GYARA ADON MACE .INA MATA MASU SON GYARA DA KYAUTATA LAFIYAR JIKINSU?
GYARA ADON MACE .
INA MATA MASU SON GYARA DA KYAUTATA LAFIYAR JIKINSU?
Wannan haɗin magani da za mu koya muku, an tsara shi ne daga tsirrai da abinci masu gina jiki, wanda za a iya amfani da shi musamman wajen ƙarfafa lafiyar mace a fannoni daban-daban.
Daga Shafin Bashir Halilu
Haɗin yana taimakawa wajen
1- Ƙara girman mama (cikowar nono).
2- Inganta lafiyar mahaifa.
3- Ƙara jini da kuzari ga mace.
4- Inganta sha’awa da ni’ima.
5- Ƙara nauyi, ƙiba da ni’imar jiki.
6- Taimakawa masu fama da rashin haihuwa.
7- Cikakken gyaran jiki bayan haihuwa ko juna biyu.
ABUBUWAN DA ZA A NEMA
1- Hulba gwangwani huɗu
2- Waken suya gwangwani huɗu
3- Farar shinkafa gwangwani biyu
4- Gero gwangwani biyu
5- Jar masara gwangwani biyu
6- Aya gwangwani biyu
7- Kantu gwangwani biyu
8- Ɗanyar gyaɗa gwangwani biyu
9- Garin busasshen dabino rabin gwangwani
10- Nazarƙwaila murfi ɗaya
11- Gadali ɗan ƙarami
12- Garin ƴaƴan kan-ɓarawo gwangwani ɗaya
13- Madara rabin gwangwani
14- zuma lita ɗaya
AMFANIN KOWANE SINADARI A JIKIN MACE.
1. Hulba
– Tana ƙara girman nono sosai.
– Tana warkar da cututtukan mahaifa.
– Tana taimako wajen daidaita haila da warkar da ciki bayan haihuwa.
2. Waken suya:
– Yana da sinadarin protein da phytoestrogen, wanda ke da alaƙa da ƙara girman nono da lafiyar mata.
– Yana ƙara kuzari da gina jiki.
3. Farar shinkafa:
– Tana ƙara nauyin jiki da sinadarin kuzari.
– Tana cike da carbohydrates masu sauƙin narkewa.
4. Gero:
– Yana ƙara jini da ƙarfafa jijiyoyi.
– Yana da iron da fiber, masu taimako ga masu fama da rauni.
5. Jar masara:
– Tana ƙara kuzari da yawan jini.
– Tana ƙara cikakken nauyin jiki da ni'ima.
6. Aya:
– Tana ƙara sha’awa da ni’ima ga mace.
– Yana gyara mahaifa da karin sinadarin magnesium da zinc.
7. Kantu:
– Yana taimakawa wajen busar da jini ko kumburi a mahaifa.
– Yana ƙara lafiya da sabbin sinadarai ga jiki.
8. Ɗanyar gyaɗa:
– Babban tushen protein da healthy fat, tana ƙara ƙiba mai kyau da kuzari.
– Tana da kyau wajen sake gina jiki bayan juna biyu.
9. Garin dabino:
– Yana ƙara jini sosai.
– Yana ƙara sha’awa da kuzari.
10. Nazarƙwaila :
– Tana ƙara sha’awa, tana da sinadarin da ke motsa jijiyoyi da hankali.
– Tana taimakawa wajen daidaita jinin haila.
11. Gadali :
– Babban sinadari ne na gyaran mahaifa da busar da ruwa.
– Yana hana infection a farji.
12. Garin ƴaƴan kan-ɓarawo:
– Yana ƙara lafiyar jijiyoyi da magance cututtukan hanji.
– Yana kara kuzari da motsa sha’awa.
_ Yana ciko da nonon mace.
13. Madara:
– Tana ƙara sinadarin calcium da protein.
– Tana gina ƙashi da ƙarfafa garkuwar jiki.
14. Zuma:
– Tana tsaftace jiki, tana ƙara kuzari da karfi.
– Tana gyaran ciki da fitar da guba.
YADDA AKE HAƊAWA
Ki haɗa kayayyakin, ki tsaftace su sosai, kada ki surfa kowanne amma za ki iya wankewa. Sai ki haɗa su waje ɗaya, ki niƙa, su zama gari. Ki dinga ɗibar babban cokali biyu ko uku, ki dama du ruwan zafi. Sai ki zuba madara da zuma aciki, ki sha. Kullum sau biyu.
Waye zai fi amfani da wannan haɗin?
1- Macen da ke son ƙara girman nono ko ƙiba.
2- Macen da ta haihu ko ta ke shirin haihuwa.
3- Wadda ke da karancin jini ko rauni a jiki.
4- Wadda ke son gyaran ciki da mahaifa.
5- Wadda ke fama da raunin sha’awa ko bushewar gaba.
6- Matar da ke son ƙara ƙiba da murmurewa.
Duk mai bukatar haɗaɗɗen maganin ko haɗin Sabaya na musamman da sauran magunguna, sai a kira wannan lamba 08134434846.
Daga shafin Bashir Halilu mai bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.


Comments
Post a Comment