HAƊUWAR SHAIƊAN DA ANNABI YAHYA (AS) HAR KARO BIYU.
Daga Shafin Bashir Halilu
A cikin littafin Maka'idish Shaiɗan, Ibni Abid dunya ya ruwaito cewa:
Abdullahi ɗan Muhammad ɗan Ubayd ya ce: Ahmad ɗan Ibrahim al-Abdiyyu ya ba mu labari, ya ce: Muhammad ɗan Yazid ɗan Khunays ya ba mu labari, daga Wuhaib ɗan -Ward ya ce:
"An ruwaito mana cewa: Iblis, mugu kuma makiri, ya bayyana ga Annabi Yahya ɗan Annabi Zakariyya (AS), sai ya ce masa:
'Ina so in ma ka nasiha.'
Sai Annabi Yahya (AS) ya ce:
'Ƙarya kake! Kai ba za ka yi min nasiha ba. Amma ka ba ni labarin mutane.'
Sai Iblis ya ce:
'Ɗan Adam ya kasu gida uku a wurinmu:
1. Na farkon su ne mafi wahala a gare mu. Muna zuwa wajensu, mu sa su aikata saɓo, amma su kan tuba da neman gafara, har su lalata duk wani makirci da muka yi musu. Muna komawa kansu, su kuma su dawo su tuba. Ba ma samun abin da muke so daga gare su, kuma ba ma daina ƙoƙarin fitinarsu. Wannan ya jefa mu cikin wahala."
2. Na biyu su ne kamar ƙwallo a hannun yara a gare mu. Muna juyawa da su yadda muke so. Sun riga sun bar mana kansu gaba ɗaya."
3. Na uku kuwa irinka ne, mutane masu tsarki, ba mu da iko da ku."
Wannan ƙissa ta nuna mana cewa masu tuba bayan sun aikata zunubi su ne suke wahalar da Shaiɗan.
ƘISSA TA BIYU
Ibnu Abid dunya ya ce:
Muhammad ɗan Yahya al-Marwazi ya ba mu labari, ya ce:
Abdullahi ɗan Khubayƙ ya ce:
"Annabi Yahya ɗan Annabi Zakariyya (A.S) ya haɗu da Iblis a siffarsa, sai ya ce masa:
'Ya Iblis, faɗa min wa ne mutum ka fi ƙauna, kuma wane mutum ka fi ƙi?'
Sai Iblis ya ce:
'Mafi ƙauna a wurina shi ne mumini mai rowa kuma mafi ƙyama a wurina shi ne fasiƙi mai kyauta'.
Sai Annabi Yahya (AS) ya ce: "Ta yaya hakan ya kasance?"
Sai Iblis ya ce:
"Saboda marowaci rowarsa ta ishe shi, ya riga ya hana kansa alkhairi, ba sai na sha wahala da shi ba. Amma fasiƙi mai kyauta, ina tsoron kada Allah Ya duba halin kyautarsa Ya karɓe shi."
Sannan Iblis ya juya, ya tafi, yana cewa:
"Da ba kai ne Yahya ba, da ban gaya maka ba."
Duba Littafin Maka'idish Shaiɗan.
Daga Shafin Bashir Halilu.
Comments
Post a Comment