RAYUWAR JINNUL ƘARIN Nau'in Aljanin da kowane mutum yana da shi a jikinsa, har Annabawa.

RAYUWAR JINNUL ƘARIN

Nau'in Aljanin da kowane mutum yana da shi a jikinsa, har Annabawa.

Daga shafin Bashir Halilu.

     Alƙur’ani da Hadisai sun yi magana akan jinnul ƙarīn, wato Aljani mai rakiyar mutum, wanda ke tare da shi tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Wannan Aljani mugun Aljani ne asali, kuma yana da halaye da ayyuka da suka shafi saka mutum ya aikata sharri da ruɗar mutane. Asalin Jinnul Ƙariyn dukkansu kafurai, maƙiya Allah da Manzonsa kuma aikinsu a koda yaushe shi ne su sa mutum ya aikata saɓo.

   Ga hujjoji daga Alƙur'ani mai girma da Hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kuma magangun Malaman sunnah akan samuwar jinnul Ƙariyn, kasantuwarsa tare da kowane mutum da kuma yadda suke cutar da mutane ta hanyar saka su saɓon Allah.

BAYANI AKAN JINNUL ƘARIN DAGA ALƘUR'ANI 

1) Suratu Ƙaf, ayah ta 27.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

قَالَ قَرِينُهُ رَبَّنَا مَا أَطْغَيْتُهُ وَلَكِن كَانَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ   • قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا لَدَى وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِالْوَعِيدِ • مَا يُبَدَّلُ الْقَوْلُ لَدَى وَمَا أَنَا بِظَلَّامٍ لِلْعَبِيدِ • 

Ma'ana:

27. Shaidaninsa ya ce: "Ya Ubangijina, ni ban batar da shi ba, sai dai kawai ya kasance cikin bata mai nisa."

28. (Allah) ya ce: "Kada ku yi husuma a gabana, hakika tuni Na gabatar muku da gargadin azaba.

29. "Ba a sauya magana a gabana, kuma Ni ba mai zaluntar bayi ba ne."

  Sharhi:

    Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a nan ne shi kafirin zai nemi ya kawo wani hanzari na kauce wa hanyar Allah da cewa, shaidaninsa ne ya hallaka shi ya batar da shi. Sai shi kuma shaidanin nasa ya musunta hakan, ya tabbatar wa da Ubangiji cewa, ba shi ne ya batar da shi ba; da ma can ya kasance cikin bata mai nisa, watau yayin da ya hadu da shaidaninsa za-mu ce ta tadda mu-je-mu.

Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, bayan husuma ta kaure tsakanin kafiri da shaidaninsa, sai ya daka musu tsawa cewa, su daina wata husuma da jayayya a gabansa, wadda ba ta da wani amfani, domin kuwa tun a duniya ya aika musu da manzanninsa da narkon azaba ga duk wanda ya kafirce masa ya bijire wa umarninsa. Ya kuma tabbatar musu da cewa, shi ba a sauya magana a wurinsa, kuma ba ya saba alkawarinsa, ba kuma ya zaluntar bayinsa ko ya tauye musu kyawawan ayyukansu...."

     (Fassarar Hausa da sharhi: Dr. Sani U.R.L.)

2) Suratu Zukhruf, ayah ta 36.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
وَمَن يَعْشُ عَن ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانَا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ • وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُهْتَدُونَ • حَتَّى إِذَا جَاءَنَا قَالَ يَلَيْتَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ بُعْدَ الْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ الْقَرِينُ • وَلَن يَنفَعَكُمُ الْيَوْمَ إِذْ ظَلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ •

Ma'ana:

36. Wanda kuwa ya zama mai dundumi game da ambaton (Allah) Mai rahma, to za Mu hada shi da Shaidan ya zama shi ne abokinsa.

