AIKIN DA ZAI SHIGAR DA KAI AL-JANNAH KUMA YA HANA KA SHIGA WUTA
Daga shafin Bashir Halilu
An karɓo daga Mu'azu bin Jabal (Allah ya yarda da shi), ya ce:
Na ce: "Ya Manzon Allah, ka sanar da ni wani aiki da zai shigar da ni Aljanna kuma ya nisantar da ni daga Wuta."
Sai ya ce: "Lallai ka tambayi abu mai girma! Amma lallai yana da sauƙi ga wanda Allah Ya sauƙaƙa masa:
Ka bauta wa Allah, kada ka haɗa Shi da wani (shirka), kuma ka tsayar da sallah, ka bayar da zakka, ka yi azumin Ramadan, kuma ka yi aikin Hajji zuwa ɗakin Allah (Ka’aba)."
Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ƙara da cewa:
"Shin ba zan sanar da kai ƙofofin alheri ba?
Azumi garkuwa ne (yana kare mutum daga shiga wuta). Sadaka tana cinye zunubi kamar yadda ruwa ya ke kashe wuta, sannan sallar mutum a tsakar dare..."
Sai ya karanta:
(تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ...) har ya kai: (يَعْمَلُونَ)
Sai ya ce: "Shin ba zan gaya maka shugaban al'amari ba, da ginshiƙinsa, da kololuwar ɗaukakarsa?"
Na ce: "E, ya Manzon Allah."
Sai ya ce:
"Shugaban al’amari shi ne: Musulunci,
Ginshiƙinsa: Sallah,
Kuma kololuwar ɗaukakarsa: Jihadi a cikin tafarkin Allah."
Sai ya ce: "Shin ba zan sanar da kai abinda ya mallaki dukkan waɗannan ba?"
Na ce: "E, ya Manzon Allah."
Sai ya kama harshensa ya ce:
"Ka kiyaye wannan (wato harshenka)."
Na ce: "Ya Annabin Allah, ashe za a hukunta mu da abin da muke faɗa?"
Sai ya ce:
"Mahaifiyarka ta wabinka! Shin akwai wani abu da ke jefa mutane cikin Wuta a kan fuskokinsu – ko ya ce a kan hancinsu – face sakamakon abin da harsunansu suka girba?"
. Tirmiziyyu ne ya rawaito shi, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau kuma sahihi.
Daga Shafin Bashir Halilu
Comments
Post a Comment