KIRARIN DA SHAIƊAN YA KE YI WA MATA. ❋・────━【❆】━────・❋

Daga shafin Bashir Halilu 

Mu dai mun ce mata iyayenmu ne, mata tushen rayuwa kuma jigonta amma ga kirarin da Shaiɗan fitinanne ya ke yi wa mata .

 قال القرشي: وحدثني مُحَمَّدُ بْنُ إِدْرِيسَ، حدثنا أَحْمَدُ بْنُ يُونُسَ، حدثنا الْحَسَنُ بْنُ صَالِحٍ قَالَ: : سَمِعْتُ أَنَّ الشَّيْطَانَ قَالَ لِلْمَرْأَةِ:

    أَنْتِ نِصْفُ جُنْدِي، وَأَنْتِ سهمي الذي أرمي به فلا أخطأ، وَأَنْتِ مَوْضِعُ سِرِّي وَأَنْتِ رَسُولِي فِي حَاجَتِي.
(مكائد الشيطان، لابن أبي الدنيا)

      Al-Qurashiy ya ce: Muhammadu bin Idris ya zantar da mu, ya ce: Ahmad bin Yunus ya zantar da mu, ya ce: Al-Hasan bin Salih ya ce:

     "Na jiyo cewa Shaiɗan ya ce wa wata mata: 
    "Ke rabin sojojina ce, ke kibiyata ce da nake harbi da ita kuma ba ta taɓa kuskure ba, ke ce wurin sirrina, kuma ke ce jakadiyata wajen buƙatata."

     (Duba littafin Maka'idish Shaiɗan na Ibni Abid dunya).

Daga shafin Bashir Halilu.

Comments

Popular Posts