37. Lalle kuma su (shaidanun) tabbas suna kange su daga tafarki nagari, su kuma suna zato cewa lalle su shiryayyu ne.

38. Har zuwa lokacin da suka zo mana (wato mutumin da shaidaninsa) sai ya ce: "Ina ma a ce tsakanina da kai akwai nisan gabas da yamma; to tir da aboki irinka."

39. (Allah Ya ce da su): "A yau tun da kun riga kun yi zalunci zamantowarku tare a cikin azaba ba zai amfane ku ba
(Fassarar Hausa: Dr. Sani U.R.L.).

SAMUWAR JINNUL ƘARIN DAGA HADISAN MANZON ALLAH (SAW).

Ga wasu ingantattun hadisai da suka yi magana kai tsaye akan jinnul qarīn (القرين) — wanda ake nufi da aljani da Allah Ya ɗaura ga kowanne mutum:

 1)  Sahih Muslim (2814)

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ:

"ما منكم من أحدٍ إلا وقد وُكِّل به قرينه من الجن." قالوا و أنت يا رسول الله؟ قال
"وإياي، إلا أن الله أعانني عليه فأسلم، فلا يأمرني إلا بخير."

Ma'ana: 

    A cikin Sahih Muslim, an karɓo daga Abdullahi, ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce:

> “Babu wanda ke cikinku face an ɗaura masa qarīn daga cikin aljanu.”

Sahabbai su ka ce:
“Kai ma (kana da shi) ya Rasulallah?”
Ya ce:
“Ni ma haka ne, amma Allah Ya taimake ni a kansa har ya musulunta, kuma ba ya umartata da komai sai alheri.”

      Wannan hadisin yana nuna cewa kowane mutum yana da qarīn daga cikin aljanu, sai dai na Annabi ﷺ ya musulunta, don haka ba zai iya sa shi ya aikata saɓo ba.

 2)  Sahih Muslim (2813)

عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قالت:

> دَخَلَ عَلَيَّ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ فَوَضَعْتُ لَهُ وِسَادَةً فِيهَا تَصَاوِيرُ، فَوَقَفَ، فَلَمْ يَجْلِسْ، وَبَدَا عَلَى وَجْهِهِ الْكَرَاهِيَةُ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَتُوبُ إِلَى اللَّهِ، مَاذَا أَذْنَبْتُ؟ قَالَ:
> "مَا بَالُ هَذِهِ الْوِسَادَةِ؟"

> قُلتُ: "اتَّخَذْتُها لكَ لِتَجلسَ عليها."
قال "إِنَّ أَشَدَّ النَّاسِ عَذَابًا يَوْمَ الْقِيَامَةِ الَّذِينَ يُضَاهُونَ بِخَلْقِ اللَّهِ."
ثم قال "وَقَرِينِي قَدْ جَلَسَ لِي عَلَى ذَلِكَ."

Ma'ana: 

    An karɓo daga Nana A’isha (RA), ta ce:

> Manzon Allah ﷺ ya shigo wajena, sai na shimfiɗa masa matashi mai dauke da hotuna. Sai ya tsaya, bai zauna ba, fuskar sa tana nuna ƙyama. Sai na ce: “Ya Manzon Allah, ina tuba zuwa ga Allah, me na yi?”
Sai ya ce: “Me ye a jikin  wannan matashin?”
Na ce: “Na yi shi ne domin ka zauna a kai.”
Sai ya ce: “Lallai mafi tsananin azaba a ranar ƙiyama su ne masu kwaikwayon halittar Allah.”
Sannan ya ce: “Qarīn nawa ne ya yaudareni hankalina ya kai kan hakan.”

       Wannan yana nuna cewa jinnul qarīn yana iya ƙarfafa mutum zuwa ga abin da bai dace ba, idan ba a gina tsoron Allah da tsarkin zuciya ba.

MAGANGANUN MALAMAN SUNNAH AKAN SAMUWAR JINNUL ƘARIN TARE DAƊAN ADAM.

