CIWON HAƘORI DA YADDA AKE MAGANCE SHI
Daga shafin Bashir Halilu.
Ciwon haƙori 🦷 yana nufin zafi ko ciwo da ke tasowa daga cikin haƙori ko kuma daga kewayensa kamar dadashi, asalin jijiyoyi ko ƙashin da ke rike haƙoran. Ana iya samun rami a cikin haƙori ko ruɓewar haƙori ko kuma ƙwayoyin cuta masu illata haƙora.
IRE-IREN CIWON HAƘORI
1. Ruɓewar haƙori (Tooth Decay):
Yana faruwa ne saboda cin abinci mai sikari da yawa, kamar shan alewa, da rashin wanke baki yadda ya kamata, samuwar ƙwayoyin cuta masu lalata haƙori.
2. Ciwon Dadashi (Gum Disease):
Wanda ke haddasa kumburi da zubar jini daga dadashin.
3. Ciwon Jijiyar Haƙori (Pulpitis):
Yana faruwa ne idan jijiyar da ke cikin haƙori ta kamu da cuta ko ta kumbura.
4. Ciwon Ƙashin haƙori (Abscess):
Wanda ke faruwa sakamakon ruɓewar ƙwayoyin cuta a tushen haƙori ko cikin ƙashin haƙori.
5. Ciwon Haƙorin Turmutsutsun haƙora (Wisdom Tooth Pain):
Shi kuma yana faruwa ne idan haƙori ya kasa fita da kyau ko yana matsawa sauran haƙora.
6. Kuɗar haƙori. (Tooth Sensitivity):
Wato jin zafi idan an ci abu mai sanyi, abu mai zafi, abu mai ɗaci ko abu mai tsami.
ALAMOMIN CIWON HAƘORI
1- Zafi mai tsanani a haƙori.
2- Jin ƙaiƙayi ko tsami a haƙori.
3- Fitar jini daga dadashi.
4- Kumburi a fuska ko kumatu.
5- Warin baki mara daɗi.
6- Jin haƙori yana rawa.
7- Ciwon kai ko jiri (idan ciwon ya tsananta).
8- Zafi idan taɓa haƙora ko aka tauna wani abu.
YADDA AKE HAƊA MAGANIN CIWON HAƘORI.
Daga shafin Bashir Halilu.
Mai bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.
Ga yadda za ka iya haɗa magungunan gargajiya don magance kowanne daga cikin nau'o'in ciwon haƙori guda shida da aka ambata.
1) Ruɓewar Haƙori (Tooth Decay).
A samu ganyen darbejiya, ka busar da shi a inuwa, ka niƙa ya zama gari. Sai ka samu Gishi da Man kwakwa. A haɗa garin ganyen darbejiyar da gishiri, sai a zuba ɗan man kwakwa a ciki. A shafa haɗin da brush ko yatsa a kan haƙoran da suka ruɓe sau biyu a rana na tsawon sati 1-2.
2) Ciwon Dadashi (Gum Disease)
A samu ganyen goba, a tafasa da ruwa. Sai a samu garin kanumfari da Gishiri kaɗan.
A dinga wanke bakin da ruwan ganyen goba sau biyu a rana. A sa garin kanumfari da gishiri a cakuda, a dinga shafawa a kan dadashin da yatsa.
3) Ciwon Jijiyar Haƙori (Pulpitis)
A samu garin ɓawon kuka, a tafasa shi sosai. Sai a samu Tafarnuwa, a markaɗa ta, a ɗan zuba ruwan dumi. Sai a samu ganyen Ɗoɗɗoya.
A ɗaiki tafarnuwar a ɗora a inda ciwon ke damun mutum. A wanke baki da ruwan bawon kuka da safe da dare. Sai kuma ka dinga tauna ganyen Ɗoɗɗoya da haƙorin.
4) Ciwon Ƙashin Haƙori (Dental Abscess)
A samu Tafarnuwa, da Gishiri, a tafasa gishirin da ruwa. Sai a samu Zuma mai kyau.
Sai a markaɗa tafarnuwar, a zuba kaɗan a wajen da ke ciwon, a riƙe na minti 5. A dinga wanke baki da gishirin da ruwan dumi sau 3 a rana. A ɗan ɗora zuma a wurin idan ya kumbura ko yana zafi sosai.
5) Ciwon Wisdom Tooth (Turmutsutsun haƙora)
A samu Ganyen Ɗoɗɗoya, a tafasa da ruwa. Sai a samu Kanumfari a niƙa shi.
A dinga tauna garin kanumfarin a kusa da haƙorin da ke ciwon kuma a rinƙa wanke baki da ruwan ganyen Ɗoɗɗoya sau 2 zuwa 3 a rana.
6) Kuɗar Haƙori (Tooth Sensitivity)
A samu Gishiri da baking soda da Ganyen Na'ana'a.
A haɗa baking soda da gishiri, a yi brush da shi sau ɗaya a rana. A wanke baki da ruwan tafasasshen ganyen mint da safe da dare.
ƘARIN SHAWARA WAJEN KULA DA LAFIYAR HAƘORA.
1- Wanke baki bayan kowanne cin abinci.
2- Ka rage abubuwan sikari da tsami mai yawa.
3- Ka dinga amfani da magungunan da ke hana ƙwayoyin cuta (misali tafarnuwa da kanumfari).
4- Ka dinga shan ruwa da yawa.
Daga shafin Bashir Halilu mai bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.
Comments
Post a Comment