HIJIRAR FARKO ZUWA HABASHA DA KUMA MUSULUNTAR NAJJASHI SARKIN HABASHA
Daga shafin Bashir Halilu.
Mallam Ibnu Kasir ya kawo acikin littafin Al-Bidāyah wan-Nihāyah cewa:
Lokacin da azabar da Musulmai suka fuskanta a Makka ta yi tsanani daga kuraishawa, Manzon Allah ﷺ ya ba su shawarar su koma ƙasar Habasha (wato Ethiopia) ya ce:
"A can akwai sarki wanda ba a zaluntar kowa a ƙasarsa, kuma ƙasarsa ƙasar gaskiya ce, ku tafi har sai Allah Ya kawo muku mafita.”
Sai wasu daga cikin Sahabbai suka yi hijira zuwa can, cikinsu har da Ja’afar ɗan Abī Ɗalib da Abdullahi bn Mas’ūd da Zubayr binil ‘Awwām da wasu daga cikin musulman farko.
Da Ƙuraishawa suka ga cewa Musulman sun samu mafaka a Habasha, sai su ka aika da wakilai guda biyu: ’Amru binil-‘Āṣ da ’Abdullāhi bin Abī Rabī’ata, su ka ɗauki kyaututtuka masu yawa domin su ba sarkin Habasha da manyan fadawansa don su dawo musu da Musulman nan zuwa Makkah domin su cigaba da azabtar da su.
Ko da su ka isa garin Habasha sai su ka dinga bi gidajen manyan ƴan fadar Sarki da Hakimai suna kai musu gaisuwa da kyaututtuka sannan su ka nemi isa fada. Su ka isa wajen Sarki, su ka kai masa kyauta ta gaske, wacce Sarki yai farin ciki da ita sosai, sannan aka nemi jin abinda ke ta fe da su fadar Sarki.
Sai su ka fara gabatar da kansu cewa manya ne da mahukunta daga garin Makkah su ka turo su akan waɗannan baƙin Musulmai da ke gudun hijira a Habaha, sannan su ka ce:
"Waɗannan mutane sun bijirewa addininmu da na iyayensu, wato addinin bautar gumaka, sannan sun zo nan wajenku sun ƙi shiga addininku. Shi ya sa muke roƙon ku ku mayar mana da su gida don mu dinga kula da su."
Da Sarkin Habasha Najjāshi ya ji wannan bayani na su sai ya ce:
"To, ni ba zan miƙa mutum ga abokan gabansa ba sai na ji daga gare su."
Don haka sai Sarki ya sa aka baiwa Su Amru binil Asi masauki sannan aka aikawa Musulman da ke gudun hijirah cewa Sarki yana nemansu a fada domin ƴan uwansu sun zo akan maganarsu.
Da aka kira Musulman, sai Najjāshi ya tambaye su ya ce:
"Me ya sa ku ka bar ƙasarku da addininku?”
Sai Ja’afar bin Abī Ɗālib ya ce:
"Ya kai wannan Sarki, mun kasance mutanen da ke cikin jahilci, muna bautar gumaka, muna cin naman mushe, muna saɓawa iyaye, muna yawaita alfasha da aikata miyagun laifuka; Sai Allah Ya aiko mana da Manzo daga cikinmu, mun san amincinsa da gaskiyarsa, wannan Manzo ya umarce mu da bautar Allah Shi kaɗai, ya hana mu yanke zumunci da sharri, ya umarce mu da yin gaskiya da tsafta; Amma sai waɗannan mutanen na mu su ka tsananta mana, su ka yi mana zalunci iri-iri, su ka ƙuntata mana, su ka hana mu sakewa. Da mu ka ga haka sai mu ka bar cikinsu, mu ka zaɓe ka, mu ka zo ƙasarka, muna masu fatan za mu zauna lafiya kuma ba za a zalunce mu a wajenka ba.”
Duk wannan abun da ke faruwa fadar Sarki ta cika maƙil da Fadawa da Malaman Nasara da sauran jama'a, kowa yana sauraro.
Da Najjashi ya ji wannan bayani na Ja'afaru bin Abi Ɗalib sai ya ce: "Shin kuna da wani abu na ilimi daga abin da Manzon na ku ya zo da shi?"
Sai Ja’afaru bin Abi Ɗalib ya masa masa, kuma ya karanta masa farkon Suratu Maryam (ayoyin da suka ambaci ƙissar Nana Maryam da kuma haihuwar Annabi (A.S.).
A nan ne Najjashi da sauran Malaman Nasara su ka ji haƙiƙan ƙissar Nana Maryam wadda ba su taɓa ji acikin littattafansu ba, kuma su ka ji gaskiyar yadda aka haifi Annabi Isa (A.S.).
Najāshi ya fashe da kuka har fuskarsa da gemunsa su ka jiƙe da hawaye. Sannan ya ce:
"Wannan da abinda ka karanta na Alƙur'ani da abinda Īsā ya zo da shi na Attaurah duk suna fitowa daga wuri ɗaya ne (ma'ana daga wajen Allah su ke."
Saboda haka Sarki ya ƙi yarda ya mayarda Musulmai hannun arnan Makkah wato Ƙuraishawa sannan ya umarci fada ta tashi haka.
Bayan wakilan Ƙuraishawa Abdullahi bin Rabi'ata da Amru binil Asi sun koma masaukinsu, sai takaici ya cika musu zuciya da ɓacin rai. Ga shi sun yi asarar dukiya mai yawa, sun rabawa Sarki da Fadawa ga shi kuma ba biyan buƙata. Don haka sai su ka sake dabara.
Washegari sai ’Amru binil ‘Āṣi ya koma wajen Sarkin ya ce: " Ya mai girma Sarki, su fa waɗannan mutanen suna faɗin kalmomi marasa kyau a kan Annabi Īsā!"
Sai Najjāshi ya sa aka sake kiran su, ya ce: "Me kuke faɗi a kan Īsā ɗan Maryam?"
Sai Ja’afaru bin Abi Ɗalib ya ce: "Annabinmu ya gaya mana cewa shi bawan Allah ne, kuma ManzonSa, da kalmarsa wadda ya aiko ta ga Maryam, da ruhi daga gare Shi.”
Da jin haka sai Najjāshi ya ɗauki ƙyalle a ƙasa ya bugi ƙasa da shi, ya ce: Wallahi, Īsā bai ya wuce haka a wajen Allah ba, ku tafi, ku zauna lafiya a ƙasata. Duk wanda ya ce zai cutar da ku, zai biya diyya."
Ya kuma ce wa ‘Amru binil Asi da abokinsa Abdullahi bin Rabi'ata “Ku koma, ba zan miƙa Musulmai gare ku ba.”
Sannan ya sa aka ɗebo kyaututtukan da su ka ba shi, ya ce a mayar musu kayansu kuma ya umarce su su fice daga ƙasarsa.
MUSULUNTAR NAJJASHI SARKIN HABASHA
Ibn Kathīr ya faɗi cewa Najāshi ya musulunta a sirri, ya rubuta wasiƙa zuwa ga Manzon Allah ﷺ, ya aiko masa da kyaututtuka. Amma ya ɓoye addininsa saboda ya tsorata da mutanensa su tayar da hankali.
Ummu Salama – wadda ta halarci hijirar – ta ce:
"Wallahi ba mu taɓa jin ƙima da jin daɗi kamar yadda muka samu a hannun Najāshi ba."
Daga Shafin Bashir Halilu.


Comments
Post a Comment