1) Shaikhul Islam Ibnu Taymiyyah Allah Ya gafarta masa a cikin Majma'il-Fatāwā (18/122) ya ce:

        "Aljanu na iya shiga cikin jikin ɗan Adam, su yi magana da harshensa da wata magana da shi kansa ba ya gane ta, ko da yake ba ya ma jin yana faɗinta. Wannan al'amari ya shahara a wajen masu ilimi da waɗanda ba su da shi, har a kan gani da ido. Kuma Jinnul ƙarīn wani nau’i ne daga cikin waɗannan aljanu."

2)  Ibnul l-Qayyim Allah Ya gafarta masa, a cikin Zādul-Maʿād (3/117) ya ce:

     "Jinnul ƙarīn yana da iko a kan mutum, kuma babu wanda ke kubuta daga gare shi sai wanda Allah Ya kiyaye shi kuma Ya kare shi daga sharri. Irin waɗannan kuwa su ne muminai na gaskiya waɗanda ke kare kansu da ambaton Allah da sallah."

3) Shaykh Ibn ‘Uthaymeen Allah Ya gafarta masa, a cikin Sharḥu Riyāḍhus -Ṣāliḥīna ya ce:

      "Jinnul ƙarīn daga cikin aljanu an naɗa shi bisa mutum, yana ƙawata masa sikat laifuka kuma yana ƙarfafa shi wajen aikata su. Sai dai ba ya iya tilastawa mutum yin biyayya gare shi, domin yana da iko da zaɓi a hannunsa."

4) Shaykh Ṣāliḥ al-Fawzān Allah Ya ƙara masa lafiya, a cikin Sharḥu Kitāb at-Tawḥīd ya ce:

       "Jinnul ƙarīn Shaiɗani ne, yana tare da mutum, ba ya rabuwa da shi, yana sanya masa wasuwasi, yana ƙawata masa sharri da ƙyamar alheri. To, shi abokin gaba ne mai manne wa mutum, kuma bawan Allah ba zai kuɓuta daga gare shi ba sai ta hanyar neman tsari da ambato da kuma tsoron Allah."

YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUL ƘARIN YA SAMU RINJAYE AKANSA 

   Sheikh Wahid Abdus-Salām Bāli da wasu daga cikin Malaman sunnah, sun bayyana wasu alamomi da mutum zai gane cewa Jinnul Ƙarin ya samu rinjaye akansa.

1. Yawan muguwar sha’awa da mugun tunani mara kyua ba tare da dalili ba.

2. Kiyayya da jin tsana ga ayyukan addini, kamar sallah da karatun Al-Qur’ani.

3. Yawan mantuwa da ruɗewa musamman yayin ibada.

4. Jin murya ko magana a cikin kai daga wani kamar yana umarni ko hana abu.

5. Fushi da saurin ɓacin rai da rashin haƙuri ba tare da hujja ba.

6. Ciwon kai ko jiki ba tare da bayyanannen dalili ba.

7. Canjin hali: mutum yana yin abubuwa marasa kyau da ba dabi’arsa ba.

8. Mugun mafarki ko mafarkin jima'i da mace/namiji.

9. Jin kamar akwai wanda ke tare da mutum ko yana magana da shi.

10. Yawan jinkirin ci gaba a rayuwa duk da ƙoƙari.

Idan mutum na da waɗannan alamomi, yana da kyau ya nemi ruqya ta shari’a daga masani.

YADDA AKE NEMAN TSARI DAGA SHARRIN JINNUL ƘARIN 
Malamai sun yi bayani cewa ana samun tsari daga sharrin Jinnul Ƙarin ne ta hanyar karatun Alƙur'ani, addu'o'in neman tsari da kula da ibada kamar sallah akan lokaci da kuma ƙarfafa zuciya akan ayyuka alkhairi da gujewa munanan ayyuka.

    Ya Allah Ka tsare mu daga sharrin duk wani Shaiɗani, mutum da Aljan. 

     Daga Shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya. 
Lambar waya 08134434846.

Comments

Popular Posts