ƘISSAR AL'HUD'HUDA DA ANNABI SULAIMAN (AS).
Daga Shafin Bashir Halilu.
Wata rana Annabi Sulaiman عليه السلام
ya fita zuwa wata tafiya shi da jama'arsa, sai ya kasance rana ta yi tsananin zafi.
Sai Al'hud'huda su ka zo su ka buɗe fuka-fukansu a sararin samaniya, su kay wa Annabi Sulaiman عليه السلام rumfa, har ya zamanto ya samu inuwa.
Sai Annabi Sulaiman (AS) ya ji daɗin abinda su kay masa. Ya ce musu "Me ku ke so nay muku kyauta da shi?"
Sai babbansu ya ce "Mu na so kowanne a cikin mu a saka masa kambun zinare a tsakiyar kansa. (Wato hular sarauta ta zinare)".
Sai sauran Alhud'hudan su ka ruɗe "E muna so, e muna so, kowannenmu yana buƙatar hular zinare".
Sai Annabi Sulaiman (AS) ya roƙi Allah Ya fito musu da hular zinare akansu, sai kuwa kowanne ta fito masa.
Sannan Annabi Sulaiman (AS) ya ce musu "Wannan hular Zinaren sai ta zama fitina a kanku".
Daga nan sai Alhud'huda su ka tashi, suka je bakin kogi su ka sauka, kowanne yana kallon fuskarsa a cikin ruwa yana ta murna yana farin ciki da wannan kwalliya da akay masa ta zinare.
To ana nan sai wani mutum maharbi ya kama Alhud'huda guda ɗaya. Da ya duba tsakiyar kansa sai ya ga ai zinare ne, saboda haka sai ya baiwa 'yan uwansa labari, sai su ma su ka shiga farautar Hud'huda.
Nan da nan sai masu farautar Alhu'huda su ka dinga zama masu kuɗi saboda zinaren da suke samu a kansa.
Daga nan duk mutanen gari sai kowa ya koma farautar Alhud'huda. Sai su ka zamanto saura kaɗan a duniya kuma ko ina ana tarkonsu.
Sai Alhud'huda sukay shawara suka koma wajen Annabi Sulaiman عليه السلام su ka ce "Ya Annabin Allah, ka roƙi Ubangiji Ya cire mana wannan kambun zinare da yake kan mu".
Sai Annabi Sulaiman (AS) ya ce "Ai dama na gaya muku sai ya zama fitina a kanku".
Sai aka cire musu kambun zinare dake kan su, aka saka musu tozo irin na Zakara wanda muke gani a kansu yanzu.
Allah Ya sa mun fahimci wannan ƙissa kuma mun wa'azantu da ita.
Daga shafin Bashir Halilu
Comments
Post a Comment