DUK WANDA YA ƘIRƘIRO SABUWAR IBADA TO BA SHI DA LADA
عَنْ أمِّ المُؤمِنينَ أمِّ عبْدِ اللهِ عائشةَ رَضِي اللهُ عَنْهَا قالَتْ: قالَ رسولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
{مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ مِنْهُ فَهُوَ رَدٌّ}
رواه البخاريُّ ومسلمٌ.
وفي روايةٍ لمسلمٍ: {مَنْ عَمِلَ عَمَلاً لَيْسَ عَلَيهِ أَمْرُنا فَهُوَ رَدٌّ}.
An karɓo daga Ummul-Mu’uminina, Ummu Abdullahi, Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Manzon Allah ﷺ ya ce:
“Duk wanda ya ƙirƙiri wani abu a cikin wannan al’amari na mu (addininmu), wanda ba daga cikinsa ya ke ba, to abun juyarwa ne.”
★Wato dukkan wanda ya ƙirƙiro wani aiki na ibada wanda ba musulunci ne ya yi umarni ba to za a mayar masa da aikinsa, Allah ba Zai karɓa ba ballantana Ya ba shi lada.
(Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.)
A wata ruwaya daga Muslim kuma:
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce:
“Duk wanda ya aikata wani aiki wanda ba bisa umarninmu ba ne, to ba a karɓa.”
★Ma'ana aikin ibada wanda Allah da Manzonsa ba su ce a yi ba.
Allah Ya raba mu da bid'ah, Ya ba mu ikon riƙo da sunnah kuma Ya tabbatar da mu akan imani.
Daga Shafin Bashir Halilu
Comments
Post a Comment