HAƊUWAR SHAIƊAN DA ANNABI ISA (A.S.)


Daga Shafin Bashir Halilu.

      An karɓo daga Abu Bakar Muhammad ya ce: Al-Fablu bin Musa al-Baṣri ya ba mu labari, ya ce: Ibrāhīm bin Bashshār ya ce: Na ji Sufyān bn ‘Uyaynah yana cewa:

         "Annabi  Isa ɗan  Maryam (A.S) ya haɗu da Iblīs, sai Iblīs ya ce masa:

— “Kai ne wanda saboda girman allantakarka ya kai ga cewa ka yi magana tun kana jariri a cikin zanin goyo, alhali babu wanda ya taɓa yin magana a cikin zanin goyo kafin kai."

      Sai Annabi Īsā (A.S) ya ce da shi  “Ai matsayin Allantaka da girma na Allah ne, wanda Ya sa na iya magana. Shi ne kuma zai kashe ni, sannan Ya raya ni.”

Sai Iblīs ya ce “To kai ne wanda girman allantakarka ya kai har kana ta da matattu”

Sai  Annabi Isā (A.S) ya ce: “Ai matsayin Alkantaka na Allah ne, wanda Zai kashe ni, kuma Ya kashe waɗanda na ta raya, sannan Ya raya ni.”

Sai Iblīs ya ce: “Na rantse da Allah, kai Allah ne a sama, kuma Allah ne a ƙasa!”

     A wannan lokacin sai Mala’ika Jibrīl (A.S) ya buge Iblīs da fikafikansa bugun farko har ya kusan kaiwa mahudar rana, sai ya sake bugunsa karo na biyu har ya kusa kaiwa madubin ruwan rana mai zafi (al-‘ayn al-ḥāmiyah). Sannan ya buge shi karo na uku har ya jefa shi cikin tekun na bakwai, ya nitsar da shi har sai da ya ɗanɗano ƙasan datti mai wari. Sannan ya fito yana cewa: “Babu wanda ya taɓa gamuwa da abin da na gamu da shi daga gare ka, ya Ibn Maryam.”
       Duba littafin Maka'idish Shaiɗan na Ibni Abid Dunya.

Daga shafin Bashir Halilu

Comments

Popular Posts