CIWON ZUCIYA DA MAGUNGUNANSA


Daga shafin Bashir Halilu.

🫀 Menene Ciwon Zuciya 🫀?

     A likitance, ana kiran ciwon zuciya da sunaye iri-iri bisa ga irin matsalar da take faruwa, kamar:

1. Coronary Artery Disease (CAD) – Bushewar jini ko danƙarewa a jijiyoyin zuciya.

2. Heart Failure – Raguwa ko gazawar zuciya wajen aikin tunkuɗa jini.

3. Arrhythmia – Bugun zuciya wanda ya ke gudu ko jinkiri ba bisa ƙa'ida ba 

4. Cardiomyopathy – Raguwar ƙarfi ko kumburin tsokar zuciya.

5. Valvular Heart Disease – Matsala da kofar zuciya (valves).

ALAMOMIN CIWON ZUCIYA
1- Jin ciwo ko danna a ƙirji.
2- Wahalar numfashi.
3. Yawan gajiya mai tsanani ba tare da an yi aiki mai yawa ba 
4- Bugun zuciya da sauri ko rashin daidaito.
5- Hawan jini ba bisa ƙa'ida ba.
6- Yawan gumi ba tare da an yi aiki ba.
    Da dai sauransu.

WASU DAGA CIKIN ABUBUWAN DA KE KAWO CIWON ZUCIYA 

1- Cin abinci mai yawan mai da gishiri.
2-Shan taba ko giya da sauran kayan shaye-shaye.
3- Rashin motsa jiki
4- Hawan jini wanda aka gaza shawo kan sa.
5- Ciwon sukari (diabetes)
6- Yawan damuwa (stress)
7- Gado, wato tarihin ciwon zuciya a iyaye ko kakanni.

MAGUNGUNAN DA ZA SUKE TAIMAKAWA MAI CIWON ZUCIYA WAJEN SAMUN WARAKA.

1. Ganyen Zogale
       Yana saukar da hawan jini, yana wanke jijiya daga kitse.
  Ana dafawa kamar shayi ko a markada a sha safe da yamma.

2. Tafarnuwa
      Tana rage cholesterol, tana tsaftace jijiyoyin jini.
  Za a iya shan tafarnuwa ɗaya ko biyu a kowace safiya da rana da dare.

3. Ɗanyar Citta.
        Tana taimakawa hawan jini da hana ɗanƙarewar jini a zuciya.
   Ana iya yin shayin citta ko a jika a ruwa a sha.

4. Lemon Tsami.
     Yan rage yawan cholesterol kuma yana taimakawa wajen narkar da abinci.
   A haɗa ruwan lemon tsami da ƴar zuma da ruwa mai ɗumi, a sha da safe.

5. Ƙwayoyin Habbatus Sauda.
    Amfani da su na ƙarfafa zuciya da numfashi, da baiwa jijiyoyi kuzari.
  A haɗa garin Habbatus sauda da zuma a sha cokali 1 da safe da yamma.

6. Girfa.
   Tana rage sinadarin sugar da cholesterol.
    Ana iya dafawa da shayi ko ruwan dumi, a sha yi.

7. Ganyen Gwanda.
    Yana ƙarfafa zuciya da rage gajiya.
  A dafa ganyen a sha kamar shayi sau 1 a rana.

   
     Waɗannan magunguna da mu ka ambata suna taimakawa mai ciwon zuciya wajen samun sauƙi amma fa dole ka yi la'akari da nau'in ciwon zuciyar da ke damunka wajen zaɓar nau'in maganin da za ka haɗa.

   Ga wanda ya ke buƙatar maganin da muje haɗawa na ciwon zuciya da sauran cututtuka zai iya tuntuɓarmu a wannan lamba 08134434846.

    Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts