MUHIMMANCIN ZAMAN LAFIYA A MUSULUNCI.
Daga shafin Bashir Halilu
1- Kare rayuka da dukiyoyi.
Zaman lafiya yana hana kashe juna da lalata dukiyoyi, wanda aikata hakan babban zunubi ne a Musulunci.
2- Ibada cikin nutsuwa.
Ba za a iya bautar Allah yadda ya kamata ba kamar Sallah, azumi, hajji da sauran ibadu, matuƙar ba zaman lafiya a gari.
3- Inganta zumunci da ƙaunar juna
Zaman lafiya yana kawo ƙauna da fahimta a tsakanin Musulmi, wanda hakan ginshiƙi ne na samar da al'umma mai ƙarfi.
4- Ci gaban tattalin arziki da ilimi.
A cikin zaman lafiya ake samun damar noma, kasuwanci, da karatu ba tare da fargaba ba.
5- Kariya daga shaiɗan da rikicin zuciya
Rikici yana buɗe ƙofa ga Shaiɗan don tayar da husuma. Zaman lafiya yana hana hakan.
6- Ƙarfafa haɗin kai da taimakon juna.
Zaman lafiya yana ƙarfafa haɗin kai wajen gina al'umma da taimakon marasa ƙarfi.
7- Kariya daga halaka da azaba daga Allah.
Idan mutane suka rika aikata zalunci da rikici, Allah na iya azabtar da su gaba ɗaya.
9- Neman gafara da rahamar Allah.
Zaman lafiya da yafiya yana daga cikin halayen da Allah Ke so, kuma yana jawo rahama da gafara.
10- Neman zaman lafiya da haƙuri da yafi cika umarnin Allah ne da kuma kwaikwayon halayen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
Muna fata Allah Ya ƙara mana zaman lafiya, Ya kare mu daga sharrin dukkan masu son tayar mana da fitina a garuruwanmu ko cikin addininmu na Musulunci.
Daga shafin Bashir Halilu.
Comments
Post a Comment