani Musulmi?, zan sa masa kambun sarauta’
Sai ɗaya daga cikinsu ya ce: ‘Ban bar wane ba sai da ya saki matarsa.’
Sai Iblis ya ce:
‘Ai zai iya sake aure.’
Sai wani Shaiɗanin ya ce: ‘Ban bar wane ba sai da ya saba wa iyayensa.’
Sai Iblis ya ce:
‘Ai zai iya yi musu biyayya daga baya.’
Sai wani ya ce: ‘Ban bar wane ba sai da ya yi zina.’
Sai Iblis ya ce: ‘Kai ne!’
Sai wani ma ya ce: ‘Ban bar wane ba sai da ya sha giya.’
Sai Iblis ya ce: ‘Kai ne!’
Sannan wani ma ya ce: ‘Ban bar wane ba sai da ya kashe wani.’
Sai Iblis ya ce: ‘Kai ne! Kai ne! (Kai na fi so!)’
Duba littafin Maka'idish Shaiɗan.
Daga shafin Bashir Halilu.
Comments
Post a Comment