ASALIN HALITTAR AL-JANU MAZAUNA CIKIN RUWA.
Daga shafin Bashir Halilu.
A cikin Alkur'ani mai girma, Allah Maɗaukakin Sarki Ya na cewa:
وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ عَاصِفَةً تَجْرِى بِأَمْرِهِ إِلَى الْأَرْضِ الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا وَكُنَّا بِكُلِّ شَيْءٍ عَالِمِينَ ٠ وَمِنَ الشَّيَاطِينِ مَن يَغُوصُونَ لَهُ وَيَعْمَلُونَ عَمَلًا دُونَ ذَلِكَ وَكُنَّا لَهُمْ حَافِظِينَ ٠
Ma'ana
81. Sulaimanu kuwa (Muka hore masa) iska mai karfi tana gudu da umarninsa zuwa kasar da Muka yi albarka a cikinta, (watau Sham). Mun kuwa kasance Masana ga kowanne abu.
82. Akwai kuma wasu aljannu da suke nutso don fito masa (da lu'u-lu'u) suna kuma yin wani aikin ban da wannan (kamar gine-gine); Mun zamanto kuma Masu kula da su)).
Sharhi:
Sannan Allah Ya bayyana cewa Ya kuma hore wa (Annabi) Sulaimanu ikon sarrafa aljannu da sanya su su yi masa hidima irin wadda ya bukata daga gare su. Daga cikinsu akwai wadanda aikinsu kawai shi ne nutso a karkashin ruwa suna fito masa da albarkatu iri daban-daban kamar lu'ulu'u da marjani. Wasu kuma ba su da wani aiki sai yi masa manyan gine-gine da mutum-mutumi da ganuwoyi da makamantansu. Allah ya bayyana cewa shi ne mai tsare da su, yana kuma sane da adadinsu da ayyukansu, babu kuma mai iya guduwa daga cikinsu.
(Fassara da sharhi: Dr. Sani U.R.L).
ASALIN HALITTAR AL-JANU MAZAUNA CIKIN RUWA.
Aljanu gaba ɗaya, ciki har da mazaunan ruwa, Allah Ya halicce su daga wuta mai zafi kamar yadda ya zo a cikin Al-Qur’ani. Amma masana tafsiri da malamai kamar Ibnu Kasir da Mujahid sun bayyana cewa akwai jinsuna daban-daban na aljanu – wasu suna cikin iska, wasu a cikin duwatsu, wasu a cikin dazuka, har da cikin ruwa da cikin teku. Aljanu mazauna ruwa su ne waɗanda aka haifa ko kuma suke zaune da rayuwa a ƙasan ruwa – teku, kogi, rafi, tafki, tsofaffin rijiyoyi da dai sauransu. A ciki suke da duniyoyins da masarautunsu da iyalansu da kuma komai na su.
Aljanu mazauna ruwa, kamar sauran jinsin Aljanu, suna da Iri daban-daban na launin fata (kamar ja, baƙi, shuɗi da dai sauransu. Suna iya canza siffa ( su zama mutum, dabba, ko ruwa). Suna iya fita daga ruwa su bayyana a doron ƙasa. Suna amfani da wasu sinadaran ruwa don yin sihiri ko ɓoye kai.
Wasu malamai sun ruwaito cewa suna da ƙafafu masu kama da na kifaye, ko kuma wasu suna da fuka-fukai kamar na kifin shark. Wannan ya danganta da jinsinsu.
Ibn Taymiyyah ya ce
“Aljanu suna cikin kowane irin wuri; cikin iska, rana, ruwa, har ma cikin gida. Wasu sun ƙware wajen ruwan teku da zurfafan kogi.”
Imamul Qurɗubi ya bayyana cewa
“Wani rukuni na aljanu sun kware wajen ilmin ruwan teku da abubuwan da ke cikinsa kamar zinariya, lu’ulu’u da sauran ma’adinai.”
Aljanu sun kasance suna tonon zinariya, azurfa, da lu’u-lu’u daga zurfafan ruwan teku, kuma suna kawo wa Annabi Sulaiman (AS). A bisa wannan hujja, malamai sun ce akwai kwararrun aljanu na ruwa da suka fi kowa ƙwarewa a gano ɓoyayyun ma’adinai a karkashin ruwa.
A gargajiya irinta Bahaushe, ya aminta da akwai Aljanu mazauna ruwa waɗanda kan yi m'amala da mutane, kodai kyakkyawar mu'amala ko kuma ta cutarwa. Gawurtaccen Aljnin ruwa mai cutarwa ko yin kisa ana kiransa da suna Mai kilago a Hausa.
ALAMOMIN DA KE NUNA AL-JANIN RUWA YA SHAFI MUTUM.
Tsautsayi ya kan kai mutum inda Aljanun ruwa suke rayuwa, har su shafe shi da cuta. Wani sa'in kuma akan yi wa mutum sihiri wanda aka haɗa kai da Aljanu mazauna ruwa ko neman taimakonsu don a cutar da mutum, kamar asirin da ake yi a jefa a tsohuwar rijiya ko a jefa a kogi ko ruwamai gudana.
Ga wasu alamu da mutum zai gane Aljanun ruwa sun shafe shi.
1. Tsananin tsoron ruwa_ Kamar mutum ya dinga yin jiri ko jin kamar zai faɗa ruwa idan ya ga babban kogi ko yaje kusa da rijiya.
2. Mafarkin ruwa akai-akai_ Kamar mafarkin kogi ko ruwan sama ko wanka da ruwa .
3. Yawan mafarkin halittun cikin ruwa, kamar kifaye, kwaɗi, dorinar ruwa da dai sauransu. Musamman mutum yana cikin ruwa tare da su.
4. Yawan kwanciya a jikin ruwa ko guri mai danshi, kamar wurin rafi, kogi, jikin randa da dai sauransu.
5. Mutum ya rika yawan fama da matsanancin ciwon ƙirji ko mara ba tare da dalili ba
6. Yawan faɗuwa ko yawan ciwon kai da baya
7. Rashin samun bacci musamman da dare, da mafarkai masu ban tsoro masu alaƙa da ruwa.
8. Mutum ya dinga yawan jin kamar ana kiran sunansa daga cikin ruwa.
9. Fitsarin kwance ga manya, kamar budurwa ko matar aure ko maza magidanta, musamman bayan mutum ya yi mafarkin ga shi a cikin kogi ko kumaya gan shi yana futsari a wani waje, sai ya farka ya ga jikinsa ya jiƙe da fitsari.
10- Fama da ciwon sanyi wanda aka kasa gane shi ko shawo kan sa a asibiti.
YADDA AKE HAƊA MAGANIN CUTUTTUKAN ALJANUN RUWA
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.
Abubuwan da za a samu.
1)Ganyen magarya. 2)Ganyen habba. 3) Ganyen rimi. 4)Ganyen ɓaure. 5)Gishiri. 6)Lalle
Yadda za a haɗa
A daka su wuri ɗaya, zuba a tafasasshen ruwa. A barshi ya huce kaɗan. A yi wanka da shi da sassafe ko bayan sallar magariba.
Yana da kyau kuma a dinga haɗawa da addu'o'i da ayoyin ruƙ'yah domin samun waraka da dogaro ga Allah.
Ga duk mai bukatar magungunan da muke hadawa na matsalolin Ajanu da sihiri da sauran cututtuka na yau da kullum zai iya tuntuɓarmu a wannan lamba 08162600700.
Daga Shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08134434846.
Comments
Post a Comment